RAAF Official Website

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi Saba'in Zuwa Ga 'Yan Shi'a (2)

Rate this item
(3 votes)
Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya

AMSOSHIN TAMBAYOYI SABA'IN ZUWA GA 'YAN SHI'A -2-
Daga
Saleh Muhammad Sani Zaria
P.O. Box 4167 - Kano
E-Mail: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
6/7/2007

 Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

TAMBAYA DA AMSA TA 2-6

Asasan da aka gina tambayoyin a kai:

 

1)    Shi’anci ya ginu ne a kan Imamancin Ali bin Abi Talib (AS), wanda shi ne Imami na farko! A kan haka ake kiransu Imamiyya.

 

2)    Shi’a suna ganin cewa tun da Annabi (SAWA) ya yi wasici da Imamancin Ali da zuriyarsa a bayansa, to haka duk wanda ya zo ya yi mulki kafin Aliyu (Khalifofin nan uku) a gurin ’yan Shi’a ’yan kwace ne, azzalumai ne.

 

3)    Shi’a na ganin Imamanci a matsayin mafi girman rukunnan addinin Musulunci, wanda duk sauran rukkunna ba su kai shi ba.

 

4)    Babu ambaton rukunin Imamancin Ali (AS) a cikin AlKur’ani, alhali kuwa ya ambaci komai daki-daki.

 

5)    Annabi (SAWA) bai ambaci cewa wanda ya kwace mulki a hannun Ali da ’ya’yansa azzalumai ba ne.

 

6)    Shigan Ali (AS) cikin kwamitin da Umar ya kirkirsa don zaben Khalifa a bayansa ya yi karo da akidar nassi a kan Khalifancinsa.

 

7)    Daga mutum shida na kwamitin mutane shida da Umar ya kirkira mutum hudu sun janye sun bar Ali da Usman, daga nan kuma Musulmi suka zabi Usman suka bar Ali (AS). A nan ma Ali bai fito ya yi da’awar nadin da Manzo ya yi masa ba.

 

8)    Duk shugaba dole ya zama shi ne liman. Ga shi kuma duk littafan tarihi na Shi’a da na Ahlussunna sun dace a kan cewa Annabi (SAWA) ya hori Abubakar ya yi limanci alhali bai taba horon Ali da ya yi limanci koda sau daya.

 

 

 

Nassin Tambayoyin

 

1)    Me yasa wannan rukunin babba ba a ambace shi a cikin AlKur’ani ba? Ga shi kuwa Allah Ya fadi dukkan sauran rukunnan da su ’yan Shi’a suke ganin ba su kai shi ba! Gashi kuwa Allah (SWT) Ya fayyace abubuwa daki-daki, tun daga Sallah, tsarki har farauta

 

2)    Me yasa a cikin AlKur’ani babu aya ko daya, wadda ta ce Imam Ali (AS) shi ne Imami bayan Manzon Allah (SAWA)?

 

3)    Kun ce Aliyu Allah Ya ba wannan hakki, kuma duk wanda ya zo kafin shi kwace ya yi! To me yasa Ali ya shiga cikin kwamitin da Uamar ya hada kafin ya rasu don zaben Khalifa a bayansa?

 

4)    Yayin da uku suka janye suka bar wa uku (su ne Ali da Usman da Abdul-Rahman bi Auf). Kuma da Abdul-Rahman ya janye, aka bar Ali da Usman, sannan aka yi kuri’a tsakanin Musulmi aka zabi Usman, me yasa Ali ya ki cewa ai dama ni Allah ya zaba?

 

5)    Me yasa Annabi bai fadi irin abin da ya fada wa kabilar banu Talha, wadanda ke tsaron Ka’aba, a lokacin da ya ari makullinsu ya bude Ka’aba bayan ya bude Makka ba, wannan shi ne fadarsa (SAWA): “Ku karbe shi (makullin) ya ku banu Talha! Tabbatacciya ta dindindin a cikin gidanku ba mai karbarsa a hannuku sai azzalumi.” To idan har Manzo (SAWA) ya fadi haka ga banu Talha, mai yasa bai fadi irin haka ga wannan Imamanci na Ali (AS) ba.

 

6)    Me ya sa Manzon Allah (SAWA) bai umurci Ali ya ba da sallah koda sau daya ba kafin ya bar duniya? Tare da sanin cewa ba mai ba da sallah sai shugaba. Ko a littafin Shi’a ko a na Sunni ba inda aka ambaci cewa Annabi (SAWA) ya hori Imam Ali (AS) ya limanci Sallah ko sau daya, alhali littafan duk bangarori biyun sun tafi a kan cewa Abubakar ya limanci Sallah.

 

 

 

AMSAR TAMBAYA TA 2-7

 

 

 

Game da asasan da ya gina wadannan tambayoyin nake ce masa:

 

Akidar Imamanci A Shi’a

 

1)            Babu shakka kan cewa akidar Imamanci ita ce ruhin Shi’anci da ta bambanta shi da sauran mazhabobin akida na Musulunci; kuma da wannan ne suka sami sunansu na Imamiyya. Muna alfahari da haka, kuma mun yi imani da cewa da wannan akida muna matsayin da Allah (SAWA) yake bukata, muna kuma rokonSa Madaukaki da Ya sa mu zama masu gaskiya a kan wannan akida, Ya kuma karba daga gare mu.

 

2)        Zancen kiran wadanda suka yi Khalifanci kafin Ali (AS) a matsayin ’yan kwace kuma azzalumai, wannan wani zargi ne da ya fade shi da ka, ba tare da ya dangana shi da wani Imami daga Imaman Ahlul-baiti (AS) da littafin da aka fitar ba, balle mu ambata masa fassarar maganar da abin da take nufi. Da dai ya yi haka da amsa masa ta zama dole. Duk da haka, wannan na iya daukar ra’ayi da fahimtar wani daga cikin malamaan Shi’a ko mai nazarin lamurra daga cikin su; wanda ko dai ya yi daidai a kan hakan ko ya zama ya yi kuskure. Idan lamarin ya zama tabbatacce ne a wajen Allah (SWT), to ai ba wani abin zargi ga wanda ya yarda da shi. Idan kuwa ya zama kuskure ne, to dukkanin mu mun dace a kan cewa Allah Ya dauke alkami a kan wanda ya yi kuskure! Kai, idan ma a matsayin ijtihadi ne, mai kuskuren har lada yake da shi (bisa hadisin da Bukhari ya fitar, kuma Ahlussunna suka inganta shi).

 

Wani abu dake da mahimmanci a nan shi ne cewa irin wannan bambancin ra’ayi a kan matsayin Khalifofin da suka zo kafin Ali (AS) ya wuce haddin lokacin mu; har a tsakanin Sahabbai ma an same shi. Daga cikin wata doguwar muhawara da ta faru tsakanin Umar  bin Khattab da Ibin Abbas a kan haka, wadda malaman tarihi –hatta na Ahlussunna- irin su Tabari suka fitar akwai fadar cewa:

 

Umar ya ce wa Ibin Abbas: "Labari ya zo min cewa kai kana fadin cewa an kawar da shi (Khalifanci) daga gare ku (dangin Manzo) ne bisa hassada da zalunci." Sai Ibin Abbas ya ce: "Amma fadar cewa bisa zalunci; to ai wannan bayyananne ne ga jahili da wanda ya sani. Amma fadar cewa bisa hassada ne, to ai an yi wa Adamu hassada; mu kuma ’ya'yansa ne wadanda ake yi wa hassada."[1]

 

Don haka don an sami wata fahimta daga na baya, wadda aka samu irin ta daga magabata na daga Sahabbai, wannan wani abu ne karbabbe a wajen dukkanin mu.

 

3)  Amma fadar cewa ’yan Shi’a na “ganin Imamanci a matsayin mafi girman rukunnan addinin Musulunci, wanda duk sauran rukkunnan ba su kai shi ba”, wannan ya nuna bai san yadda Shi’a suka kasa rukunnan addini ba; domin kuwa babu malamin da ya fadi haka; ina kalubalantarsa da ya fadi inda ya ga wannan magana da wannan ma’anar. Wace irin kwakwalwa ke iya yarda da mahimmancin reshe fiye da tushe? Ba don imani da Allah ba ta ina za mu samu hanyar imani da ManzonSa? Sannan ta ina za mu sami hanyar Imani da Imamai, wadanda su ne Khalifofin ma’aiki bisa nassi, in ba ta hanyar imani da Manzon ba? ’Yan Shi’a na ganin mahimmancin rukunin Imamanci ne bisa la’akari da cewa yawa yawn Musulmi sun yi rikon-sakainar-kashi da wannan asali, ta yadda suka yarda da cewa kowane fasiki ma yana iya samun hanyar hawa wannan mukami mai tsarki. Amma fadin haka da ma’anar cewa ya wuce sauran rukunnan addini babu malamin Shi’a da ya fade shi, kuma babu gama-garin Shi’a da ya yi imani da shi.

 

Tsarin akida a Shi’a ya kasa Rukunnan Addini (Usuluddin) zuwa gida biyar ne kamar haka:

 

a).   Tauhidi: Shi ne imani da kadaicin Allah (SWT) a samuwarSa, da ZatinSa, Siffofinsa, da bautarmu gare Shi da sauransu.

 

b).   Adalci: Suna daukar wannan a matsayin reshen Tauhidi, sun kebe masa babi mai cin gashin kai ne saboda yawan sabani da ya shiga tsakanin Musulmi a kan ma’anar adalcin Allah da irin babobin da ya taro.

 

c).   Annabci: Shi ne imani da manzancin Manzo (SAWA) da cewa shi ne karshen manzanni, da imani da ismarsa daga kowane irin kaucewa daga hanya, bisa sani ko bisa kuskure ko mantuwa da sauran abubuwan da suka shafe shi (SAWA) da sakonsa.

 

d).   Imamanci: Suna daukan wannan a matsayin reshen Annabci. Ya tanadi imani da ci gaban shigabancin da Annabi ya fare shi karkashin wadanda Manzo ya yi wasici da su; da cewa Manzo ya yi wasici da wasu kebabbu daga zuriyyarsa saboda tanajin da Allah ya yi musu don wannan babban aiki; da imani da ismarsu da sauran abubuwan da suka shafi Imamanci. Kuma kasancewar ’yan Shi’a ne kawai suka yi imani da Imamanci a matsayin rukunin addini kuma suna tattauna shi ta wannan mahanga, koma bayan sauran mazhabobin Musulunci, wannan ya sa suke alamta rukunin Imamanci da “Rukunin Mazhaba” (Usulul-Mazhab).

 

e).   Makoma: Shi ne imani da cewa bayan wannan rayuwa akwai wata bayan mutuwa, wadda a cikin ta ne kowa zai fuskanci abin da ya aikata. Tare da imani da abubuwan da ranar ta kunsa na hisabi da wuta da Aljanna da Siradi da sauran abubuwan da suka tabbata a zahirin AlKur’ani da ingantattun Hadisai.

 

Bayan wannan bayani muna iya tambayar Mansur daga ina ya ga an fadi “Imamanci a matsayin mafi girman rukunnan addinin Musulunci, wanda duk sauran rukkunna ba su kai shi ba?” 

 

Da wannan nake ganin Mansur ba shi da hurumin yin magana a kan akidar Shi’a saboda ba shi ma da masaniya a kan yadda tsarin tushen akida yake a wajen su, abin da shi ne farkon abin da ya kamata kowa sani a kan kowace mazhaba!

 

Imamanci A AlKur’ani

 

 4) Amma fadar cewa babu rukunin Imamanci a cikin AlKur’ani, wannan yana kara tabbatar da jahilcinsa ne a kan dalilan da Shi’a suka gina akidarsu. Saboda dalilai biyu ’yan Shi’a suke gina akida a kansu, wadanda sune abin da sallamammen hukuncin hankali ya hukunta da abin da tabbataccen Nassi, wanda shi ne Zahirin AlKur’ani ko sahihin Hadisi ya bayyana. Mu ba ma ganin bambanci tsakanin abin da zahirin AlKur’ani ya hukunta da abin da sahihin Hadisi ya karantar. Yau da ace ma AlKur’ani bai yi zancen Imamanci ba (kamar yadda yake da’awa) amma sai ingantattun Hadisai wdanda babu shakka a kan fitowarsu daga Manzo (SAWA) suka yi horo da imani da Imamancin Imamai (AS), da wannan ya wadata ya sa mu dauke shi da mahimmanci daidai da yadda Hadisan suka karantar; saboda a iyaka fahimtarmu horon Annabi (SAWA) horon Allah (SWT) ne; haninsa kuma haninSa ne kamar yadda AlKur’ani din ya yi ta nanatawa, kamar fadarsa:

 

Duk Abinda Manzo ya zo muku da shi ku karba, abin da kuma ya hane ku ku hanu. Al-Hashari (59): 7.

 

Da fadarsa cewa:

 

Ba ya halatta ga mumini ko mumina idan Allah da ManzonSa suka hukunta wani abu ya zama suna da wani zabi na su, wanda kuwa ya saba wa Allah da ManzonSa hakika ya bata bata bayyananniya. al-Ahzabi (33): 36.

 

Da cewa:

 

Wanda ya bi Manzo hakika Allah ya bi, wanda kuwa ya juya baya, to bamu aiko ka a matsayin mai sa ido a kan su ba Al-Nisa’i (4): 80.

 

Ya kuma ce:

 

Ya ku wadanda ku ka yi imani ku bi Allah da Manzonsa da majibitan al’amari daga cikin ku…Al-Nisa’i (4): 59.

 

Mun fahimci sabaawa horon Manzo (SAWA) a kan komai (ba kawai horonsa a kan abin da ya shafi Imamanci ba), yana haifar da fuskantar azabar Allah (SWT). Allah Ya ce:

 

Masu saba wa horonsa (Manzo) su ji tsoron haduwa da wata fitina ko su hadu da azaba mai radadi. Al-Nur:63.

 

To balle kuma AlKur’ani ya yi magana a kan Imamancin Ahlul-bait (AS) a wasu wurare na ayoyinsa kamar haka:

 

a).   Ayar Imamanci A Tsatson Annabi Ibrahim (AS): Ita ce ayar dake alkawarta wa Annabi Ibrahim wanzuwar Imamanci a tsatsonsa a lokacin da Allah Ya ba shi mukamin Imamanci, kari a kan Annabci, bayan ya ci duk jawarabawar da Allah ya yi masa. Ayar ta ce:

 

Ku tuna lokacin da Ubangijin Ibrahimu Ya jarrabe shi da wasu kalmomi sai ya cika su, Ya ce: “Ni zan sanya ka Imami ga mutane.” Sai (Ibrahimu) ya ce: Har ma daga zuriyyata.” (Sai Allah) Ya ce: “Azzalumai ba za su samu alkawarina ba.” Al-Bakara:124.

 

Wannan aya ita ta bijiro da nazarin Imamanci da mafi kyawun fuska. Saboda tana bayar da ainihin tushen akidar ta Imamanci ne da abubuwan da ta kebanta da su. Ga mahimman darussan da ake iya dauka daga ayar kamar haka:

 

i).       Imamanci sakamako ne na jarabawar Allah (SWT) ce (Waithibtala), wadda kuma aka yi nasara a kanta da cikakkiyar siga (Fa’atammahunna).

 

ii).      Irin wannan Imamancin wani matsayi ne sabanin Annabci. Domin an nada Ibrahim a matsayin ne bayan ya riga ya zama Annabi, saboda amfani da sigar (Inni Ja’iluka), wadda siga ce ta Sunan Fa’ili (Ismul-Fa’il) wadda ba ta inganta  ayi amfani da ita a kan abin da aka riga aka yi shi, sai wanda ake yi a lokacin da ake fadar ta; ko a lokacin da zai biyo bayan maganar –sai a lura da kyau.

 

iii).    Ibrahim (AS) ne ya roki Imamanci ya saura ga tsatsonsa (Wa min zirriyyati), kuma Allah Ya amsa masa.

 

iv).    Wannan matsayi na Imamanci Allah Ya kebance shi ne ga wasu “zababbu” daga Zuriyyar Ibrahim (AS), ba dukkansu ba (La yanalu ahdi az-zalimin); azzalumi a nan shi ne mai ajiye abu a sabanin mahallinsa –wato wanda ba ma’asumi ba.

 

v).     Imamanci alkawarin Allah ne (‘Ahdii); ba matsyin “zabe” ko “shawara” ko hakkin “masu kullawa da kwancewa” daga mutane ba ne.

 

vi).    Imamancin da Allah Ya ba Annabi Ibrahim (AS) da zababbu daga Zuriyyarsa shi ne shugabancin al’amarin addini da na duniya tare; wanda ba duka Annabawa ne suka sami wannan mukami ba.

 

vii).  Mukamin Imamanci na iya haduwa da Annabci -kamar yadda ya hadu a kan Annabi Ibrahim (AS); kuma ta gangaro kan babban jikansa da ya fi shi mukami, wato Annabi Muhammad (SAWA); haka ana iya samun Annabi ba Imami ba –kamar yawa yawan Annabawan da suka gabaci Ibrahim da wadanda suka zo bayansa. Kuma Imamanci na iya samuwa ga wanda ba Annabi ba, kamar yadda ya faru ga “zababbu” daga Zuriyyar Annabi (SAWA) –wadanda su ne ci gaban tsatson Annabi Ibrahim (AS).

 

viii). Wannan Imamancin ne Kalmar nan da Allah Ya ambace ta da cewa:

 

Ya kuma sanya ta kalma ce mai wanzuwa a Zuriyarsa don (wadanda ake kira) su dawo (kan hanya). Al-Zukhrufi:28.

 

Wannan dan bayani kadan ne daga dadadan jawaban malaman Shi’a a kan tushen Imamanci da asalinsa a cikin AlKur’ani mai girma. Kamar yadda kowa ke iya gain, fahimtar ta samo asali ne daga kyakkyawan fahimtar AlKur’ani. Kai sunan ma na Imamanci daga nan Shi’a suka samo shi.

 

Bayan wannan aya da ta bayyana ruhin Imamanci da tushensa, akwai tarin ayoyi da mu ’yan Shi’a muka fahimci suna dora mu ne a kan akidar Imamancin Ali (AS) da tsarkaka daga ’ya’yansa, wadanda su ne “zababbu” daga Zuriyyar Annabi Ibrahim (AS). Kadan daga cikinsu sun hada da:

 

b).   Ayar Wilaya: Wadda ke cewa:

 

Masu jibintar al’amarinku kawai su ne Allah da ManzonSa da kuma wadanda suka ba da gaskiya, wadanda suke tsai da Sallah kuma suke bayar da zakka (ta sadaka) a lokacin da suke cikin ruku’u. Duk wanda ya mika wilayarsa ga Allah da ManzonSa da wadannan da suka bada gaskiya, hakika rundunar Allah su ne masu galaba.  al-Ma’ida: 55-56).

 

Duba saukarta a kan Imam Ali (AS) a cikin:

 

i).       Fakharuddin al-Razi (wanda ya rasu a shekara ta 604), Tafsir al-Kabir (wanda ya rasu a shekar ta 604), juz’i na 12, shafi na 26 bugun Beirut; ya fitar da hadisin Abu Zarri, wanda ya ce: “Na taba yin sallar Azahar tare da Manzon Allah (SAWA) wata rana, sai wani mabaraci ya yi bara a masallacin, babu wanda ya ba shi komai. Sai (mabaracin) ya daga hannunsa sama ya yi addu’a da cewa: [Ya Allah Ka yi shaida na yi bara a Masallacin Manzo (SAWA) amma ba wanda ya ba ni komai]. A lokacin Ali (AS) yana cikin ruku’u, sai ya mika masa karamin dan yatsansa na hannun dama wanda ke sanye da zobe, sai mabaracin ya zo ya cire zoben a gaban idon Annabi (SAWA), sai ya ce:

 

Ya Allah Musa ya roke ka da cewa: “Allah Ka yalwata min kirjina” har zuwa “Ka shigar da shi cikin lamarina”[2]; sai Ka saukar da AlKur’ani mai cewa: “(Sai Allah) Ya ce: ‘za Mu karfafa dantsenka da dan’uwanka, kuma Mu sanya muku nasara…’”[3]. Ya Allah ni Muhammadu ne AnnabinKa kuma abin zabinKa, Ka yalwata min kirjina, ka saukaka min lamarina, kuma ka zaba min mataimaki, Ali daga ’yan-gidana, Ka karfafa bayana da shi.

 

Sai Abu Zarri ya ci gaba da cewa: “Wallahi Manzon Allah (SAWA) bai gama wannan kalma ba har sai da Jibrilu ya sauko da cewa: [Ya Muhammad! Karanta:

 

ii).      Zamkhashari (wanda ya rasu ashekara ta 528), cikin tafsirinsa al-Kasshaf, juz’I 1 na shafi na 347, bugun Darul-Arabi dake Beirut.

 

iii).    Suyuti, (wanda ya rasu a shekara ta 911), a cikin Durrul-Manthur Fit-Tafsiri bil-Ma’thur, juz’i na 3, shafi na 104-106. Ya maimaita shi al-Hawi lil-Fatawi, juz’i na 1, shafi na 119, bugun Beirut.

 

iv).    Ibin Kathir (wanda ya rasu a shekara ta 774), a cikin Tafsirul-Qur’anil-Azeem, juz’i na 2, shafi 74, bugun Darul-Ma’arifa dake Beirut.

 

v).     Al-Tabari (wanda ya rashu a shekara ta 310), a cikin Jami’ul-Bayan An Ta’awil Aayil-Qur’an, juz’i na 13, shafi na 108, bugun Halab. Ya fitar da hadisin Galib bin Ubaidulla da ya ce: “Na ji Mujahid yana fadar saukar wannan aya a kan Ali bin Talib da ya yi sadaka yana cikin ruku’u.

 

vi).    Hakim al-Haskani (ya rayu a karnin Hijra na biyar),  a cikin Shawahidul-Tanzil, juz’i na 1, shafi na 161 bugun Manshurat al-A’alami, dake Beirut.

 

vii).  Al-Baidhawi, cikin Tawali’ul-Anwar, juz’i na 1, shafi na 586, bugun Misra. Ya maimaita shi a cikin Anwarul-Tanzeel, juz’i na 2, shafi na 156, bugun Turkiyya.

 

viii). Ibin Hibban, a cikin al-Baharul-Muhit, juzu’I na 4, shafi na 301, bugun Beirut.

 

ix).     Shaukani, cikin Fatahul-Kadir, juz’i na 2, shafi na 78, bugun Beirut.

 

x).      Bukhari, cikin Fatahul-Bayan, juz’i na 3, shafi na 453, bugun Beirut.

 

 

 

c).   Ayar Isar Da Sako: Ita ce ayar da ke cewa:

 

  Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, idan ba ka aikata (haka) ba, to ba ka isar da (sauran) sakonSa ba, kuma Allah Zai kare ka daga mutane.... al-Ma'ida, 5:57.

 

Daukacin malaman Shi’a ba sa tantama a kan saukar wannan aya a kan nadin Ali (AS) a ranar Ghadir. Kuma sun dace a kan cewa Manzo (SAWA) ya aiwatar da tanajin ayar na nadin Ali (AS) a matsayin Amirul-Mu’minin. Wasu daga malaman Ahlussunna ma sun dace da wannan fahimta ta Shi’a, irin su:

 

1.      Hafiz Abu Na'im, a cikin Nuzulul-Qur'ani, shafi na 86.

 

2.      Imam al-Wahidi, a cikin Asbabun-Nuzul, shafi na 135.

 

3.     Hakim Haskani, a cikin Shawahidut-Tanzil Li Qawa'idit-Tafdhil, juzu'i na 1, shafi na 249-258.

 

4.      Jalaluddini Suyuti, a cikin Durrul-Manthur Fi Tafsir Bil-Ma'athur, juzu'i na 2, shafi na 29.

 

5.      Imam Fakharuddin al-Razi, a cikin Tafsirul-Kabir, juzu'i na 12, shafi na 50.

 

6.      Muhammad Rashid Ridha, a cikin Tafsirul-Manar, juzu'i na 6, shafi na 463.

 

7.      Shaukani, a cikin Fatahul-Qadir, juzu'i na 2, shafi na 60.

 

8.      Kanduzi, cikin Yanabi'ul-Mawadda, shafi na 119.

 

9.      Badaruddin, cikin Umdatul-Qari Fi Sharhi Sahihil-Bukhari, juzu'i na 18, shafi na 206.

 

10.  Alusi, cikin Ruhul-Ma'ani, juzu'i na 6, shafi na 193.

 

11.  Sayyid Siddik Hassan Khan, a cikin Fatahul-Bayan Fi Maqasidul-Qur'an, juzu'i na 3, shafi na 63.[4]

 

 

 

d).  Ayar Cikan Addini: Wadda ke cewa:

 

A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika ni'imaTa a kan ku, Na kuma yardar muku Musulunci a matsayin addini.  Surar Ma'ida, 5:3.

 

Wannan ita ke bayyana aiwatar da horon ayar da ambatonta ya gabata, wadda take horo da nadin Imam Ali (AS), da cewa da Imamancin Ali (AS) Allah Ya cika addini. Biyu ba sa sabani a kan haka a Shi’a; haka mun yi bayanin malaman Ahlussunna da suka dace da Shi’a a kan haka a amsar tambaya ta daya sai a koma a duba.

 

e).   Ayar Hassada: Wadda take bayanin irin abubuwan da wasu suka binne a cikin zukatansu na yi wa wannan gadajjen matsayi hassada. Wannan aya ita ce:

 

A’a, suna dai yi wa mutanen hassada ne kan abin da Allah Ya ba su daga falalarSa. To hakika Mun bai wa Iyalan Ibrahim Littafi (sako)_da Hikima (zurfin ilimi), kuma Muka ba su mulki mai girma (Imamanci). Al-Nisa’i: 54.

 

Wani abin sha’awa shi ne cewa wasu daga malaman Ahlussunna sun dace da malaman Shi’a a kan saukar wannan aya a kan Ahlul-Baiti (AS). Misali Ibin Hajar al-Haitami ya fitar da haka a cikin littafinsa al-Sawa’ikul-Muhrika, shafi na 233, a wajen ambaton aya ta shida daga ayoyin darajojin Ahlul-baiti (AS); har ma ya fitar da Hadisin Imam al-Bakir (AS) da ke cewa: “Wallahi mu ne Mutanen a wannan aya”.

 

Mun gode wa Allah a kan wannan ni’ima ta matse masu zagin mu su fadi abin da suke zagin mu a kan aiki da shi.

 

 

 

f).    Ayar Shiriya da Shiriyarsu: wadda ke cewa:

 

Lallai Ni mai gafara ne ga wanda ya tuba ya yi imani kuma ya yi aikin kirki sannan ya shiriya. Taha:82

 

“Shiriya” a nan shi ne Wilayar Ahlul-baiti (AS), kamar yadda Ibin Hajar ya fitar a bayanin aya ta takwas ta darajojin Ahlul-bait (AS) a cikin al-Sawa’ik dinsa, shafi na 235; ya ce: “ya tabbata daga al-Banani cewa Ya shiriya zuwa wilayar Ahlul-baiti (AS).”

 

Jero dukkan ayoyin da suka yi Magana a kan Imamancin Ahlul-bait (AS) da zantukan malamai a kanau ba zai yiwu mana a dan wannan sassarfar ba. Mun takaita da wadannan sai a wani jikon.

 

 

 

Imamanci a Hadisai

 

5) Amma tambayar cewa me ya sa Annabi (SAWA) bai fadi irin abin da ya fada a kan banu Talha ba, wannan na nuna rashin natsuwarsa da rashin fahimtar lagon maganganun Manzo (SAWA). Yanzu shi dakikin ina ne da har ya kasa fahimtar cewa kowace magana tana da mahallinta. Shin banu Talha Ahlul-bait ne? ko kuwa makullan Ka’aba Imamanci ne? Menene fuskar wannan sukurkutaccen kiyasi? Wancan wani abu ne alhali wannan wani ne dabam, to don me kuma magana a kansu za ta zo da siga daya? Hala banu Talha Khalifofi ne a gunsa?

 

To Manzo (SAWA) ya yi maganganu da yawa kan Imamanci tare da tsawatar da mutane a kan kaucewa tafarkinsa, daga cikin maganganunsa akwai:

 

a).   A lokacin da Manzo (SAWA) ya dawo daga Hajin ban-kwana, ya kuma yi zango a Ghadir Khum, ya sa an tanaji yanayin day a dace, kuma ya yi lacca da cewa:

 

Kamar an kira ni na amsa (wato kusatowar rasuwarsa kenan). Lallai ni mai barin nauyaye biyu ne a cikin ku, dayan su ya fi daya girma: (su ne) Littafin Allah da kebabbun Mutan-Gidana; ku lura da yadda za ku yi mu’amala da su a baya na, domin su biyun ba za su taba rabuwa ba har su same ni a bakin tafki.

 

Sannan sai ya ce:

 

Lallai Allah Madaukaki Shi ne majibincina, kuma ni ne majibincin kowane mumini.

 

Sannan sai ya kama hannun Ali ya ce:

 

Wanda na zama majibicnisa to wannan majibincin (al’amarin) shi ne. Ya Allah Ka jibinci (al’amarin) wanda ya jibince shi, Ka kuma ki wanda ya ki shi…. (Hadisin na da tsawo).[5]

 

b).   Fadar Manzon Allah (SAWA) cewa:

 

Ku saurara! Lallai misalign ’Yan-Gidana (Ahlul-bait dina) a cikin ku kamar jirgin ruwan Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira; wanda kuwa ya ba shi ya nutse.[6]

 

c).   Ga shi kuma ya na cewa:

 

Taurari aminci ne ga wadanda ke kasa daga makuwa haka kebabbun ’Yan-Gidana aminci ne ga al’ummata daga sabani (a addini). Idan kuwa wata kabila (wato wasu jama’a) daga Larabawa (ko wasun su) suka saba musu, to za su sassaba su zama kungiyar ibilis.[7]

 

Ibin Hajar, daga Ahlussunna, ya bayyana fuskar wannan kwatanci da cewa:

 

Fuskar kwatanta su da jirgin ruwa shi ne cewa wanda ya so su kuma ya girmama su a matsayin godewa ni’imar Allah da Ya daukaka su, sannan kuma ya yi riko da shiriyar malamansu, to wannan ya tsira daga duhun ka-ce-na-ce. Wanda kuwa ya sabawa hakan, wannan ya halaka cikin kogin kafirce wa ni’ima; kuma ya halaka cikin dimuwar kangara da taurin-kai.[8]

 

Har zuwa inda ya ce:

 

Fuskar kwatanta su da kofar tuba kuwa ahi ne cewa Allah Madaukaki Ya sanya shiga wannan kofa, wadda ita ce kofarAriha’I ko Baitul-Mukaddasi, tare da kaskantar da kai da istigfari, ya zama sababin gafara. Sai Ya sanya kaunar Ahlul-bait ta zama sababin haka.[9]

 

d).   Wani hadisi da yake kara tabbatar wa da duk mai gaskiya Imamancinsu shi ne hadisin da Tabrani ya fitar a cikin al-Kabir, da isnadin da ya dangane da Ibin Abbas, ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya ce:

 

Wanda zai yi masa dadi ya rayu irin rayuwata, ya kuma mutu irin mutuwata, ya kuma shiga Aljannar da Ubangijina Ya dasa ta, to ya mika wa Ali wilaya a baya na, kuma ya so wanda ya mika masa wilaya, ya kuma yi koyi da Ahlul-bait dina a baya na; domin su kebabbun Iyalina ne; an halicce su daga turbayata; kuma an azurta su da fahimtata da ilimina. To bone ya tabbata ga masu karyata darajojinsu daga al'ummata, wadanda suke yanke zumuncina a kansu; kar Allah Ya sada su da cetona.[10]

 

Matir ya fitar da irinsa, haka ma al-Barudi, da Ibin Jarir, da Ibin Shahin, da Ibin Mundah, ta hanyar Ishak, daga Ziyad bin Matraf, ya ce: Na ji Manzon Allah (SAWA) yana cewa:

 

Wanda ya so ya rayu irin rayuwata ya kuma mutu irin mutuwata, ya kuma shiga Aljannar nan da Ubangijina Ya yi min alkawari, wadda it ace Aljanar dauwama, to ya mika wa Ali da zuriyyarsa wilaya a baya na; domin su ba za su taba fitar da ku daga shiriya ba kuma ba za su taba shigar da ku kofar bata ba.[11]

 

e).   Wata ruwayar ta kara fitowa da Imamancinsu fili ga mai idon basira, inda Annabi (SAWA) ke cewa:

 

A kowane zango na al'ummata akwai daidaitattu daga kebabbun 'yan-gidana, zasu rika korewa addini karkace karkacen batattu da cushe cushen mabarnata da tawilin jahilai. Ku saurara! Lallai Imamanku sune masu kai ku zuwa ga Allah, don haka ku lura a bayan wa za ku taru.[12]

 

f).    A Wani wajen an ruwaito Manzo (SAWA) yana cewa:

 

Ku sanya Ahlul bait dina a wajen ku a matsayin kai a dangane da jiki, da matsayin ido dangane da kai; kai ba ya shiriya kuwa ba tare da ido ba.[13]

 

Wadannan kadan ne daga abin da ya zo na ruwayoyin da suka tabbatar da Imamancin Ahlul-bait (AS) ta hanyoyin Ahlussunna. Na takaita da na su –ba tare da na kawo na ’yan Shi’a ko daya ba- don hujja ta fi cika. Da na ambaci na mu da an ga abin da karin armashi. Ko ta halin kaka dai, ya rage ga mutum kuma, ko ya koma ya yi riko da tawile tawilen ’yan tawili ko karyatawar masu karyatawa –irin su Ibin Taimiyya- ko ya kama gaskiya ya san tsira. Mu kam mun yi gaba; mun ji mun yarda, kuma mun yi biyayya Allah Ya amince mana.

 

6-Tambayar ko me yasa Manzo bai hori Ali da ya ja mutane Sallah ko sau daya ba kuwa yana nuna raunin dalili ne. Da farko idan ma muka tafi a kan ’yar masaniyar da ya ginu a kanta, sai mu tambaye shi shin horon wani ya ja Sallah a lokacin lalurar Manzo (SAWA) yana daya daga nassosin Imamanci/Khalifanci ne a gun Wahabiyawa? Idan haka ne to ga wasu abubuwa kamar haka:

 

a).   Ba Abubuakar ya kamata ya zama Khalifa na daya (a bisa tsarinsu) ba kenan, Ibin Ummu Makatoom ya kama ta ya zama Khalifa na daya, don Annabi (SAWA) ya hore shi da ya ja mutane Sallah kafin ya hori Abubakar da ittifakin kowa.

 

b).   Ba a ruwaito Annabi ya taba horon Umar da Usman da su ja mutane Sallah ba; kai! ba’a ruwaito cewa Abubakar yace Umar ya ja mutane Sallah ba a lokacin Khalifancinsa ba; haka nan ba inda akace Umar ya taba nada daya daga cikin mutane shidan kwamitinsa da ya ja mutane Sallah; kai sai ga shi ma yana nada Suhaib al-Rumi da ya yi wa mutane sallah na kwana ukun da ya yi yana jinya, a daidai lokacin da wancan kwamiti ke shagalce da zaben magajinsa. Kenan ashe Khalifancinsu ba karbabbe ba ne a bisa wannan ka’ida.

 

c).   Ba inda aka ce Annabi (SAWA) ya ta’allaka limancin wani da Khalifanci.

 

d).   Su da kansu (Abubakar da Umar din) basu kafa hujja da haka a matsayin abin da ya sa Abubakar ya cancanci zama Khalifa ba a lokacin da Ansar suka yi tutsu a kan kudurinsu a Sakifa. Babu wannan bayani a cikin hudubar Abubakar, babu a zancen Umar; alhali kuwa sun fi kowa bukatar irin wadannan dalilai a lokacin. Wanda hakan ke nuna kafa hujja da limancin Abubakar a matsayin dalilin Imamanci ko Khalifanci wani bakon abu ne da su Sahabban ma ba su san shi ba.

 

Sannan ka’idar Ahlussunna ta limanci ta yi hannun riga da wannan ra’ayi; domin kuwa su sun halatta (kai! sun ma wajabta) bin kowane irin liman Sallah; mumini ko fasiki, mutumin kirki ko fajiri; wannan shi ne abin da ya tabbata a riwayoyinsu da suke ingantawa, haka shi ne abin da fakihansu suka tabbatar a fatatwowinsu.

 

Kara da cewa kissar limancin Abubakar a lokacin rashin lafiyar Annabi (SAWA) ba ta zama amintacciya ko ta hali kaka ba. Kai! masu bin diddigi da tahkiki daga bangarorin biyu sun karyata ta gaba daya, saboda yadda ta kunshi karyata-kai a cikinta. Muna fatan wani lokaci mu yi nazarin haka a makaranta.

 

A karshe ta bayyana cewa kafa hujja da limancin wani a matsayin dalilin Imamanci da Khalifanci tsagwaron rashin dalili ne da jin raunin matsayi.

 

Abin mamaki kuma shi ne a lokacin da Mansur ke neman da mu kawo masa hujjoji daga AlKur’ani da Hadisai a kan Imamancin tsarkakan ’Yan-Gidan Manzo (SAWA), sai ga shi yana son tabbatar da Khalifancin wasunsu daga wajen AlKur’ani da Hadisai.

 

 

 

Amsoshin tambayarsa

 

1.      Ta bayyana karara cewa AlKur’ani ya bayyana wannan rukuni kamar sauran rukunna babu wani bambanci. Jahilcinsa ga zantukan AlKur’ani a kan haka kuwa ba dalili ba ne a kan cewa AlKur’ani bai tattauna su ba. Idan shi ya zabar wa kansa wasu tawile tawile, waninsa ma yana da ’yancin ya zabi nasa fassarar, masamman bisa dogaro da Hadisan da suka inganta a gunsa.

 

2.      Ali (AS) Imami ne, wanda aka tanaje shi don kare addini, don haka bai taba barin wannan aiki nasa ba. Kuma rashin mulki bai sauke shi daga matsayinsa na Imami ba. Shigarsa cikin kwamitin Umar (da kowane irin kwamiti ma) don sauke nauyinsa ne na Imami, kuma hakan ya taimaka.

 

3.      Idan Mansur bai sani ba, ya sani cewa ba al’umma ce ta zabi Usman ba, Abdul-Rahman bin Auf ne ya nada shi yayin da ya karbi sharuddan da Umar ya gindaya na yin aiki da AlKur’ani da Sunnar Manzo da tsarin Abubakar da Umar; kuma kafin Abdul-Rahman ya kai gare shi sai da ya tuntubi Imam Ali (AS) da wandannan sharudda amma Imam ya ki yarda da sharadin karshe na bin tsarin Abubakar da Umar. Ina yi masa nasiha da ya koma ya karanta tarihi da kyau daga amintattun littafan Ahlusunna na tarihi irin su Tabari da Ibin Athir da Ibin Hisham don ya daina ruda jahilan masu sauraronsa.

 

4.      Annabi ne ke da zabin yadda zai fadi sakonsa, ba Ibin Taimiyya ko Ibin Abdul-Wahab ko karan-kada-miya Mansur ne za su koya masa ba. Kuma Annabi ya yi bayanai da yawa a kan haka.

 

5.      Saboda horo da jan Sallah ba shi da alaka da shugabancin addini da duniya kamar yadda duk bangarorin suka dace. Da suna da alaka da ya yi hakan, kuma da Abubakar da Umar ma sun yi haka, kuma da munga shugabannin Wahabiyawa na yin irin haka a kasashensu.

 

 

 

Na mu Tambayoyin

 

 

 

1.      Sanin kowa ne cewa rukunin addinin Wahabiyanci shi ne cewa duk Musulmin da ya fahimci akida sabanin yadda kuntataccen tunaninku ya fahimta Mushriki ne, arne ne don haka jininsa da dukiyarsa halal ne, shin me yasa wannan rukunin babba na akidarku ba a ambace shi cikin AlKur’ani ba? Yaya shi AlKur’ani bai kasa Mushirikai zuwa masu sallah da marasa sallah ba, ta yadda har zai bayyana cewa masu salla ma sun fi hadari a kan wadancan da ba sa sallah, kamar yadda Ibin Abdul-Wahab ya yi ta nanatawa ba? Gashi kuwa Allah (SWT) Ya fayyace abubuwa daki-daki, tun daga Sallah, tsarki har farauta.

 

2.      Mu da Ahlussunna mun dace a kan cewa haddin kalmar shahada shi ke barin mutum a Musulunci, muna kafa hujja da hadisan da ke bayanin shika shikan Musulunci biyar dake farkon babobin littafanmu na hadaisai irinsu al-Kafi da Bukhari, da irin hadisin Zaidu da Manzon (SAWA) ya yi bara’a ga wanda ya kashe Musulmin dake furta Kalmar Shahada; alhali ku a gun ku wannan ba uzuri ba ne. Tambayar it ace: me ya sa Hadisai ba su fito dalla dalla sun bayyana irin ra’ayinku ba? Yaya aka yi aka sami wannan munnan karo tsakanin tanaje-tanajen Musulunci da tanaje-tanajen addininku ga shi kuwa kun fi kowa kuri da tutiya da Musulunci da “Ahlussunna”?

 

3.      A yau muna ganin Sarakuna a manyan kasashen Wahabiyawa dake daure muku gindi ba su ne limamai ba; shin wannan ya dace da karantarwar addininku? Ina kuma ka’idar taku ta “Khalifana Limamina kuma Limamina Khalifana”? Shin su ne suka saba wa ka’idar ko ku ne ba ku fahimci addinin na ku ba tukuna?

 

Ibin Taimiyya ya tuhumci Imam Ali (AS) da kwadayin mulki cikin Minhajul-Sunna, haka ya tuhumci Fadima da kwadayi saboda ya nemi hakkinta da AlKur’ani ya bayyana a ayar gado, kai kuma Mansur a yau kana son nuna mana sabanin haka, shin wa za mu saurara ne? Menene ainihin sakon Wahabiyanci kan Imam Ali (AS) da sauran tsarkakan Ahlul-baiti ne? Ko kuma kuna yin takiyyar ne?

 


 

 


 

[1] Duba Tarihin Tabari, juz’i na 3, shafi na

 

[2] Surar Taaha: 25-32.

 

[3]Surar Qasasi: 35.

 

[4]Wadannan kadan kenan daga cikin daruruwan malaman Ahlussunna da suka fitar da saukar Ayar Isar da Sako. A kan haka Allama al-Amini ya fitar da tarinsu a cikin littafin da ya kebe don tabbatar da al'amarin Ghadir ta hanyoyin Ahlussunna. Sunan wannan littafi al-Ghadir Fil-Kitab Wal-Sunnati Wal-Adab. Ya kunshi juzu'o'i 20. Mai so na iya komawa can ya duba.

 

[5]Hakim ya fitar da shi daga Zaid bin Arkam a wani hadisi marfu'i, a shafi na 109, juz'i na 3 cikin littafinsa al-Mustadrak, sannan sai ya ce: “Wannan hadisi ne Sahihi a bias sharadin Shehunan nan biyu (Bukhari da Muslim), amma basu fitar da shi dukkansa ba”. Haka nan ya fitar da shi ta wata hanyar a shafi na 533, uz'i na , cikin al-Mustadrak din dai, har ma a nan ya sake cewa: “Wannan hadisi ne mai ingantaccen isnadi, amma (Bukhari da Muslim) bas u fitar da shi ba”. A nan nake cewa: Zahabi ma ya kawo shi a cikin littafinsa al-Talkhis, yana mai ikirari da ingancinsa.

 

[6]Hakim al-Naishaburi ya fitar da shi a cikin Mustadrak al-Sahihain, juz'i na 3, shafi na 151, da isnadin day a kare da Abu Zarri (RA).

 

[7]Hakim al-Naishaburi, Mustadrak al-Sahihain, juz'i na 3, shafi na 149, daga Ibin Abbas. Sannan Hakim ya ce: “Hadisi ne mai ingantaccen isnadi (amma) kuma (Bukari da Muslim) bas u fitar da shi ba.

 

[8] Ibin Hajar al-Haithami, Sawa’iq al-Muhriqah,shafi na 91, babi na 11, wajen tafsirin aya ta bakwai daga jerin ayoyin da jero a kan darajojin Ahlul-bait (AS).

 

[9] Duba zancensa sannan ka gaya min mai ya sa bai yi riko da shiriyar Imamai daga cikinsu a komai na furu’a da akidarsa ba; Ko wane abu daga usulul-fikihi  da ka’idojinsa ba, ko wani abu na ilumman Sunna da AlKur’ani ba, ko wani abu daga tarbiyya da gyaran ruhi ba? Me yasa ya saba musu ya je ya nutsar da kansa a cikin kogin kafircewa ni’ima, ya halaka a cikin dimuwar kangarewa da taurin-kai? Allah Ya yafe masa kan munana mana da ya yi, da irin kage kagen da ya yi mana!!

 

[10]Wannan hadisi da lafazinsa shi ne hadisi na 3819 daga hadisan Knazul-Ummal, a karshen shafi na 217, juz'i na 6. Haka nan an fitar da shi a littafin Muntakhabul-Kanz, sai a duba shi a farkon hamishin Masnad Ahmad, juz'i na 5, shafi na 94. banbancin kawai shi ne a nan y ace: "An azurta su da fahimtata.." ba tare da ya ambaci "…da ilimina.." ba. Wata kila kuskuren mai rubutawa ne. Abu Na'im ya fitar da shi a cikin Hilyatul-Aulya'i, kamar yadda Ibin Abil-Hadid ya bayyana a sharhin Nahjul-Balaghah, juz'i na 2, shafi na 450, bugun Misra. Haka nan Ahmad bin Hambali ya fitar da shi a cikin Masnad dinsa, a littafin Mannqibu Ali bin Abi Talib.

 

[11] Wannan shi ne hadisi na 2578 daga hadisan Kanzul-Ummal, juz'i na 6, shafi na 155. Haka nan an fitar da shi a Muntakhabul-Kanz, dake hamishin Masnad na Ahmad, juz'i na 5, a sadarar karshe na shafi na 22. Ibin Hajar al-Askalani ma ya kawo shi a takice a yayin da yake bayar da labarin Ziyad bin Matraf, a sashin farko na littafinsa al-Isabatu Fi Tamyiz al-Sahabati, sannan sai y ace: "Ina cewa: a cikin Isnadinsa akwai Yahay bin Ya'ala al-Muhari; shi kuwa abin gudu ne". Ni kuma ina cewa: wannan abin mamaki ne daga irin al-Askalani! Domin Yahaya bin Ya'ala amintacce ne bias ittifaki. Hakika Bukhari ya fitar da hadisinsa kan Umrar Hudaibiyya, a cikin Sahih dinsa. Haka nan Muslim ya fitar da hadisinsa a kan haddodi, shi ma a cikin Sahih dinsa. Zahabi, a cikin Mizanul-I'itidal ya sanya amincinsa cikin abubuwan dab a mai shakka a kai. Imam al-Kaisarani kuwa ya sanya shi ne cikin jerin wadanda Bukhari da Muslim ke kafa hujja da su.

 

[12]Mulla ya fitar da shi a cikin tarihinsa; kamar yadda ya zo a wajen tafisirin: "Ku tsayar da su lallai su wadanda za a tambaya ne" a shafi na 90 da littafin Sawa'ikul-Muhrikah, na Ibin Hajar.

 

[13]Wasu daga cikin masu Sunan sun fitar da shi da isnadi marfu'I day a kare da Abu Zarri. Haka Imam al-Saban ya fitar da shi a wajen ambaton darajojin Ahlul-bait a cikin littafinsa Is'afur-Ragibin. Haka nan Sheikh Nabhani ma ya fitar da shi a cikin littafin al-Sharful-Mu'abbad, shafi na 31; da wasu amintattun. Wannan nassi ne a kan wajibcin shugabacinsu da cewa shiriya zuwa ga gaskiya baya kasancewa sau ta hanyarsu.

 

 

 

Last modified on

38 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel