RAAF Official Website

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi Saba'in Zuwa Ga 'Yan Shi'a (1)

Rate this item
(6 votes)
Tafsir Kano [2012 (156) Tafsir Kano [2012 (156)

AMSOSHIN TAMBAYOYI SABA'IN ZUWA GA 'YAN SHI'A -1-
Daga
Saleh Muhammad Sani Zaria
P.O. Box 4167 - Kano
E-Mail: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
6/7/2007

 Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah madauwama su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAWA), da tsarkakan ‘Yan-Gidansa, da zababbun Sahabbansa da daukacin Annabawa da Manzannin Allah, da masu binsu da kyautatawa har ranar tashin kiyama.

 

Bayan haka, wannan yunkuri ne na amsa wasu tambayoyi saba’in da wani matashin Basalafe daga Sokoto, mai suna Mansur Ibrahim, ya furta su a wani wa’azin raba kan Musulmi da aka saba gudanar da irinsa a lokuta da yawa a kasar nan. Wata cibiya dake samun tallafi daga wasu kasashen Larabawa na Wahabiyawa da ake kira Cibiyar Ahlul-Baiti da Sahabbai dake da matsuguni a birnin Sokoto kuma take karkashin kulawar shi Mansur din ne ta shirya shi, a ci gaba da harkokin da aka kirkire ta don su. An furta wadannan tambayoyi ne a harabar Masallacin Sarkin Musulmi Bello (wanda ya kamata ya zama maharhadar dukkanin tunane tunanen Musulunci) dake daura da fadar mai martaba Sarkin Musulmi a birnin Sokoto (wanda ya kamata ya zama aminci ga dukkanin masu amsa sunan Musulunci a kasar nan ko mecece mazahabarsu kuwa). An gudanar da wannan taro na kokarin kawo kyamar juna tsakanin al’ummar Annabi (SAWA) ne a ranar 13 ga watan Zul-Qa’ada (wanda ke cikin watanni masu alfarma da aka hana Musulmi yakar Kafirai ma a cikinsa) na shekara ta 1427 bayan Hijra; daidai da 2 ga Disamba na shekarar miladiyya ta 2006 (daidai lokacin da Musulunci ke cikin mawuyacin halin da Kafirai suke son kau da shi daga samuwa gaba daya).

Tambayoyin sun iso gare mu tun a watan Disamba din da aka yi furuci da su ta hanyoyin ‘yan’uwa Musulmi da suka damu da hadin kan Musumi da ‘yan Shi’a na garin Sokoto da abin ya fi shafan su kai tsaye. Daga nan ne muka yi nazari a kan yiwuwar amsa su ko kyale su su tafi da lokaci kamar yadda irin haka ya faru a lokuta da dama, masamman bayan cikakkiyar masaniyar da muke da ita a kan kudurin makiya Musulunci na amfani da sabaninmu na cikin gida wajen rusa karfin Musulunci, bayan sun kasa cin mu da yaki ta hannun mujahidanmu a Iraki da Lebanon da Afganistan. Sai muka ga cewa taimaka wa Musulunci ta wannan bangaren bai kasa ta sauran bangarorin ba idan ma bai wuce su ba.

 

Wannan ya sa a karshe muka kudurta nazarin wadannan tambayoyi da dora su a ma’aunin Shari’a da hankali da tunani; sai sakamakon wannnan nazari ya nuna mahimmancin amsa su, don hakan ya zama tonon asirin masu furta irinsu ga dukkan al’umma.

 

Daga abin da mai tambayoyin ya gabatar kafin fara bijiro da tambayoyin nasa, mun fahimci abubuwa kamar haka:

 

 

 

ط       Tasirantuwa da tafiyar wasu da aka kira da “gwamnoni” ko “wakilan Shi’a” na jihohi da kananan hukumomi zuwa wani kwas na wata shida a kan Shi’a a kasar Shi’a ta duniya – Iran, shi ne ainihin dalilin wadannan tambayoyi.

 

ط       Don haka aka biojiro da tambayoyin a matsayin kalubale ga wadannan da suka dawo da abin da “suke ganin cewa ilimi ne” daga kwas din Shi’a.

 

ط       An bukaci su na Sokoto da su hadu da sauran ‘yan’uwansu ‘yan Shi’a na Nigeria; idan abin ya ci tura su hada da ‘yan Shi’a na duniya su gani ko suna samun amsoshin wadannan tambayoyi.

 

ط       Ya yi kira ga ‘yan Shi’a da su yi ikhlasi saboda yana kyautata musu zaton cewa Allah suke nufi.

 

ط       Idan har ‘yan Shi’a sun iya amsa wadannan tambayoyin, ya wajaba su –‘yan Salafiyya- su dunguma su fada Shi’a. Idan kuwa basu iya amsa su ba, to wajibi ne ga su ‘yan Shi’a su koma hanya (???), wadda ita ce turba ta gaskiya.

 

ط       Ya ba masu sauraronsa shawara da cewa idan har ‘yan Shi’a suka iya amsa wadannan tambayoyi to duk su fada Shi’a.

 

ط        Idan kuwa suka amsa bakwai daga cikinsu, to ya rantse da “Wallahi” zai koma Shi’a. (Ya maimaita wannan).

 

 

 

Abubuwan da za a lura da su ga amsoshinmu kuwa sun hada da:

 

 

 

ط       Mun san kowa ya kwana da sanin cewa masu wadanncan tambayoyi Salafiyawa ne Taimiyawa, wadanda suke da kallo na Musamman ba kawai ga sauran Musulmi ba, a’a ga sauran bangarorin Wahabiyawa ma na Izalar Kaduna da ta Jos. Don haka ba wai kawai muna sane da irin hannun rigar dake tsakaninsu da Ahlussunna ba ne, a’a mun kwana da sanin abin da ke akwai na sabani tsakaninsu da ‘yan Izala. Sun rungumi akidar mushirikantar da Ahlussunna da bidi’antar da su; suna kuma jahilantar da sauran ‘yan Izala da kauyantar da su. Wannan sananne ne ga kowa. Don haka a wannan amsa da wadanda suka yi da mu mu ke nufi.

 

ط       Za mu ambaci nassin tambayar, ko dukkanta ko takaito ta, daidai da yadda tsarinta da tsawonta suka kunsa, saboda saukaka wa mai karatu fahimtar tambayar.

 

ط       Akwai bayanin asasan da kowace tambaya ta doru a kansu da bayyana abin da ya inganta da wanda bai inganta ba daga asasan, wannan kuwa saboda mun samu mai tambayar ya jahilci mafi yawan abubuwan da ya so kawowa a tambayoyin nasa. Idan kuwa asasin tambaya ya baci, tambayar ma ta baci, idan kuma tambaya ta baci amsa ta ba shi da wata fa’ida kenan.

 

ط       Wasu tambayoyin ba na ‘yan Shi’a ba ne, na al’ummar Musulmi ne baki daya; kamar abin da ya shafi rikice rikicen da suka biyo bayan wafatin Annabi (SAWA) da abin da ya shafi barnace barnacen Yazidu da ire irensu. Wannan mun amsa masa su ne a madadin Musulmi baki daya; wannan yasa dole mu fadi dukkanin fuskokin da Musulmi suka kalli irin wadannan lamurra.

 

ط       A wasu amsoshion mun bayyana matsayi uku: matsayin  Ahlusunna da matsayin ‘yan Shi’a da matsayin Wahabiyawa/Salfiyawa/Taimiyyawa (wadanda duk dodo daya sukewa tsafi). So tari biyun farko sukan dace a kan sabanin abin da kashi na uku suke tafiya a kai.

 

Ga tambayoyi saba’in din a jere tare da amoshinsu; bisa tsarin fayyace kowace tambaya ta hanyar fitar da asasan da ta ginu a kai, tare da ambaton nassin tambayar da rassanta, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar takaito su saboda tsari da guje wa tsawaitawa.

 

 

 

TAMBAYA TA -1-

 

Asasinta:

 

a)     Yaradar kowa ne cewa Addini ya cika a ranar Arfa (???) da saukar Ayar Cikar Addini a Shekara ta goma bayan hijra.

 

b)     Tsammanin cewa sanin kowa ne (???) Shi’a da akidarta da siyasarta da harkarta duk sun bayyana ne bayan Manzo (SAWA).

 

Tambaya: Shin Shi’a tana cikin addinin nan da aka kammala a ranar Arfa? Idan tana cikinsa, yaya aka yi Annabi bai fade ta ba? Yaya aka yi Annabi bai gina addininsa a kanta ba? Yaya aka yi Annabi bai karantar da almajiransa ita ba. Idan kuwa bayan addini ya kammala ta zo to menene amfaninta?

 

 

 

AMSAR TAMBAYA TA -1-

 

Game da asasan tambayar nake cewa:

 

1-Babu shakka dukkan Musulmi sun yarda da cewa addini ya cika bisa asasin wannan aya ta cikin Surar al-Ma’ida dake cewa:

 

A yau na cika muku addinin ku, kuma na cika ni'imaTa a kanku, na kuma yardar muku Musulunci a matsayin addini.   Surar Ma'ida, 5:3.

 

Bambancin ‘yan Shi’a da wasu malaman bangarorin Musulmi a kan wannan shi ne cewa su sun yi imani da saukar ayar ne a ranar Ghadir, ita ce ranar da Manzo (SAWA) ya nada Imam Ali (AS) a matsayin Imami kuma shugaban Musulmi; wannan kuwa ya kasance ne a ranar 18 ga Zul-Hijjah na shekara ta 10 bayan hijra. Kuma Manzo ya cika wannan aiki ne a matakin karshe na rayuwarsa (bayan tun farkon sako ya yi ta nanata haka ta zantukansa da ayyukansa dabam daban).

 

Wannan fahimta ta Shi’a na saukar wannan aya a ranar Ghadir abin dacewa ne a tsakaninsu, don haka duk littafansu na tafisri (wadanda suka wuce arba’in) da litaffansu na ruwayoyi da hadisai (wadanda suka ninninka na Ahlussunna) sun tabbatar da haka a muhallinsa. Daga cikin mafassarar AlKur’ani na Ahlussunna da masu ruwayarsu ma akwai wadanda suka bayyana saukar wannan aya a ranar Ghadir a cikin littafansu, kamar Suyuti, a cikin tafsirinsa, a yayin fassarar wannan aya, inda ya fadi cewa:

 

An ambata, daga Ibin Mardawai da Ibin Asakir, dukkansu daga Abu Sa'id al-Khudri, ya fadi cewa: "A lokacin da Manzon Allah (SAWA) ya nada Ali (a matsayin Khalifa) a ranar Ghadir, ya kuma yi kira da a mika masa wilaya, sai Allah Ya saukar da wannan aya."[1]

 

Haka nan Abu Ja'afar Ibin Jarir al-Tabari ya ruwaito saukar wannan aya a ranar Ghadir Khum kuma a kan Ali (A.S).[2]

 

Haka nan Hakim al-Haskani ya ruwaito da Isnadinsa da ya kare da Abu Sa'id al-Khudri, cewa: “A lokacin da wannan aya ta sauka, Manzon Allah (SAWA) ya fadi cewa:

 

Allah Shi Ya fi girma, a kan cikan addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da manzancina da shugabancin Ali dan Abi Dalib a baya na.[3]

 

Ibin Kathir ya fitar a cikin tafsirinsa, ta hanyar Ibin Mardawai, daga Abu Sa'id al-Khuduri da Abu Huraira, cewa sun ce: "Wannan aya ta sauka ne a ranar Ghadir Khum a kan Ali."[4] Har ila yau ya fitar da haka a cikin tarihinsa.[5]

 

Don neman cikakken bayani a kan abin da ya gabaci haka da abin da ya biyo bayan haka da zantukan malaman Ahlussunna da na ‘yan’uwansu ‘yan Shi’a a kan haka, ana iya koma wa dan littafinmu mai suna Raddin Shubuhohi A Kan Ghadir da Nassosin Imamancin Ahlul-Bait (AS), wanda aka buga shi a wannan shekarar.

 

Don haka an dace a kan saukar ayar a kan cikan addini amma ba a dace a kan saukarta a ranar Arfa ba.

 

2-Dangane lokacin bayyanar Shi’a da akidarta da siyasarta da harkarta kuwa nake cewa: babu dacewa a kan haka, ba a tsakanin Shi’a da Ahlussunna kawai ba, har ma a tsakanin Ahlussunna an saba. Na tabbatar da wannan tun sama da shekaru goma a cikin littafina Tarihin Shi’a da Akidojinta, kuma na kara tabbatar da haka da fadi a bincikena na kwana kwanan nan a silsilar raddinmu ga Ja’afar Adam a Kano; sai a nemi littafin da laccarmu a kan haka a  kaset na 10, da na 11 da na 12.

 

Mu ‘yan Shi’a mun dace, da kalma daya, a kan cewa Annabi (SAWA) ne ya kafa Shi’a tun yana raye, kuma ya fara yin haka tun farkon aiko shi a yayin da Allah Ya hore shi da tsawatar da danginsa makusanta a cikin AlKur’ani Mai girma, inda Allah Ya ce:

 

Ka tsawatar da danginka makusanta (Shu’ara 26:214)

 

Masu tafisiri da tarihi da malaman Sababul-Nuzul sun yi gab da dacewa a kan cewa yayin da wannan aya ta sauka Manzo (SAWA) ya tara danginsa makusanta na daga ‘ya’yan Abdul-Mutallibi ya kuma kira su zuwa ga Musulunci a karshe ya ce musu:

 

Wanene a cikin ku zai zama mataimakina a kan wannan al’amari; a kan ya zama dan’uwana kuma abin wasicina kuma Khalifana a bayana?

 

Sai Ali (AS) ya mike ya ce: “Nine ya Annabin Allah!” Sai Manzon Allah (SAWA) ya dafa kafadansa ya ce: “Wannan dan’uwana ne, kuma abin wasicina kuma Khalifana a cikinku ku saurare shi kuma ku yi masa biyayya.”

 

Don samun wannan bayani ta bangaren ‘yan’uwa Ahlussunna duba littafai masu zuwa:

 

v      Tafsirin Tabari, wajen fassarar wannan aya.

 

v      Tafisrin Bagawi, wajen fassarar wannan aya.

 

v      Tarikh al-Umam wal-Muluk na Tabari, juz’I na 2 shafi na 217.

 

v      Al-Kamil Fi al-Tarikh na Ibin al-Atheer, juz’I 2, shafi na 62-64.

 

v      Siratul-Halabiya, juz’I na 1, shafi na 461.

 

Irin wadannan nassosi da laffuza makusanta sun yawaita daga Manzon Allah (SAWA) ta hanyoyin dukkan bangarorin Musulmi. Illa dai kowa na da fassararsa a kanta, wadda a kan ta ne yake gina akidarsa da siyasarsa da sauran lamurran addininsa.

 

Na’am gaskiya ne cewa Ibin taimiyya, wanda ya gina akidarsa a bisa asasin saba wa dacewar Musulmi da kayata abin da ya inganta a wajensu, ya gina mabiyansa a kan karyata wannan nassi, kamar yadda ya bayyana haka a cikin littafinsa Mihajul-Sunna, juz’i na 4, shafi na 80. Karyatawarsa kuwa ba hujja ba ce a wajen malaman Ahlussunna na hadisi, wadanda suka tabbatar da rashin adalcinsa a kan abin da ya shafi Ali da ‘ya’yansa, balle kuma ‘yan Shi’a.

 

 Kai! Hatta kalmar ta Shi’a (da ma’anarta na bin Ali da kebabbun ‘ya’yansa) Manzon Allah (SAWA) ne ya fara furta ta a cikin wannan al’ummar. Biyu ba sa sabani a kan haka a tsakanin ‘yan Shi’a domin hakan ya inganta ta hanyoyinsu, a wasu lokuta ma har ta hanyoyin Ahlussunna. Misali Ibin Jarir al-Tabari ya fitar a cikin tafsirinsa a lokacin fassarar wannan aya dake cewa:

 

Lallai wadanda suka yi imani suka kuma aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafi alherin halitta” (al-Bayyinat aya ta 7-8). Cewa An karbo daga Abul-Jarud, daga Muhammad dan Ali cewa Manzon Allah (SAWA) ya fada (dangane da fadar Allah mai cewa): “….wadannan su ne mafi alherin halitta” cewa: “Ya Aliyu! kai ne da ‘yan Shi’arka.”[6]

 

Suyuti ma, a cikin tafsirinsa, ya yi bayanin haka da cewa:

 

Ibin Asakir ya fitar daga Jabir bin Abdullahi ya ce: “Mun kasance a wajen Annabi Allah (SAWA) sai Ali ya fuskanto inda mu ke, sai Annabi (SAWA) ya ce: ‘Na rantse da wanda raina ke hannunSa, cewa wannan (yana nufin Ali) da ‘yan Shi’arsa su ne masu babban rabo ranar kiyama.’ Sai ayar (Surar Bayyinat aya ta 7-8) ta sauka. Daga nan Sahabban Annabi suka kasance duk lokacin da Ali ya fuskance su sukan ce: Mafi alherin halittu ya zo.[7]

 

Ibin Hajar al-Haithami ya sa ta cikin jerin ayoyin da suke bayanin falalar Ali (AS) a cikin littafinsa AL-Sawa’ik al-Muhrikah, inda ya ce:

 

Aya ta goma sha biyar (cikin jerin ayoyin da ke nuna darajojin Ali) ita ce fadar Allah (SWT) mai cewa: Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafi alherin halitta, Hafiz Jalaluddin  al-Zarandi ya fitar daga Ibn Abbas cewa: “Yayin da wannan aya ta sauka, Annabi (SAWA) ya cewa Ali dan Abi Dalibi: ‘(mafi alherin halittu) su ne kai da ‘yan Shi’ar ka. Za ka zo kai da ‘yan Shi’ar ka ranar kiyama alhali kuna masu yarda (da abin da za ku gani) kuma wadanda aka yarda da ku; kuma makiyin ka zai zo alhali ana fushi da shi kuma wulakantacce’.” Sai Imam Ali (AS) ya ce: “Wanene kuma makiyi na?” Sai Annabi (SAWA) ya ce: “Wanda ya yi maka bara’a kuma ya la’ance ka”.[8]

 

Amma ‘yan’uwa Ahlussunna sun sassaba ne kamar yadda bayani ya gabata. Akwai masu ganin bayyanarta a lokacin Annabi (SAWA), kamar yadda ‘yan Shi’a ke gain, irin su Ustaz Muhammad Abdullahi Anan, dan kasar Masar, kamar yadda ya nuna haka a cikin littafinsa al-Jam’iyyatus-Sirriyyah, inda ya ke cewa:

 

Babban kuskure ne a fadi cewa Shi’a sun fara bayyana ne yayin da Khwarijawa suka balle, da cewa ana kiran su  da wannan suna ne saboda sun saura a bangaren Ali; gaskiyar al’amarin dai shi ne cewa Shi’ar Ali sun bayyana ne tun lokacin wafatin Annabi (SAWA)…..

 

Amma mafi yawa daga cikinsu suna ganin cewa Shi’a (da ma’anar bin Ali) ta bayyana ne a sakamakon yadda lamurra suka kaya bayan wafatin Annabi (SAWA). Daga cikin irin wadannan akwai Dr. Ahmad Amin, wanda ya ce:

 

Tushen farko na Shi’a wasu mutane ne a  bayan wafatin Manzo (SAWA), wadanda suka ga cewa Ali da Mutan-Gidansa ne suka fi cancantar su Khalifancinsa.[9]

 

Sanannen abu ne cewa wadannan da ya kira da “Wasu Jama’a” daga Sahabbai suka kasance. Ya’akubi ya ambace su a cikin tarihinsa da cewa su ne:

 

1-Abbas dan Abdul-Mudallab.

 

2-Utbatu dan Abi Lahab.

 

3-Salman al-Farisi.

 

4-Abu Zarr al-Giffari.

 

5-Ammar bin Yasir.

 

6-Mikdad bin Aswad.

 

7-Bara'a bin Azib.

 

8-Sa'ad bin Abi Wakkas.

 

9-Ubayyu bin Ka'ab.

 

10-Dalhatu bin Ubaidullah.

 

11-Daukacin Banu Hashim tare da wasu mutane daga Muhajirai da wasu daga Ansar.[10]

 

Wasu daga cikinsu kuma sun dangana bayyanar Shi’anci da lokacin Usman, tare da dangana rikice rikicen da suka haifar da kashe Usman din da bayyanar Shi’a. Masu wannan ra’ayi sun jona Abdullahi bin Saba’a da bayyanar Shi’a tare da dora masa alhakin haddasa rikicen rikicen da suka faru a tsakanin Sahabbai a lokacin, wanda ya tafi da ran Khalifa. Wannan shi ne ra’ayin duk mai fada da Shi’a (da kowane irin dalili yake fadan); saboda imanin cewa ya fi biya musu bukatarsu.

 

Wannan ra’ayi bai samu karbuwa daga masu tantace tarihi da bin diddiginsa irin su Allama al-Askari (daga malaman Shi’a) da Dr. Taha Hussaini (daga malaman Ahlussunna) ba. Na farkon (malamin Shi’a) yana da littafi mai mujalladai biyu a kan Abdullahi bin Saba’a, inda ya auna zantukan masu tarihi da masu hadisi da ma’aunan da bangarorin biyu suka saba kimanta labarai, sai kissar Ibin Saba’a ta raunana daga tushenta. Shi kuwa Dr. Taha Hussaini ya kalli raunin abun ne ta nazarin abubuwan da suka faru a lokacin da ake hasashen bayyanar Ibin Saba’a, sai ya fitar da sakamakon cewa Abdullahi bin Saba’a tatsuniya ce da makiya Shi’a suka tanade ta don fadan da suke yi. Ya kara da tabbatar da cewa yarda da haka wawantar da magabata ne na daga Sahabbai da nuna su a matsayin sakakkun da kowane mutum ke iya kutsawa cikinsu ya yi tasiri wajen kirkirar rikice rikice da akida ba tare da sun lura ba (koma ka duba cikakken zancensa a cikin littafinsa al-Fitnatul-Kubra, wajen bayanin kashe Usman).

 

Daga cikin Ahlussunna wadanda suka tabbatar da cewa Abdullahi bin Saba’a tatsuniya ce kawai akwai:

 

1-     Dr. Suhail Zakar, wanda ya yi tahkikin littafin al-Muntazam na Ibin al-Jauzi, a juz’I na uku, a hamishin shafi na 302, inda ya ce: “Abin da ya fi rinjaya shi ne cewa ba a taba yin wani wai shi Ibin Saba’a ba; mutum ne da aka kirkire shi kawai.”

 

2-     Dr. Abdul-Aziz al-Hilabi, malami a Sashen Tarihi na Jami’ar Sarki Sa’ud dake Riyadh, wanda ya kebe littafi kan Abdullahi bin Saba’a, a shafi na 71 ya rubuta cewa:

 

Abun da zamu iya takaitawa daga wannan bincike na mu shi ne cewa Abdullahi bin Saba’a tastuniya ce; don ba a taba yinsa ba. Idan kuwa har an samu wani mutum da wannan sunan to babu shakka bai aikata abin da Saif (wanda shi kadai ya ruwaito kissar Ibin Saba’a) da masu littafan dake bayanin addinai ke dangana masa ta fuskar siyasa da addini ba.

 

3-     Ahmad Abbas Saleh, a cikin littafinsa al-Yaminu wal-Yasaru, shafi na 95.

 

Idan wannan ya tabbata, to zancen cewa “Shi’a da akidarta da siyasarta da harkarta duk sun bayyana ne bayan Manzo (SAWA)” ya wargaje; saboda haka ba sananne ba ne ga masana da masu bin diddigi daga dukkan bangarorin.

 

Wannan ya bar mu kenan da cewa ‘yan Salafiyya, kamar yadda suka saba, sun zaba wa kansu yarda da cewa an kirikiri Shi’a ne a bayan Annabi (SAWA) don su ci gajiyar haka wajen ruda wawaye da jahilai daga masu sauraronsu.

 

Mu kuwa ‘yan Shi’a muka ce, Annabi (SAWA) ne ya dasa Shi’anci tun yana da rai, ta hanyar furta ta da bakinsa, da yi mata ban-ruwa da maganganu da ayyukansa, duk wannan don Shi’ancin ya yi amfani wajen kare Musulunci daga sauye sauyen dake iya samunsa bayan wafatinsa. Wannan kuwa shi ne abin da Shi’anci ya aikata a jiya, yake kuma aikatawa a yau, zai kuma ci gaba da aikatawa a gobe da yardar Allah.

 

 

 

Amsar Tambayoyin

 

Yansu zamu iya amsa tambayoyinsa, a bisa wadannan asasai da muka ambata, da cewa: Shi’anci ba kawai yana cikin addinin Musulunci ba ne, a’a shi ne ma dan Musulunci na halas, wannan kuwa saboda:

 

ط       Shi ne dan fari da Musulunci ya Haifa bayan bayyanarsa. Kuma Annabi (SAWA) ne ya yi masa zanen suna, kuma shi ya fara furta shi da bakinsa mai albarka.

 

ط       Annabi (SAWA) ya gina addinsa a kan mika wilaya ga Ali da tsarkakan ‘Yan-Gidansa bisa horon Allah (SWT); kuma ya karantar da Sahabbansa a kan haka, kuma an samu wadanda suka fahimci karatun sannan suka yi aiki da shi, kamar yadda aka samu wadanda suka fahimta suka kau da kai; kai! akwai ma wadanda ba su fahimci karatun ba kwata kwata. Haka lamari ya kasance ga wadanda suka biyo bayan Sahabbai na daga Tabi’ai da Tabi’ut-Tabi’in har zuwa yau din nan. Wannan kuwa shi ne halin dan Adam a tawon tarihinsa a doron wannan kasa.

 

ط       Cikan Addini da wannan aya ta Surar Ma’ida ke Magana ya tabbata ne da wilaya ga Ali bin Abi Talib (AS), wanda hakan ne asalin Shi’anci ba wani abu dabam ba.

 

Ta mu Tambayar gare shi a kan haka ita ce:

 

ط       Shin Wahabiyanci yana cikin addinin nan da suka yi imanin a Arfa aka kamala shi? Idan yana cikinsa, ya ya aka yi Annabi bai fade shi ba? Ya ya aka yi Annabi bai gina addininsa a kansa ba? Yaya aka yi Annabi bai karantar da almajiransa shi ba.

 

ط       Idan har ya yi haka a ina ya yi? A kawo mana bayanannun dalilai a kan haka –kamar yadda muka kawo a namu- ba tawile tawile ba.

 

ط       Idan kuwa Ibin Taimiyya ne ya halicce shi a karni na takwas, kuma Ibin Abdul-Wahab ya yita kokarin sa masa suna (duk da hakan ya gagara, har yanzu yana nan sai sace sunan wasu ake yi ana ba shi) kuma shi ya yayyafa masa rayuwa a karni na sha daya, to meye amfaninsa?

 

ط       Shin akwai wani hadisi daga Manzo (SAWA) –ko da kuwa rarrauna ne- da ya furta Ahlussunna da bakinsa irin yadda ya furta Shi’a?

 


 

 


 

[1]Suyuti, Durrul-Manthur Fit-Tafsiri Bil-Ma’athur, wajen fassarar wannan aya.

 

[2]Ya zo cikin littafinsa mai suna Kitabul-Wilaya.

 

[3]Haskani, cikin Shawahidut-Tanzil, wajen fassara wannan aya.

 

[4]Tafsirin Ibin Kathir, juzu'i na 2, shafi na 14.

 

[5] Tarihin Ibin Kathir, juzu'i na 5, shafi na 210

 

[6]Tabari, Ibin Jarir, Tafsirul-Kur’an, juz’i na 30, shafi na 171wajen fassarar wannan aya.

 

[7] Suyuti, Durrul-manthur Fil-tafsiri bil-Ma’athur, wajen fassarar wadannaa ayoyi.

 

[8]Ibin Hajar al-Haithami al-Makki, al-Sawa’q al-Murikati Lir-raddi ala ahlil bida’i wal-Zandikati, shafi na 182

 

[9]Ahmad Amin, Fajarul-Islam, shafi na 266, bugun Beirut.

[10]Ya’akubi, Tarikh al-Ya’aqubi, Juz’I na 2, shafi na 124, bugun Beirut. Haka nan Zubair bin Bakar, cikin littafin al-Muwaffaqiyyat, shafi na 580.

Last modified on

74 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel