RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

Tambayoyi Kan Azumi Da Batun Shika Na Aure

Rate this item
(5 votes)
Sheikh Muhammad Nur Dass, Shugaban Mu'assasar Rasulul Aazam Sheikh Muhammad Nur Dass, Shugaban Mu'assasar Rasulul Aazam

Mai Tambaya: Muazu M. Kafur:

Salaam, Allah Ya jikan mallam ina da tambayoyi kamar haka: 1. Idan zamani ma'ana lokaci yayi duli(zawo) mutum bai samu ya fitar da zakkar fidda kai ta karshen watan azumi ba har sai da wata shekara (ta musulunci) ta shiga, yaya mutum zaiyi da ita awannan lokacin?

Ga amsar Maulana Sheikh(H):

SALAM, IDAN FAKIRCI NE YA SA BAI SAMU YA FITAR BA, TO BABU KOMAI A KANSA, WAJIBCI YA FADI A KANSA.

 2. Shin mutum ya samu yayi azumi awani gari ko wata nahiya kuma yayi zakkar fidda kai a wani garin ko nahiya daban da inda yayi azumin?

Amsar Maulana Sheikh(H)=

''WAJIBI NE KA FITAR A GARIN DA KAKE DA ZAMA SAI DAI HAKAN BAI HARAMTA IDAN BABU WADANDA SUKA CANCANCI ZAKKA A GARIN DA KAKE TO HALAS NE KA KAI WANI GARI DABAM''

 3. Idan mutum ya shagalta da azumin ramuwa ko kaffara na farilla, shin zai iya yin wani azumin na nafila ba tare da gabatar da ramuwar farillan ko kaffarar ba? 

 Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

''IDAN ANA BIN MUTUM AZUMIN FARILLA TO YIN AZUMIN NAFILA BAI INGANTA''.

 

4. Idan mutum ya sami sabani da matar sa sai tarika cewa ya sake ta ta gaji da zama dashi, shi kuma yaki sakinta shin yayi laifi na shari'a?

 Ga Amsar Maulana(H):

 
''DON TACE YA SAKE TA SAI YA KI SAKINTA , SAM BAI YI LAIFI BA, TO SAI A KOMA A DUBA KORAFINTA KO DA TA HANYAR SHIGO DA DANGI NE, KANA SAI A SULHUNTA TSAKANI''

 

5. Mutum ne ya biya sadaki na matar da zai aura, kuma iyayenta suka furta cewar sun bashi ita kuma yace ya amsa har aka sa ranar daurin aure, to amma kafin ranar tazo sai ya taki matar da kwanan aure, shin yayi laifi? Kuma menene hukuncin shari'a akan takin da yayi wa matar?

 
Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

''KARBAN SADAKI BA SHIKE HALASTA TA GA MUTUM BA, ABIN DA KE HALASTA MASA ITA SHI NE KARANTA SIGAR AURE, DON HAKA A NAN SUN AIKATA LAIFI SHI DA ITA, AMMA HAKAN BAI HARAMTA AURE A TSAKANINSU BA''

6. Idan ana bin mutum sallar farillah, ya samu yayi lafila? 

 

Ga Amsar Maulana Sheikh(H)

 

''WANDA AKE BIN SA SALLAR FARILLA ZAI IYA YIN NAFILA KUMA TA INGANTA, WATO SA'BANIN HUKUNCIN AZUMI''.

 

7. Idan tafiya ta zama daga bangaren aikin mutum akan iktisabinsa, menene hukuncin sallolinsa abisa kasaru ko cikawa?

 

Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

 

''IDAN MUTUM YA ZAMA MAI YAWAN TAFIYE TAFIYE AKAN AIKI KO KASUWANCI, TA YANDA CIKIN KWANA GOMA ZAI YI TAFIYA SAU DAYA KO SAMA DA HAKA , TO CIKA SALLAH ZAI YI''.

8. Ni ne na dade ina sallar kasaru acikin tafiya ta sai daga baya na gano cewar ya kamata in cika ne bayan tsawon lokaci. Shin menene abin yi agare ni a cikin irin wannan halin?

 

Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

 

''MUTUMIN DA YA YI SALLAR KASARU A MAIMAKON CIKA SALLAH, TO ZAI RAMA SALLOLIN DA YA YI SU A KASARU YA MAI DA SU CIKAKKU, SAI DAI IDAN BISA JAHILCI NE''.

 

 9. Ko ya halatta ayi sujada akan tiles na zamani wanda akayi shi da cast?

 

Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

 

''SUJJADA A KAN TILE HALAS NE, TO SAI DAI IN SUN KARA MASA WANI SINADARI DA YA RUFE TA SAMANSA A YAYIN NAN SUJJADA BAI INGANTA A KAI''

 

10. Menene hukuncin shari'a na mafarki a musulunci? 

 

Ga Amsar Maulana Sheikh(H):

 

''MAFARKIN MA'ASUMI SHI NE HUJJA, DON HAKA BA MA DAUKAN HUKUNCI DAGA MAFARKAI, SAI DAI MU DAUKO DAGA LITTAFAN FIKIHU''

 

NB

Ana Iya Aiko Tamboyi Zuwa Ga Sheikh Muhammad Nur Dass Ta Shafin Tambayoyi Da Amsoshi A Shafin Facebook Ta Nan: https://www.facebook.com/groups/435244429890536/

 

 

Last modified on

116 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel