RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

Sheikh Saleh Zariya Ya Halarci Taron Malamai Da Farkawar Musulmi A Tehran Featured

Rate this item
(4 votes)
Sheik Saleh Zaria Da Jagora Imam Khamenei Sheik Saleh Zaria Da Jagora Imam Khamenei

A ranar Litinin 29, Aprilun 2013 ne Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya ya wakilci shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam Sheikh Muhammad Nur Dass a taron kasa da kasa na Malamai Da Farkawa ta Musulunci na kwanaki biyu da aka gudanar a Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ya bude wannan taron inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewar riko da koyarwar Musulunci da kuma kasantuwa a fage a matsayin wasu abubuwa guda biyu masu muhimmanci wajen kawo karshen makirce-makircen makiya a kan al'ummar musulmi.

 

Yayin da ya ke ishara da bayyana wajibcin kiyaye matsayi na addini, shata manufar da ake son cimmawa, nesantar sanya fata cikin alkawurran kasashen yammaci da kuma makirce-makircen da suke kullawa wajen haifar da rikici na kabilanci da mazhaba da kuma rashin yin watsi da matsalar al'ummar Palastinu a matsayin abubuwan da wajibi ne a ba su muhimmanci wajen tabbatar da irin farkawar da al'ummar musulmi suke samu.

 

Yayin da ya koma kan gagarumin nauyin da ke wuyan malaman Musulunci a wannan lokacin da al'ummar suka farka, Ayatullah Khamenei ya kirayi malaman da su taka tsantsan ainun a lokacin da suke sauke nauyin da ke wuyansu na shiryar da al'umma.

Kafin bude taron dai sai da Jagoran ya gana a kebe da wasu daga cikin manyan malaman da suka halarci taron. Daga cikin malaman da suka gana da Jagoran har da Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya.

Last modified on

38 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel