RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

Auren Mutu'a Tsakanin Musulmi, Martani Ga Uztaz Ja'afar Adam... Featured

Rate this item
(6 votes)
Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya

AUREN MUTU'A TSAKANIN MUSULMI
Martani Ga
Muhammad Rabi'u Umar R/lemo Da Ustaz Ja'afar Adam
Daga
Saleh Muhammad Sani Zaria
P.O. Box 4167 - Kano
E-Mail: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
27/03/2007

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

Na bibiyi abubuwan da aka rubuta a kan Auren Mutu’a a wannan jarida mai farin jinni ta Aminiya tun daga farkonsa har na baya bayan nan. A dukkanin abubuwan da aka gabatar anyi kokari wajen fito da ainihin lamarin fili. Daga abubuwan da aka tattauna, rubutun  Muhammad Rabii’u Umar R/Lemo a fitowar wannan jarida ta ranar 16/03/2007; da hirar da jaridar ta yi da Mal. Ja’afar Adam a fitowarta ta ranar 23/20/2007 sun ja hankalina matuka. Hakan ya sa na ga ya kamata na bayar da tawa gudunmawar da fatan ta taimaka wajen kara wa tattaunawar armashi.

 

 

Da farko zan fara da abin da duk masu rubutun (masamman Umar R/Lemo da Mal. Ja’afar) suka yarda da shi na dacewa a kan halaccin Mutu’a da ayar AlKur’ani ta cikin Surar Nisa’i aya ta 24; a kan haka ne ma nake ganin cewa duk mai hankali zai yi mamakin yadda Mal. Ja’afar ya kwatatnta auren mutu’a da “Dadiro” da “Kwanan-Gida!” Idan har ya yarda da cewa akwai ayar AlKur’ani wadda ta halatta Mutu’a –ko da kuwa ya yarda da cewa an goge ta daga baya- to da wace irin mahanga kuma yake kwatanta shi da dadiro da kwanan-gida? Ina ayar da ta taba halatta dadiro da kwanan-gida a AlKur’ani har ya cancanci irin wannan kwatanci? Dadiro fa alfasha ne! Yanzu yana jin cewa akwai inda Allah Ya taba horo da alfasha sannan daga baya ya hana? Kuma yana jin cewa Sahabban da suka aikata mutu’a (koda kuwa a farkon halatta shi din ne) sun aikata alfasha kenan? Yaya matsayin Sahabban da suka saura da fahimtar rashin goge mutu’a –ba wani bambanci tsakanin “fitattu” ko “masu gafaka” da wasunsu- yana jin irin wadannan sun yarda –kuma suna- aikata alfasha kenan?  Misalta haka da matakan haramta giya kuskure ne, saboda Musulunci ba shi ya halatta giya a matakin farko ba; alhali mutu’a Musulunci ne ya kirkire shi tun asali.

 

Ko ta halin kaka dai lamarin ba yadda Ja’far da R/Lemo suke dauka ba ne, tun lokacin Sahabbai akwai sabanin ra’ayi a kan wanzuwar hukuncin auren mutu’a, sai dai na su ba irin sabanin da ya biyo bayan yaduwar kikiran hadisan karya ba ne. A wancan lokacin sabanin kan ko Khalifa na da hakkin haramta hukuncin Allah da ManzonSa –bisa kowane irin dalili ne kuwa- ko ba shi da wannan hakkin. A nan ina cewa ne hadisan da ake ambata a yau, wadanda suke dangana haramta mutu’a ga Manzo [SAWA] kirkirarru ne kuma Sahabbai ba su san su ba. Insha’Allah zan tabbatar da haka a binciken da zai zo kan wadannan hadisai a nan gaba cikin wannan kasida insha’Allah.

 

Kamar yadda ’yan’uwan suka fada, sabani ya gudana ne tsakanin malaman Musulmi (ba kawai tsakanin ’yan Shi’a da Ahlusunna kamar yadda R/Lemo ya so nunawa ba) dangane da goge shi da abin da ya goge shi da lokacin da aka goge shi.

 

Fadar Goge Auren Mutu’a Da AlKur’ani

 

Wasu daga malaman Ahlussunna da fakihansu sun tafi a kan cewa AlKur’ani ne ya haramta mutu’a kafin komai. Daga ayoyin da suke kawowa a kan haka akwai fadar Allah cewa: “Kuma su ne wadanda suke kare al’aurarsu (daga aikata sabo); sai ga matayensu ko kuyangin da suka mallaka, to lallai su (a kan wannan) ba ababen zargi ba ne. To duk wanda ya nemi wanin wannan to wadannan su ne masu ketare iyaka” (al-Mu’uminun: 5-7); bisa la’akari da cewa auren mutu’a ba aure ba ne, kuma matar da aka yi auren da ita ba matar aure ba ce, ga shi kuma da ma ba kuyanga ba ce. Aya ta biyu da suke kafa hujja da ita ita ce ayar Saki dake cewa: “Ya kai wannan Annabi, idan za ku saki mata ku sake su ga iddarsu” (al-Talak: 1). Sai kuma aya ta uku wadda ita ce ayar gado tsakanin ma’aurata dake cewa: “Kuna da (gadon) rabin abin da matanku suka bari idan ba su da da…” (al-Nisa’i: 12).

 

A kan haka na ke cewa:

 

1- Duk an dace a kan cewa Surar Mu’uminun (wadda ayar da suke da’awar an goge mutu’a da ita) a Makka aka saukar da ita, alhali Nisa’i (wadda ayar halaccin mutu’a ta zo a cikin ta) a Madina ta sauka, ta ina saukakkiyar Makka ke iya goge saukakkiyar Madina? Da wannan ba zai yiwu wannan aya ta goge mutu’a ba. Haka wannan ya raunana abin da masu haramtawa ke doruwa a kai na cewa halattawarta a farkon Musulunci ne, wanda a rayuwar Makka kenan. A duk surorin nan biyu kuwa babu wani dalili daga dukkan bangarorin biyu da ya toge ayar mutu’a da cewa a Makka ta sauka.

 

2- Mutu’an da muke zance a kansa AURE ne; don haka matar da aka yi da ita MATAR AURE ce; saboda tun da har AlKur’ani ya zo da shi da sigar yarjejniya tsakanin mata da miji, ya shiga cikin tsaikon aure kenan. Da wannan za mu iya kasa auren Musulunci zuwa kashi biyu: auren dindindin da auren mutu’a; a dabi’ance zai zama suna da wuraren da suka daidaita da inda suka saba da juna.

 

3- Duk malaman da suka halatta Mutu’a sun wajabta idda ga matar da aka yi auren da ita a duk lokacin da auren ya kare. Iddarta kwana arba’in da biyar ne da ittifakin malaman Shi’a (zancen da wasu ke dangana musu na cewa ba sa wajabta idda a kan auren mutu’a tsabagen kage ne da shaidar zur). Wannan ya bayyana kuskuren Mal. Ja’afar na tunanin cewa wani na iya “auren mutu’a da wata (mace) na awa biyu misali, kuma tsawon rayuwar auren ya kare; wani ya ya aura na tsawon kwana biyu shi ma ya kare; wani ya aura na kwana biyar…” a ina ya ga wannan? Mafi karancin muddar dake tsakanin karewar auren mutu’a da wani sabo shi ne kwana 45. Ya kamata a rika neman sani kafin ayi magana!

 

4- Idan kuwa don ba saki a cikinsa ne, to ai saki ba manufar aure ba ne, shi hanyar magance matsaloli ne a lokacin da abubuwa suka rincabe suka kai haddin rashin wani magani idan ba sakin ba; don haka ne ma Manzo [SAWA] ya siffanta saki da “halal din da Allah ke fushi da shi.” Kara da cewa masu halatta mutu’a sun halatta miji ya yafe abin da ya saura na muddar auren saboda kowane irin dalili ne kuwa, wanda hakan ke matsayin hanyar samar da mafita irin na saki.

 

5-Fadar cewa an haramta mutu’a ne da ayar gado tsakanin ma’aurata, bisa la’akari da cewa ba a wajabta gado tsakanin ma’aurata a auren mutu’a ba, wannan ba kakkarfan dalili ba ne; saboda babu abin da ke lizimta wa hatta dauwamammen aure gadon ma’aurata; bisa la’akari da cewa akwai halayen da shari’a ta yanke igiyar gado tsakanin ma’aurata, kamar a lokacin da kafirci ya gindaya (saboda kafiri ba ya gadon Musulmi); ko kisa ya shigo (saboda wanda ya yi kisa ba ya gadon wanda ya kashe). Da wannan za mu iya fahimtar cewa gado wani tanaji ne na dabam daga aure, illa dai shi aure (na dindindin) daya ne daga sabubban gado; iyakarta kenan.

 

6-Dukkanin wadancan ayoyi ba su fito barobaro sun haramta auren mutu’a kamar yadda ayar da ta halatta shi ta fito da halattawan ba; domin kuwa ayar da ta halatta cewa ta yi: “Abin da kuka yi mutu’a da su a kan shi, to ku ba su ladaddakinsu (wannan) farilla ne” (Nisa’i: 24). Ga shi kuwa Allah Yana fadar yadda Yake goge wata aya da wata da cewa: “Idan muka shafe wata aya ko muka manta da ita (wato muka kau da kai daga gare ta) mukan zo da wadda ta fita ko kamar ta” (Baqara: 105). Idan za mu yi amfani da yadda muka saba fahimtar AlKur’ani a nan, ya kamata mu fahimci cewa ayoyin da ake da’awar goge mutu’a da su ba su fito da haramta shi daidai da yadda ayar dake halattawa ta fito da bayanin halattawan filla filla ba. Kuma ba su zo da wani hukunci day a musanya mutu’a ba (bisa la’akari da cewa da ma can akwai tsarin dauwamammen aure kafin a halatta mutu’a). Wannan ya saba da waccan ka’ida ta “goge aya da wadda ta fi ta ko irin ta.”

 

Wadannan dalilai shida kawai sun isa su sa dole mu ki yarda da goge mutu’a da wata aya daga AlKur’ani.

 

 Fadar Goge Auren Mutu’a Da Hadisai

 

Wannan ya kawo mu nazari a kan da’awar goge mutu’a da ruwayoyi, wanda shi ne mafi karfin madogaran masu haramtawan. Ruwayoyin haramta mutu’a sun kasu kashi biyu kamar haka:

 

Kashi Na Daya: Su ne ruwayoyin dake dangana gogewan ga Manzo (SAWA). Irin wadannan hadisai an dangana ruwayarsu ga mutane uku:

 

a) Imam Ali bin Abi Talib: a hadisin Abubakr bin Abi Shaiba, wanda isnadinsa ya hadu da Sufyan bin Uyaina daga Zuhri, ya kare da Ali [AS] ta hanyar dansa Muhammad (binl-Hanafiyya), wanda kuma yake cewa (wai Ali) ya ce: “Lallai Manzo (SAWA) ya hana auren mutu’a a lokacin (yakin) Khaibara kuma ya hana cin naman jakunan gida.” Wannan ya maimaitu da lafuzza makusanta a kusan duk littafan hadisai na Ahlussunna.

 

Wannan hadisi ba ya iya zama hujja a kan goge mutu’a saboda dalilai ma su zuwa:

 

1. Yana da babbar matsala a isnadinsa, saboda a ciki jerin wadanda suka ruwaito shi akwai Sufyan bin Uyaina, wanda shi Sufyan sananne ne datadlisi a hadisai (wato boye aibobin da ke tattare da hadisi ko sanadinsa). Wannan shi ne abin da Zahabi ya tabbatar a cikin littafinsa Mizanul-l’itidal (2/170), har ma ya kara da cewa shi Sufyan bin Uyaina “ya kware da irin wannan aiki na tadlisi, kuma ba ya yin haka sai ta hanyar jingina wa mutanen da aka yarda da su.” Dacewan malaman hadisi ne kuwa cewa tadlisi na daga mafi girman abubuwan dake raunana hadisi; don haka irin hadisin dake da wannan illa ba zai taba goge hukuncin AlKur’ani ba.

 

2. Yayi karo da abin da ya shahara daga Imam Ali [AS] na nacewarsa a kan halaccin auren mutu’a; ta yadda har maganarsa mai cewa: “Ba don cewa Umar ya hana auren mutu’a ba da babu wanda zai yi zina sai tababbe” ya zama ruwan-dare a tasakanin masu nazari a kan lamarin mutu’a. Don kore wa irin su R/Lemo shakka nake cewa a duba wannan zance na Imam Ali [AS] a tafsirin Tabari (5/13); da Tafsirul Kabir na Fakhruddin al-Razi (10/50); da tafsirin Durrul Manthur na Suyuti (2/140); da tafsirin Kurtubi (5/130) da wasu littafan hadisi irin su Nailul-Autar na Shaukani (3/250-251) da Subulul-Salam (sharhin Bulugul-Maram) na San’ani (3/967).

 

b) Sai ruwayar da ta zo ta hanyar Sabra bin Ma’abad al-Juhaniy: Shi ne hadisin Abdul-Malik bin Rabi’ bin Sabra da ke cewa: “Manzon Allah [SAWA) ya umarce mu da yin mutu’a a shekarar da aka bude Makka yayin da muka shiga birnin Makka, amma ba mu fice daga cikinta ba har sai da ya hana mu yin auren na mutu’a.” Wannan hadisi ya maiamaita da lafuzza makusanta ta yadda har ya wuce wanda ya gabace shi. Sai dai shi ma kamar wanda ya gabace shi ne, ba shi da kwarin da zai iya goge ayar AlKur’ani saboda dalilai masu zuwa:

 

1. Duk da yawan hanyoyinsa sai dai duk sun kare ne da Sabra daga babansa. Wannan ya sa hadisin ya zama cikin hadisan al-Aahad (wato hadisin da ya fito ta hanyar mutum daya) wanda malamai suka dace a kan cewa ba ya goge aya. Kara da cewa a daya daga cikin ruwayoyin na Sabra an ce huduba Manzo [SAWA] ya yi ga jama’a a tsakanin Ka’aba da Makamu Ibrahim; amma duk da haka babu wanda ya ruwaito wannan huduba sai Sabra shi kadai!

 

2. Sabra ya ruwaito shi ne daga babansa Rabi’u, wanda masana masu ruwayar hadisi suka kusan dacewa a kan cewa majhuli ne (wato ba a ma san shi ba). Wannan ma aibi ne dake raunana hadisi.

 

3.           Ruwayoyin Sabra din suna karo da juna wajen fayyace lokacin da haramtawan ya faru; wasu daga cikin su sun ce ranar bude Makka, wasu suka ce a hajjin ban-kwana. Kara da cewa ya yi karo da hadisin da a kan dangana wa Ali, wanda zance a kansa ya gabata; saboda a can an dangana haramtawan ne da lokacin yakin Khaibara. Wannan duk da cewa wasu masu sharhin hadisan, irin su Ibin Hajar mai sharhin Bukhari, sun yi kokarin sama wa wannan mummanan karyata juna dake cikin hadisan dake haramta mutu’a mafita na cewa ta yiwu an maimaita hanin ne, sai dai wannan zato ne da bai dogara da wani dalili ba, taimakon da zai iya yi shi ne ya samar mana da shakka a kan haka; wanda ya fi wannan rauni shi ne fadar maimaita halattawan da haramtawan fiye da sau daya da wasu malamai (irin su Imamu Shafi’i a littafinsa Kitabul-Ummu). Da wannnan, ta yaya kuwa za a dogara goge tabbataccen hukuncin AlKur’ani da abin da ake shakka a kan tabbatarsa?

 

c) Sai Ruwayar Salma bin Akwa’u: Shi ne hadisin Musulim (a Littafin Aure, babin mutu’a), wanda a cikin isnadinsa akwai Yunus bin Muhammad da kuma Abdul-Wahid bin Ziyad, wanda ya ce: “Manzon Allah [SAWA] ya yi mana rahusa da yin auren mutu’a a shekarar bude Makka na kwana uku, sannan sai ya hana yin auren.” Shi ma wannan hadisi kamar sauran ’yan’wansa ne, ba ya iya zama hujjar haramta mutu’a saboda raunin hanyar da ya fito (isnadinsa); domin daga maruwaitansa akwai Yunus bin Muhammad, wanda manyan masana masu ruwaya daga Ahlussuna guda uku suka raunana shi, wadannan kuwa su ne Ibn Mu’in da Nasa’i da Ahmad bin Hanbali (kamar yadda Zahabi ya bayyana a cikin Mizanul- I’itidal 4/485). Har ila yau a cikin maruwaitan nasa akwai Abdul-Wahid bin Ziyad, wanda shi ma bai sami yabo a wajen malaman fannin ba, saboda Zahabi ya ruwaito zantukan wadannan malamai suna zargin Abdul-Wahid da cewa ya shahara wajen kago insnadi na karya a ruwaya (duba Mizanul- l’itidal 2/ 672 wajen ambatonsa); haka Abu Dawud ya yi irin wannan magana a kansa; Yahya bin Mu’in ya kara da cewa “ruwayar Abdul-Wahid ba a bakin komai take ba” (duba duk wadannan bayanan a wancan littafi na Zahabi).

 

A kan wannan ka kiyasta kowane irin hadisi ka gani yana haramta mutu’a koda a littafan Shi’a ne kuwa. Ruwayar da R/Lemo ya yi ishara da ita a al-Istibsar da Tahzeebul-Ahakam na Sheikh al-Tusi (daga malaman Shi’a na karnin hijra na hudu), ko dai bai karanta su da kansa ba (da haka ya aikata abin da ya zargi Naziru Fagge da Safiya Gusau da aikatawa kenan) ko kuma ya zama shi ma ya kawar da kansa daga cewa wannan hadisi yana tsakiyar sama da hadisai ashirin a babobi daban daban na mutu’a kuma ya saba duk sauran (da haka  zargin da ya yi ga wadancan ’yan’uwa biyu na kawar da kai daga hadisan dake haramta mutu’a a littafan Sunni ya fi cancantarsa); don kuwa: (a) a cikin wadannan littafai biyu kawai hadisin ya fito; (b) Kuma duk littafan biyu mutum daya ya wallafa su; (c) Sannan mawallafin ya tabbatar da rauninta bayan ya bayyana ta a cikin Tahzeebul-Ahakam, haka ya yi bayanin ma’anar wannan hanin a cikin al-Istibsar. Don haka babu abin da ke taimaka wa haramta mutu’a a duk littafan Shi’a.

 

Kashi Na Biyu: Su ne ruwayoyin da suke dangana hana auren mutu’a da Khalifa na biyu Umar bin Khattab [RA]. Da alamun ambaton wannan ne ya fusata irin su R/Lemo har ya nemi karyata wannan dangane da tawilinsa. Sai dai duk wanda ya bibiyi wannan mas’ala da abubuwan da malaman Musulunci suka tattauna a kanta zai zama ba shi da hanyar karyata wannan dangane ga Khalifa [RA]. Misali, daga hadisan da Muslim ya fitar a wannan babin akwai hadisin Ibn Juraih daga Ibn Zubair, ya ce: Jabir bin Abdullah (al-Ansari) ya ce: “Mun kasance muna yin auren mutu’a da (sadakin) cikan tafin hannu na dabino da (nikakken) gari na ’yan kwanaki a lokacin Manzon Allah [SAWA] da lokacin Abubakr [RA], har zuwa lokacin da Umar [RA] ya hana a kan lamarin Amr bin Haris.

 

A wata ruwayar irin wannan da Muslim ya fitar, wadda Ahmad bin Hambali ma ya fitar da ita a cikin hadisan da ya kawo kan mutu’a, an nuna lokacin da Umar [RA] ya dauki wannan mataki da cewa “a karshen khalifancinsa ne” (duba duk wadannan a Sahih Muslim 4/131 a Littafin Aure, babin Mutu’a); haka wannan ruwaya ta zo a cikin Sunan na Baihaki (wajen ambaton hadisan mutu’a a Littafin Aure) da Tafsirin Kurtubi (wajen fassarar Ayar mutu’a) da wasunsu da yawa.

 

Gaskiya ne cewa wasu malamai sun ga ba makawa su koma da haramtawar zuwa ga lokacin Manzo [SAWA], da yin tawilin zantukan Khalifa Umar [RA] mai cewa “ina yin hani a kansu” da cewa yana nufin bayanin hanin da Shari’a ta yi ne, ba shi da kansa ba. Haka wadancan sun bayyana fadinsa da ya gabaci wancan din, wanda ya ke cewa: “Sun kasance” da cewa yana nufin a wani lokaci da ya gabata kafin a hana; da cewa Umar [RA] ya fadi haka ne a bisa mumbarin Manzo [SAWA] kuma a gaban Sahabbai, da dai masu sauraronsa ba su da labarin hani a kanta da sun yi korafi a kan haka. Sai dai duk wadannan tawile-tawile zasu rasa kowace irin kima idan aka yi la’akari da cewa:

 

1. Shi dai Khalifa da kansa bai fadi hanin Shari’a kafin zancensa ba; ya dai danagana wa kansa ne hanin; da kuwa akwai wani abu a Shari’a da ya haramta mutu’a da ba za a iya fahimtar abin da zai hana Umar [RA] ambatonsa a lokacin haninsa ba. Rashin dangana hanin ga Shari’a ya nuna haninsa ne kamar yadda ya bayyana haka a fili.

 

2. Ruwayoyin da ake dangana haramta mutu’a ga AlKur’ani da fadar Manzo [SAWA] duk mun tabbatar da ranuninsu a ka’idar ruwayar hadisi ta bangaren dukkan Musulmi.

 

3. A wani zancen na Umar [RA] da ya zo a cikin ruwayar  da Baihaki ya fitar da ita a cikin Sunan dinsa (7/206), an hakaito Khalifa yana fusata bayan Khaulatu bint Hakim ta tsegunta masa auren mutu’a da Rabi’u bin Umayya ya yi da wata mace, a kan haka ne Khalifa ya fadi cewa: “Wallahi da na gabaci wannan mutu’an da na jefe shi a kansa.” Wannan na nuna kafin khalifancin Umar [RA] babu hani a kan mutu’a.

 

4.              Barazanar ukuba da Khalifa ya yi ga duk wanda ya kama da auren mutu’a ya nuna yaduwarsa a tsakanin Sahabbai (sabanin yadda Ja’afar da R/Lemo suke tsammani); abin da ke nuna Sahabbai ba su da labarin haramcin mutu’a kafin Khalifa ya hana; kuma barazana daga mai mulki ba a wasa da ita, shi yasa wasu Sahabbai suka kame daga mutu’a.

 

5. Cewa Sahabbai irin su Ibin Abbas [RA] da Jabir bin Abdullah al-Ansari da wasunsu sun yi karfin halin hamayya da matsayin Khalifa, inda suka ci gaba da fatawa a kan wanzuwar halaccin mutu’a. Abubuwan da wasu ke kokarin fada na cewa Ibin Abbas ya dawo daga halatta shi daga baya; da cewa Jabir ba shi da labarin haramcin ne ya sa ya nace a kan halatta shi, duk tawile tawile ne da ba su jingina da wani dalili ba; don haka ne ma malaman furu’a suka yi sakwa-sakwa da haramta mutu’a (ba su tsananta a kansa ba).

 

6. Zancen da Imam Ali [AS] ya yi ta nanatawa na cewa ba don hanin Khalifa ba da babu mai yin zina sai tababbe. Ka kuwa riga ka ji cewa dangana ruwayar haramta mutu’a gare shi rarrauna ne da ya fito daga wadanda aka zarga da tadlis da majhuli.

 

 

Wadannan kawai sun isa nuna cewa hanin na Khalifa ne, wanda shi ke da akalar mulki a hannunsa. Illa dai akwai uzurori da wasu ke ba Khalifa a kan haka, daga ciki akwai cewa ya yi wannan hani ne saboda wata maslaha da ta shafi wannan yanayin, don haka haninsa ba na dindindin ba ne. Wannan ya sa wasu daga malaman Ahlussunna (duk da su ne ’yan tsiraru) suka saura a kan halatta mutu’a.

 

 

Fadar Halaccin Mutu’a

 

Wadanda suke ganin hallacin auren mutu’a sun dogara ne da:

 

1.      Ayar AlKur’ani (Nisa’i: 24) wadda duk Musulmi suka dace a kan cewa ita ta hallata mutu’a, amma suka saba a kan goge ta; kenan halattawan tabbatacce ne, haramtawan ne ake da shakka a kansa; babu inda shakka ke iya goge yakini.

 

2.      Ga kuma tarin hadisai a kan halaccin auren, wadanda aka ambace su a tattaunawar da Naziru Fagge da Safiya Gusau suka gabatar kuma hatta irin su Ja’afar da R/Lemo ba su yi jayayya da su ko karyata su ba.

 

3. Cewa hadisan da ake dogara da su a kan haramcin mutu’a ba su inganta ba ta fuskar isnadi da ma’ana (don sun saba wa AlKur’ani), don haka ba su da karfin da za su iya goge hukuncin da ya tabbata a AlKur’ani.

4. Malaman Ahlul-baiti (wadanda ’yan Shi’a ke dauka a matsayin magadan ilimin kakansu) duk sun dace a kan halaccin mutu’a. Halattawarsu gare shi ne ma ya wanzar da tattauna wa a kansa a tsawon tarihin bincike da nazari. Da ma kuwa Annanbi [SAWA] ya fadi cewa ya bar mana su (Ahlul-baiti) tare da AlKur’ani, kuma ba za su taba rabuwa ba har su same shi a bakin tafkin Alkausara (Sahih Muslim 4/1873 hadisi na 2408).  

5. Cewa akwai Sahabban da suka tafi a kan rashin shafe hukuncin mutu’a har suka bar duniya.

6. Kara da cewa kowane irin dalili ya sa Shari’a ta halatta mutu’a a jiya, to wannan dalili na nan a yau. Kuma bukatar mutu’a a yanzu (da hayoyin fitinuwa suka wayaita) bai kasa bukatarsa a farkon Musulunci ba idan ma bai wuce ba.

7. Cikar Musulunci da Musulmi suka yi imani da shi kuma wanda AlKur’ani ya tabbatar da shi (al-Ma’ida: 3) yana nufin cikakkun tanaje tanajen da Musulunci ya samar ne, wadanda za su magance wa Musulmi duk matsalolinsu na rayuwa. Idan aka ce Musulunci ne ya share mutu’a to an tuhume shi da samar da gibi ga mabiyansa, wanda bai musanya shi da wani abu mai tasiri ba. Saboda azumi yana rage kaifin sha’awa ne ba biyan bukatar jima’i ba; saboda mabukaci ko ya yi azumi yana da bukata idan ya yi bude-baki; kuma azumi ba ko da yaushe ake yinsa ba; sannan akwai masu uzurin da aka sauke musu azumin farilla ma balle na rage sha’awa. Halin matsi da matsan da ba su da ikon aure na dindindin kan shiga a lokacin fizgar balaga ba shi da magani sai mutu’a, in ba haka ba kuwa sai zina ko dabarun fitar da maniyyi da hannu (wanda ke haifar da cutar saurin gama jima’i ga da namiji da barazanar kau da sha’awar mace gare shi gaba daya) barnar wadannan lamurra ga daidaiku da al’umma kuwa bayyane yake ga kowa. Wannan ya kore soki-burutsun Ja’afar na kore mutu’a da rashin kawo wa matasa kakkarfar mafita.

Mutu’a A Furu’a

A nan ne nake son yin gyra a kan sigar da wannan tattaunawa take tafiya. Wani abu da masu tattaunawar suka rafkana daga gare shi shi ne cewa kallon mas’aloli irin wannan ya kamata ya fi bayar da karfi ne ta mahangar furu’a. Saboda daukar matsayin halattawa ko haramta abu irin mutu’a yana bukatar wasu ilmummuka da suka wuce harshen larabci da karanta hadisai da tafsiri. Akwai kusan fannonin ilimi har guda tara (wasu sun kai su har goma sha daya) da ya kamata mutum ya kware (ba kawai ya san wani abu a kansu ba) kafin ya yi fatawa da halal ko haram a furu’a.

Masifar da aka jarabci al’ummar Musulmi a ’yan shekarun nan shi ne na wasu ’yan Ustazai da suka fito daga wasu jami’o’in wasu kasashen Larabawa, bisa dogaro da kalkala da kadifiri na magana da harshen larabci sai suka shiga dora mutane a kan abubuwan da suka saba wa mazahabobinsu na furu’a. Wannan kuskure ne babba. Dole ne mutum ya koma ga daya daga wadanda aka dace a kan ikonsu na iya shiga cikin wadancan ruwayoyi masu karo da juna da samar da mafita, don aiki da abin da suka yi fatawa a kai. Dole Ahlussunna su koma ga malamansu (bai halatta su dauki fatawar wasunsu don jin dadi kawai ba), haka ma dan Shi’a wajibi ne ya dogara da fatawar marja’i a kan komai har da mutu’a. Wannan shi ne abin da duk bangarorin biyu suka dace a kai.

Malaman furu’a sun kasu kashi biyu a kan auren mutu’a; akwai wadanda ijtihadinsu ya kai su ga halatta shi (wadannan su ne daukacin malaman Shi’a a jiya da yau, da wasu ’yan tsiraru daga malaman Ahlusunna); sai kuma galibin malaman Ahlussunna, wadanda  ijitihadinsu ya kai su ga  haramta shi. Amma duk da haka, malaman suna da wasu hukunce hukunce da suka dora mabiyansu a kai; misali mazhabar Malikiyya sun dace a kan cewa:

1. Idan dan Malikiyya ya yi mutu’a a raba auren.

2. Matar da a ka yi mutu’a da ita ta cancanci dukkan sadakin da aka dace idan mijin ya taba saduwa da ita, da rabin sadaki idan bai taba saduwa da ita ba.

3. Kar a yi musu haddi (ba bulala ba balle jifan zawarawa); sai dai wasu sun ce a tsawatar da su da wata ukuba da alkalin shari’a ya ga ta dace.

4. Idan aka sami ciki dan yana bin ubansa ne, kuma dan halal ne. Wannan ne ya sa Mal. Ja’far ya ba ni mamaki yayin da ya ce:  “duk dan da aka samu ta auren mutu’a ba dan aure ba ne!” alhali hatta a cikin Iziyya ta Shazili (wanda ake karanta shi daga matakin farko na karatun fikihu a kasar nan) an tabbatar da sabanin haka a Babi na Takwas a kan Aure da Saki (shafi na 201-202), da cikin Thamaruddani sharhin Risala ta Abu Zaid (shafi na 447).

5. Da yana gadon iyayensa bisa fatawarsu ta cewa dan na bin ubansa.

Su kuwa ’yan Shi’a da suke halatta shi, suma sun bayyana hukunce hukuncensa; wasu daga cikin wadannan hukunce hukunce sun hada da:

1- Sadaki sharadi ne a cikinsa; yana iya zama duk abin da ma’auratan suka dace a kai.

2- Idan ba a ambaci mudda a lokacin daura shi ya zama na dindindin.

3- Ba a wajabta gado tsakanin ma’aurata a cikinsa ba, sai a inda aka shardanta hakan a lokacin daura shi.

4- Babu saki a tare da shi, sai dai mijin yana iya yafe mata muddar da ta saura a duk lokacin da ya so.

5- Ciyarwa ba wajibi ne a cikinsa sai a inda aka sa shi a matsayin sharadi a lokacin kulla auren.

6- Ba shi da iyakantaccen adadi, mutum na iya yi da iyaka adadin da ya so.

7- Ba a yi da budurwa sai da izinin waliyyinta na Shari’a.

8- Makaruhi ne a yi mutu’a da wadda ta shahara da da zina da mai zaman kanta.

9- Ya halatta ayi azalu (fitar da maniyyi a waje) yayin saduwa ba da izininta ba.

Wadannan sharudda da ire-irensu masu yawa suna iya bayyana wa kowa cewa ba a shardanta mutu’a don barna ko sangarta mutane ko raunana auren dindindin ba; sai don kara kare al’umma da rage zafi ga wadanda ba su da ikon dauwamammen aure  ko wadanda suke bukatar karin lokaci don shirin auren dindindin da sauransu. Kar a manta da cewa ba don maza kawai aka shar’anta wannan auren mutu’a ba; mata ma za su iya cin gajiyarsa kusan fiye da maza. Yanzu zawarawa nawa ne suka share shekaru ba miji, ko saboda wahalhalu da suka sha a tsohon aurensu suke tsoron gaggauta sake aure; yaya irin su Ja’afar za su yi da sha’awar irin wadannan?

Wannan zai nuna kuskuren Ja’afar na kokarin nuna mutu’a da mummunan sura. Da dai zai takaita da ambaton fatawowin malaman furu’a da haka fi alheri gare shi da  al’umma baki daya. Kuma ya kamata kafin zargin masu halatta mutu’a Ja’afar ya ba kansa lokacin sanin ainihin abin da suke fada a kan auren, amma abubuwan da ya bayyana sun nuna bai san fatawoyin masu halatta mutu’a ba.

Idan Shari’a ta halatta mutu’a ne don manufar saukaka wa mutane, shawarar Ja’afar na takaita da auren dindindin ba ta da mahalli kenan. Mun dace da shi a kan kira zuwa ga bin Sunnar auren dindindin amma ba tare da haramta mutu’a ba. Kuma kasancewar Manzo [SAWA] ya yi auren dindindin bai cutar da halaccinsa ba, saboda Annabi ba duk halal ya ke yi ba. Kuma ai an halatta masa rike mata fiye da hudu bayan kuyangu; yanzu Ja’afar zai iya auren mata fiye da hudu? Ko yana da hanyar samun kuyangu? Sai dai idan ya halatta wa kansa tabi’ar auri-saki, wanda zaluncinsa bayyane yake ga kowa.

Kuma ina ba masu tattauna mas’alolin addini shawara da koyon ladubban tattaunawa. Yanzu ina amfanin zargin da Muh. Umar R/Lemo ya yi na cewa littattafan Shi’a “cike suke da karya da cakuda gaskiya da karya.” Wannan irin diban-karan-mahaukaciya da ya yi na hukunta “littattafan Shi’a” ya saba wa kowane irin mizani –na hankali da Shari’a. Irin wannan babban zargi ya kamata ya biyo bayan tarin misalai ne na wuraren da “littattafan Shi’a” suka yi karya da wuraren da suka “cakuda gaskiya da karya”. Ya sani cewa ba a kan wasu ’yan tsiraru yake magana ba; yanzu ’yan Shi’a a kasar nan sun wuce yadda duk yake tsammani a adadi da tasiri da karfi ta kowace fuska. Ba kore samun kuskure –kai hatta ma samun ganganta karya- nake yi ga littafan Shi’a ba, amma gamammen hukuncin nasa ne yake da sa kuka da dariya a lokaci daya.

Rufewa

Na yi kokarin yin bayani ne a kan matsayin auren mutu’a a tsakanin Musulmi. Ta bayyana cewa dukkan Musulmi sun dace a kan cewa asalinsa halal ne; amma sun saba a kan wanzuwar wannan halacci da goge shi. Akwai masu ganin wanzuwar wannan halacci akwai kuma wadanda suka tafi a kan cewa an goge shi; kowa ya dogara ne da hakkin da Musulunci  ya ba shi na yin ijtihadi, da yadda ya bar kofarsa a bude ga Musulmi a kowane zamani. Abin kuma sha’awa shi ne yadda Musulunci ke da fadin kirjin rungumar sakamakon ijtihadodin ’ya’yansa –matukar sun yi su bisa ka’idar yin ijtihadi- ta yadda ya ba duk wanda ya yi daidai a ijtihadinsa lada biyu na kokarinsa da samun daidai da ya yi; ya kuma ba da lada daya ga wanda ya yi kuskure saboda kokarinsa (Hadisin Bukhari ma ya tabbatar da haka).

Don haka abin takaici ne ganin yadda wasu ke kokarin takaita wa Musulunci fadinsa; da kokarin kakaba wa kansu rigar da ba ta su ba, da kokarin tilasta mutane a kan takurarren tunaninsu.Ya zama dole Musumi su kare kansu daga irin wadancan, ta hanyar lizimtar fatawoyin malamansu na furu’a da mujtahidan da suka cika sharuddan ijtihadi. Da hake ne kawai za su tsira daga fadawa rudani da rashin sanin kakkarfar majingina. Allah Ya sa mu dace amin.

Last modified on

57 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel