RAAF Official Website

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi Saba'in Zuwa Ga 'Yan Shi'a (3)

Rate this item
(0 votes)

AMSOSHIN TAMBAYOYI SABA'IN ZUWA GA 'YAN SHI'A -3-
Daga
Saleh Muhammad Sani Zaria
P.O. Box 4167 - Kano
E-Mail: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
6/7/2007

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

 TAMBAYA DA AMSA TA 7-12

A cigaba da amsa tambayoyi saba’in da Mansur Ibrahim Bawahabiye ya yi zuwa ga ’yan Shi’a, a wannan karon zan dora daga inda na tsaya, wato daga tambaya ta takwas; a wannan karon zan kai har zuwa tambaya ta goma sha biyu in Allah Ya yarda.

 

Asasan da aka gina tambayoyin a kai:

 

Wadannan tambayoyi biyar sun ginu ne a kan wasu tunane tunane da Mansur ya dora kansa a kansu, wadanda suka hada da yarda da cewa:

 

1)    Rashin yaki da Ali (AS) ya yi na kwato hakkin da ’yan Shi’a ke da’awa gare shi ya yi karo da abin da ya zo a cikin littafansu na bayyana saukar da Imamancin Ali daga Allah (SWT) da cewa Shi (Allah din ne) Ya kira shi da Amirul-Muminin; in kuwa ba haka ba, to ya yi karo da da’awar jaruntaka da ake masa.

 

2)    A cikin Nahjul-Balagha (wanda ke madogara daga littafan Shi’a) a shafi na 136 an fadi cewa Ali (AS) ya roki a yafe masa shugabancin bayan kashe Usman saboda ganin irin masifar da ake ciki, na wasu ’yan tsiraru da suka zo daga Kufa, kuma suka kashe sarkin Musulmi –bayan ya hana a yake su. Sai Ali ya ce: “Ku bar ni ku je ku nemi wani ba ni ba.”

 

3)    Zancen Ali (AS) lokacin da aka taya masa Khalifanci bayan kashe Usman, yayin da ya ce: “Ku bar ni ku je ku nemi wani ba ni ba.” Ya karyata akidar wasici da shi.

 

4)    ’Yan Shi’a sun yarda da cewa Addini ba ya kammala sai da imani da wasici da Ali (AS).

 

5)    Mutane da yawa suna zuwa suna shiga Musulunci daga wasu garuruwa, wadanda haduwarsu da Manzo (SAWA) ta karanta; kuma ba su da labarin wasicin da ’yan Shi’a ke da’awar anyi ga Ali (AS).

 

6)    Imam Khumaini (RA) a cikin littafinsa Kashful-Asrar yana ganin Annabi (SAWA) bai isar da sakon Allah game da Imamancin Ali kamar yadda ya isar da Sakon Allah game da Manzancinsa ba.

 

7)    Cewa Ali (AS) ya karbi mukamin gwamna a lokuta dabam daban a lokacin Khalifancin Umar (RA); kamar lokacin da ya tafi Baitil-Mukaddasi bayan bude ta da yaki, inda ya nada Ali a matsayin gwamnan Madina; haka ya karbi mukamin alkalanci a karkashin Umar din dai, wanda hakan ya karyata akidar ’yan Shi’a na yarda rashin yardarm Ali (AS) da Khalifancin Umar (RA).

 

8)    ’Yan Shi’a na daukar gwamnatin Umar (RA) a matsayin kafirar gwamnati.

 

9)    ’Yan Shi’a na ganin Ali (AS) na daukar Usman kafiri ne wanda ya kwace masa mulki.

 

10)Ali (AS) ya tura ’ya’yansa Hassan da Hussaini (AS) da su tafi su kare Usman a lokacin da aka kewaye gidansa, wannan na nuna yardarsa da Usman, sabanin yadda ’yan Shi’a ke gani.

 

 

 

Nassin Tambayoyin

 

7)    Me yasa Ali bin Abi Talib (AS) bai taba hawa mumbarin Manzon Allah (SAWA) ya tunatar da jama’a nadin da Manzo (SAWA) ya yi masa kuma ya nemi jama’a da su kauce wa wadannan azzalumai –a ganin ’yan Shi’a- ba? Ina jarumtar tasa a yayin da bai yaki wadanda suka kwace hakkin da Allah Ya dora masa ba?

 

8)    Me yasa Ali bin Abi Talib ya ki karban wannan hakkin da Allah Ya saukar masa daga sama? Shin ya jin tsoro ne? Wa yake tsoro bayan Allah?

 

9)    Shin Musuluncin irin wadancan da ba su san wasici da Ali ba kammalallen Musulunci ne ko a’a? Ko kuwa an yi musu rangwame ne? Idan haka ne me yasa Manzo (SAWA) bai cika musu ba? Idan kuwa kammallale ne ina amfanin fadar cewa addini ba ya cika sai da Imamancin Ali? Ko kuwa kun yarda da irin akidar Khumaini ne na cewa Manzo bai isar da sako kan Imamancin Ali kamar yadda ya isar kan Annabcinsa ba?

 

10)Me yasa Ali ya karbi mukamin zama gwamna ba sau daya ba a lokacin Umar (RA)? Me yasa bai fadi cewa matsayinsa ba ne?

 

11)Me yasa Ali (AS) ya karbi mukamin alkalanci a karkashin gwamnatin Umar (RA)?

 

12)Me yasa Ali (AS) ya tura ’ya’yansa Hassan da Hussaini (AS) don kare Usman a lokacin da mutane suka kewaye gidansa za su kashe shi? Me yasa ba zai bari ayi masa juyin mulki ba don ya karbi mulkinsa kamar yadda aka kwace masa?

 

 

 

 

 

AMSAR TAMBAYA TA  7-12

 

 

 

Game da asasan da ya gina wadannan tambayoyin nake ce masa:

 

 

 

Zantukan Imam Ali (AS) Kan Hakkin Ahlul-Bait (AS)

 

1-Ya so nuna cewa Imam Ali (AS) bai taba tunatarwa kan hakkinsa ba. To a nan ma ya nuna jahilcinsa, don kuwa zantukan Imam (AS) a kan haka suna da yawa. Kai har ma abin da shi (Mansur) da irinsa zai iya dauka a matsayin “suka” ko “zargi” ga wadanda yake ganin sun karbi abin da hakkinsa ne. Idan yana son sanin irin wadannan zantuka ya koma ya duba Nahjul-Balagha (wadda muka ga yar yana kafa hujja da shi) don jin hudubarsa ta Shaqshaqiyya don jin haka. A cikin ta yana cewa:

 

Amma wallahi dan Abu Kuhafata ya kakabawa kansa rigar (Khalifanci) alhali ya kwana da sanin matsayina a kan haka kamar marikin dutsen nika (irin na wancan zamanin) ne; wanda abin zubowa[1] ke kwararowa daga gare ni alhali tsunstu ba ya iya kai wa kololuwar inda nake; sai na kau da kai daga gare shi (Khalifanci); sai na shiga tunanin ko dai in kutsa yaki da takaitaccen tanaji ko kuma in yi hakuri a mummunan yanayi irin wanda babba ke tsufa a ciknsa yaro kuma yake furfura, mumini kuma ke tsananin wahala har lokacin haduwa da Ubangijinsa. Sai na ga hakuri a kan haka shi yafi dacewa da hankali; sai na yi hakuri alhali ido na cike da kwalla kuma wani abu ya yi karan-tsaye a makogoro ina ganin gadona a kwace. Har zuwa lokacin da na farko ya tafi makomarsa sai ya mika akalar lamarin ga wane a bayansa.[2]

 

Har zuwa inda ya ce:

 

Abin mamaki! A lokacin da ya yi ta neman a raba shi da shi (Khalifancin) a lokacin da yake raye sai ga shi yana mika akalar abin ga wani a bayansa! Lallai sun tsananta wajen kasafta shi (Khalifancin) a tsakaninsu!! Sai ya sanya shi (Khalifancin) a wani mawuyacin ma’ajiya, wanda rauninsa ke da tsanani kuma shafansa ke da kaushi kuma tuntube da neman uzuri suka yawaita a cikinsa; ma’abucinsa kamar mahayin (dabba) mai tutsu ne, idan ya dame linzaminsa yana iya tsinkewa, idan kuma ya sake shi yana iya jefa shi a mahalaka. Sai aka jarabci mutane –abin gunin tausayi- da shiga halin rudu da rashin sanin madafa da sassauya matsayi da tangal-tangal. Sai na hakura da tsawaitan lokaci da tsananin masifa har zuwa lokacin da (na biyun) ya wuce (ya mutu), sai ya sa shi (Khalifancin) a hannun wasu mutane da ya yi da'awar wai ni daya ne daga cikinsu. Wayyo Allah da Shura! Yaushe aka fara shakka da fifikona a kan na farkonsu har na zama ana kwatanta ni da irin wadancan!! Sai dai ni na sassauto a yayin da suka sassuto kuma na yi sama a yayin da suka yi sama.[3]

 

Irin wannan jin ciwo da bacin rai na Imam na iya bayyana a wani zancen nasa mai cewa:

 

Ina wadanda suke da'awar cewa su ne wadanda suka zurfafa a ilimi koma bayan mu don karyata mu! Saboda Allah Ya daukaka mu alhali Ya kaskanta su! Kuma Ya ba mu, alhali Ya hana su! Ya shigar da mu a lokacin da Ya fitar da su. Da mu ake neman shiriya, kuma ake nemam yayewar makanta. Lallai Imamai daga Kuraishawa suke, an shuka su a wannan gidan na Hashim; (Imamanci) ba ya inganta a kan wasunsu kuma mahukunta ba sa kyautata daga koma bayansu.[4]

 

Imam ya yi kira a lokuta da yawa kan hakkinsa, ya kuma tunatar da wannan wasici na Manzo (SAWA). Daga cikin irin wadannan wurare akwai zancensa mai cewa:

 

Ina kuke zuwa? kuma yaya kuke fandarewa? alhali alamomi na tsaye, kuma ayoyi sun bayyana, kama an kafa hasumiyoyi? Zuwa ina ake ragaita da ku? Kai! yaya kuka gigice alhali ’Yan-Gidan Annabinku na cikin ku? Wadanda su ne akalar gaskiya, kuma (su ne) alamomin addini, kuma harsunan gaskiya; don haka ku ajiye su irin matsayin da kuka ajiye AlKur’ani; kuma ku je gare su irin zuwan mai tsananin kishi. Ya ku mutane! Ku karbe shi (wannan al’amari) daga cikamakon Annabawa SAWA (cewa): “Hakika mai rasuwa daga cikin mu (Ahlul-baiti) yana rasuwa alhali shi ba matacce ba ne; kuma dayan mu na zama kasa (a kabari) amma shi ba kasa ba ne”. Kar ku fadi abin da ba ku sani ba, domin so tari gaskiya na nan a inda kuke jayayya; ku nemi gafaran wanda ba ku da wata hujja a kansa, wanda shi ne ni. Ashe ban yi aiki a cikin ku da Babban Nauyi (AlKur’ani) ba? Kuma gashi nan zan bar muku Karamin Nauyi (Hassan da Hussaini); na kuma kafa muku tutar imani…. Har zuwa karshe.[5]

 

Haka nan (Imam Ali AS) ya fadi cewa:

 

Ku fuskanci ’Yan-Gidan Manzonku, sannan ku lizimci hanyarsu, ku bi inda suka bi; don ba za su fitar da ku daga shiriya ba, kuma ba za su kai ku zuwa bata ba. Ku dakata a inda suka dakata, kuma ku yunkura a inda suka yunkura. Kar ku shiga gabansu don sai ku bata, kuma kar ku yi baya can daga gare su don sai ku halaka”.[6]

 

Haka nan ya taba ambaton su da cewa:

 

Su ne rayuwar ilimi, kuma (su ne) mutuwar jahilci. Hakurinsu na bayyana muku zurfin iliminsu; kuma zahirinsu na nuna muku abin da suka boye; shirunsu na gaya muku zancensu. Ba sa saba wa gaskiya kuma ba sa sabani a cikin ta. Su ne turakun addini, kuma (su ne) madafa; da su gaskiya ta koma ainihin wajenta, kuma bata ya kau daga inda yake. Sun fahimci addini fahimta ta hankalta da ganewa, ba ta ruwaya (kawai) da ji ba; domin masu ruyawar ilimi suna da yawa alhali masu fahimtarsa sun karanta.[7]

 

Haka nan Imam Ali (AS) ya kara da fada a wata hudubar ta sa cewa:

 

’Yan-Gidansa ne mafi alherin ’yan gidaje, kuma Zuriyarsa ce mafi alherin zuriyoyi, kuma bishiyarsa (wato tsatsonsa) ita ce mafi alherin bishiya, wadda ta (tsira kuma ta) girma a haramin Makka, ta kuma yi yabanya na karimci, tana da rassa masu tsawo da ’ya’yan da ba a samu a irin ta a ko’ina.[8]

 

Haka nan ya fada a wani wajen cewa:

 

Mu ne samfuri (na duk alherai), kuma abokan tafiya, kuma masu gadi, kuma kofofi; ba a shiga gidaje kuwa sai ta kofofinsu; wanda ya shige su ta wani waje da ba kofofi ba kuwa, a kan kira shi da barawo…

 

Har zuwa inda ya siffanta ’Yan-Gidan Annabi (SAWA) da cewa:

 

Su ne zabin AlKur’ani; kuma su ne taskirorin Allah; idan suka yi magana suna (fadar) gaskiya; idan kuma suka yi shiru ba a shiga gabansu, da ma kuwa haka ya kamata shugaba ya zama mai gaskiya ga jama’arsa, ya kuma hada hankalinsa waje guda.[9]

 

Da dai sauran nassosi irin wadannan masu yawa da suka fito daga gare shi (AS) a kan wannan al’amari; kamar fadarsa (AS) cewa:

 

Da mu aka shiryar da ku daga cikin duhun (bata), kuma (da mu) kuka daukaka zuwa kololuwa, kuma da haskenmu aka yaye muku bakin duhun da kuke ciki. Mai kunnen-kashi ba ya jin nasiha da wa’azi.[10]

 

Da fadarsa (AS) a wata hudubar cewa:

 

Ya ku mutane, ku haskaka kanku daga hasken fitila mai wa’azi da wa’azantarwa. Ku sha daga  idon ruwa mai tsafta da ya tsarkaka daga duk wani datti da gurbata.[11]

 

Da fadarsa a karshen hudubarsa ta 105, cewa:

 

Mu ne bishiyar Annabci, kuma masaukan sakon Allah, kuma wajen kaiwa-da-komowar Mala’iku, kuma ma’adanonin ilimi, kuma mabubbugar hukunce hukunce. Mai taimakon mu da mai son mu yana sauraron rahamar Ubangiji, makiyin mu da mai fushi da mu kuwa yana sauraron fushin Allah.

 

Da fadarsa cewa:

 

Lallai wanda ya mutu a kan gadonsa daga cikin ku alhali ya san hakkin Ubangijinsa da hakkin manzonSa da (na) ’Yan-Gidansa, to ya mutu a shahidi, kuma ladansa na wajen Allah, ya kuma cancanci ladan duk aikin kirkin da ya yi niyyar yi (na yin shahada tare da Ahlul-baiti), niyyarsa ce ke matsayin zare takobinsa (na yaki da masu yakar su).[12]

 

Da fadarsa (AS) cewa:

 

Mu ne sharifai; magabata daga cikin mu su ne Annabawa; kungiyarmu kuma ita ce kungiyar Allah (Hizbullahi). Azzalumar kungiyar nan kuwa ita ce kungiyar shaidan. Wanda ya daidaita mu da makiyan mu, to ba ya tare da mu.[13]

 

2- Game da dalilin da ya sa Ali (AS) ya kame hannunsa a wannan lokacin, Imam din ya amsa masa da wadancan maganganu da suka gabata, da wasu masu yawa da ba mu ambace a nan ba.

 

Wani da abu da ya wajaba mu ambata a nan shi ne cewa imaninmu kan Imam Ali (AS) da sauran tsarkakan zuriyar Manzo shi ne cewa su Imamai ne; kuma nassosin da muke bayyanawa yana tabbatar musu da haka ne. Akwai wani dan bambanci tsakanin Imamanci da Khalifanci; na farkon ya fi na biyun fadi; kai Khalifanci reshe ne da rassan Imamanci masu yawa. Duk Imami Khalifa ne amma ba duk wanda ake kira da Khalifa ne yake iya zama Imami ba. Wannan na nufin cewa Khalifanci ake iya karbe shi daga hannun Imamai ba Imamanci ba (da dai Imamanci na kwatuwa da yanzu ba Ahlul-bait ba ne Imamai). Aikin Imamanci kuwa ya wuce haddin mulki da bude garuruwa da fadada masarauta da harkokin kudi! wannan duk sarakuna na yi ko ba na Musulunci ba ne kuwa. 

 

E, gaskiya ne cewa Khalifancin ma hakkin Imami ma’asumi ne, shi yake da kudurin yaki da sulhu da nadin alkalai da sauran manyan abubuwa, wannan kuwa saboda siffarsa ta Isma ne, wanda ya sa shi a matsayin da zai kau da manyan kurakurai da ka iya yin mummunan tasiri a rayuwar al’umma da makomarta. Wannan shi ne takaitaccen akidar Imamanci da ’yan Shi’a suka yarda da shi ga Ahlul-bait (AS).

 

Idan Mansur da irinsa suka fahimci wannan zai yi musu sauki su fahimci cewa ba zai yiwu a suranta fakuwar Imami gaba daya daga rayuwar al’umma ba. Kasancewarsu Imamai ya tilasta musu yunkurin kawo gyara daidai da yanayin da suka sami kansu a ciki. Don haka yakinsa da sulhunsa, yukurinsa da kame hannunsa duk suna gudana ne a wannan tsaiko na Imamanci:

 

Kace: “Sallata da ibaduna, da rayuwata da mutuwata (duk) saboda Allah Ubangijin talikai ne. Ba Shi da abokin tarayya (a kan duk haka); da wannan aka hore ni, kuma ni ne farkon mai mika wuya” al-An’am: 162-163.

 

Af, ai ana iya lura da cewa a lokacin da bukatar daga takobinsa ya yi ai ya daga din kuma ya yi yaki. Ga yakin Jamal nan da ya gudana tsakaninsa da rundunar su Ummul-Mu’minina A’isha da Danha da Zubair! Ga kuma yakinsa da Mu’awuya. A wadannan zamuna ya ga yadda Musulunci ya fuskanci barazana ne daga tushensa, wannan ya sa ya yunkura har sai da ya kwantar da fitina. Ga zancensa game da haka:

 

Sai na kame hannuna har sai da na ga inda mutane suka dosa; sun kauce daga Musulunci; Ana kiran su zuwa danne addinin Annabi (SAWA); sai na ji tsoron idan har ban taimaki Musulunci da mutanensa ba, zan ga wata baraka ko gibi a cikinsa, (wanda) masifar haka a kaina za ta fi tsanani fiye da kufcewar shugabancin ku, wanda bai wuce jin dadin (yi wa mutane hidima) na ’yan kwanaki kadan ba, abin da ya kasance daga gare shi zai wuce kamar rairayi, ko kamar yadda girgije ke yayewa. Don haka sai na yunkura a cikin wadannan rikice-rikice, har sai da barna ta kau, addini ya natsu ya zauna da gindinsa.[14]

 

3- Amma game da abin da ya ambata na zancen Ali (AS) lokacin da aka taya masa Khalifanci bayan kashe Usman, yayin da ya ce: “Ku bar ni ku je ku nemi wani ba ni ba”, wannan haka ne; an riwaito Imama (AS) ya fadi haka; amma ba da manufar da Mansur ke nunawa ba. Imam (AS) ya yi musu haka ne don jaraba su; saboda an sabar da su a kan sabanin zai ja-gorance su a kai. Ku ji abin da ya fada a kan yadda mutane suka yo masa stinke bayan kashe Usman; ya ce:

 

Kafin na farga sai ga mutane sun yo min tsinke daga ko’ina kamar sakakkun garaku; suna turereniya gare daga kowane sashi; har suka tattake Hassan da Hussaini; suka kukkuje min gyaffan jikina biyu; suka yi dandazo suka sani a tsakiya kamar ina garken tumaki.[15]

 

Daga nan ne Imam ya fadi wannan Magana da Mansur ya dauko ta daga wani waje dabam, saboda ya cika musu hujja. Ilai kuwa! Imam na karba daga gare su aka samu masu hamayya, kamar yadda duk mai ’yar tsinkaya a kan tarihin abubuwan da suka faru a lokacin ya sani.

 

Haka nan Imam (AS) ya amsa tambayar da irinsu Mansur ka iya yi daga baya, na dalilan da suka sa ya karbi Khalifanci daga baya, da abin da yasa ya daga takobi a kan ’yan hamayya da suka nemi kawar da gwamnatinsa gaba daya; a kan haka yake cewa:

 

Na rantse da Wanda Ya tsaga kwayar hatsi kuma Ya halicci talikai, ba don halartar wanda ya halarta (don yin mubaya’a) da tsayuwar hujja da samun mataimaki ba, kuma (ba don) alkawarin da Allah Ya karba daga malamai kan kar su yarda da zaluncin azzalumai da kar su kawar da kai daga hakkokin wadanda aka zalunta ba, da na yi jifa da akalar (Khalifanci) na kyale shi; kuma da na yi mu’amala da lamarin a yanzu da irin yadda na yi mu’amala da shi a baya can; da kuma kun gane cewa wannan duniyar ta ku ba ta kai darajar majinar akuya ba a gurina!

 

9- Game da matsayin Imamanci a addini bisa mazhabar Shi’a kuwa mun yi bayaninsa a zaman da ya gabata. Karin bayani a kan haka shi ne cewa a ganinmu idan dalilan Imamanci suka zama ingantattu ga mutum, to sun lizimce shi da ya yi aiki da su dai dai da yadda ya fahimce su –fahimta irin wadda ta nisanta daga son zuciya. Idan ba su inganta a gunsa ba, ko kuwa ya fahimce su da wata ma’ana ta dabam –wadda ba son zuciya da guje wa gaskiya saboda tsoro ko wani amfani na duniya a tare da haka- to ya wajaba ya yi aiki ne da abin da yake da yakini a kai, ta yadda zai je wajen Allah cikin halin tabbas da abin da yake kai; idan ya zama ya yi daidai fani’ima –da ma haka ake so- idan kuwa ya yi kuskure, to zai samu uzuri a wajen Allah (SWT) na rashin ganganci da kokarinsa na neman gaskiya, duk kuwa da ta kufce masa. Wannan ita ce akidarmu. Yana iya samun haka a cikin littafanmu na akida, kamar Asalul-Shi’a Wa’usuliha na Sheikh Kashif al-Gita’i, da aka’idul-Imamiyya na al-Muzaffar da wasun wadannan na daga kananan littafan akida da suka yadu a kasar nan. 

 

10- Bayanin sama zai iya saukaka amsa fahimtarmu kan Musuluncin wadanda  suke zuwa daga nesa su karbi Musulunci ba tare da sun san wasicin Manzo (SAWA). Tare da haka ga wasu abubuwan lura a kan haka:

 

a).   Dukkanin Musulmi –Shi’ansu da Sunnansu- mun dace a kan cewa an dauke wa masu uzurin rashin sani alkalami. Wannan abu ne da kowa ya sani a Musulmi.

 

b).   Zancen rashin sanin wasici kuwa bai kasa rashin sanin fassarar wasu ayoyi da jin wani sashi na karantarwar Manzo (SAWA) ba; dalilin wannan na iya komawa ga gangancin shi mukallafi na rashin sanin haka; irin wannan Allah zai tambaye shi. Ko kuma wata matsala da ba ta shafi shi mukallafin ba; wannan yana da uzuri har sai ya sani.

 

c).   Af, to ai sanin Musuluncin ma baki daya akwai wadanda gaskiyar sakon ba ta je musu ba har yau din nan kuwa, uzurin irin wadannan nan sananne ne a tsakanin malaman Musulmi, matukar dai ba su gaza wajen neman sani ba.

 

d).   Amma zancen cewa Imam ya fadi cewa Annabi bai isar da sako kan Imamancin Ali (AS) kamar yadda ya isar kan Annabcinsa ba, wannan na daga karairayin da bai taba gani da idonsa ba; idan kuwa ya gani ya fito da littafin na Kashful-Asrar ya karanta nassin a gaban Salafawa masu sauraronsa sannan ya fassara. Na ga irin wannan kage kage daga wasu littafan marubutan da aka yi hayarsu don wannan, kuma makiya Musulunci (irin Amurka) ke daukar nauyin irin wadannan kage kage ta hannun aminansu, wadanda su ne shugabannin su Mansur; manufarsu kuwa ba ta wuce ta raunana mu don samun saukin aiwatar da bukatunsu na sace dukiyoyin Musulmi da danne su ba. Allah Ya kare Musulunci da Musulmi daga sharrinsu da na karnukan farautansu a tsakanin Musulmi.

 

e).   Musulmi duk sun dace a kan cewa Annabi (SAWA) ya isar da sako, wannan na daga abubuwan da kowa ya sani a addini; shi ne mazhabar magabatan ’yan Shi’a, kuma shi ne matsayin na yau dinsu; shi ne hukuncin malamansu, kuma shi ne imanin mabiya daga cikinsu; duk wanda ya dangana musu sabanin haka shi makaryaci ne mai yi wa makiya Musulunci hidima ta yada karairayi da dangana kage kage tsakanin al’ummar Annabi Muhammadu (SAWA).

 

f).    Fatawoyin Imam Khumaini na nan a hannunmu, haka karantarwarsa da zantukansa; babu wata magana irin waccan; ba a Kashful-Asrar ba, ba a waninsa na daga talife talifensa masu kima ba. Kai a cikin Tahrir al-Wasilah ma akwai fatawowin da suke kafirta masu nakasa Annabcin Annabi (SAWA), kamar a Littafin Tsarki, babin wankan mamaci da yi masa sallah da likkafani da bisne shi.

 

g).   Da alamu yana da akidar zargin Annabi (SAWA) da rashin isar da sako; to sai ya fito fili ya fada ba sai ya rika kewaye kewaye da gwaje-gwaje ba. Idan kuwa dole sai ya yi rabe rabe, to ya nemi wata marabar ba ta Shi’a ba, don ba zai samu sauki daga wajenmu kan abin da ya shafi Annbi (SAWA) da sakonsa da al’ummarsa ba!

 

10- Dangane da zancen karbar mukaman siyasa da Imam Ali (AS) ya yi a lokacin Umar (RA) nake ce masa:

 

a).   Wannan shi ne ainihin abin da na amsa masa a amsa ta 3 na wannan silsila da kuwa can sama kadan, cewa Ali Imami ne kuma Imamanci ya fi Khalifanci fadi balle gwamna ko alkalanci. Don haka duk lokacin da Imami ya ga yanayi ya samu da zai aiwatar da aikinsa na Imamanci, to ba ya sake da wannan damar.

 

b).   Wannan it ace sunnar tafiyar. Kakansu Annabi (SAWA) ya kasance juzu’in al’umma mai tasiri, wanda ke amfani da duk wata dama da ya samu wajen taimakon mutane da addini ko da kuwa a lokacin zaman Makka ne da babu akalar hukuma a hannunsa. Daga jikokinsa, Imam al-Ridha (AS) ya rike mukamin mai jiran-gado a gwamnatin Ma’amun Ba’abbase, wanda a karshe shi ne ma ya kashe shi. Daga malamai kuwa, Nasiruddini al-Tusi ya rike mukamin gwamnatin Abbasiyawa don taimaka wa Musulunci. Ibin Alkama ya kasance wazirin Khalifan Abbasiyawa Mu’utasam, wanda da ya ji shawararsa ma da an sami saukin matsalar Mangol.

 

c).   Ali (AS) bai dauki Khalifofin da suka gabace shi a matsayin kafirai ba; haka nan tsarkakan Ahlul-bait (AS) ba su dauki hatta Khalifofin Umayyawa da Abbasiyawa a matsayin kafirai (da ma’anar fita daga Musulunci) ba; haka malaman Shi’a na jiya da na yau ba su hukunta kafircin wadannan Khalifofi da mabiyansu ba (duk wanda ya yi musu da’awar haka ya yi musu karya da kage); don haka ba wani abin zargi don sun yi amfani da gwamnatocin Musulmi wajen cimma kyawawan manufofin Musulunci da aiwatar da ayyukansu na Imamanci.

 

d).   A fikhunmu muna da tanajin halaccin rike mukaman hukuma hatta a gwamnatocin Kafirai, balle ta Musulmi, matukar haka zai taimaka wajen kare gaskiya da yada addini, ko tunkude barna da taimakon raunana da sauran manufofin addini da rayuwa.

 

11- Waccan amsa da ta gabata ta amsa dalilin karbar mukamin alkalanci – duk da cewa rike mukamin alkalanci, kai hatta karbar mukamin gwamna ma bai tabbata ba a sahihin tarihi. Don haka na ambaci irin wancan amsa don sanin yadda lamari yake; wato Imami na iya karba don wadancan manufofi.

 

12- Da gaske ne Imam (AS) ya aika da ’yan’yansa don kare Usman daga barazanar kisa da ya fuskanta daga wasu Sahabbai da ba su yarda da yadda yake gudanar da mulki ba. Wannan na nuna cewa:

 

a).   Ba kamar yadda Mansur ke son nunawa ba, Imam ba ya ganin Usman a matsayin kafiri; haka ma mabiyansa a jiya da yau ba su dauki Usman a matsayin kafiri ba.

 

b).   Wannan na bayyana matsayin Ali (AS) ne na rashin amincewa da irin wannan matakin da wasu suka dauka na daukar doka a hannunsu. Ali (AS) ya fi son Musulmi su magance matsalolinsu ta hanyoyin lumana, sai a inada haka ya gagara.

 

c).   Wannan na nuna halin girma irin na Ali (AS); a lokacin da manyan Sahabbai suka ki taimaka masa (kamar yadda Ibin taimiyya ya tabbatar da haka a cikin Minhajul-Sunna), Ali ya yi kokarin taimaka masa da shawarwari; haka ma da aka hana ruwa shiga gidansa Ali (AS) ne ya rika diba yana kai masa, a karshe kuma ga shi yana kokarin kare shi daga kisa, duk da bai yi nasara ba a kan haka, kamar yadda bai yi nasara wajen hana bisne shi a makabartar Yahudawa da akayi ba (saboda wadancan Sahabbai sun hana binne shi a makabartar Musulmi).

 

 

 

Amsoshin Kai-tsaye Ga Tambayoyin

 

7)    Imam Ali ya yi bayanai a kan hakkinsa, kuma ya yi kira ga mutane da su dawo hanya, kuma wasu sun ji sun dawo, wasu kuma kuma sun yi kunnen-uwar-shegu. Imam Ali (AS) Imami ne ba mai kwadayin mulki ba, don haka bai fahimci maslahar Musulunci a yakar wadannan Khalifofi ba. Kuma a lokacin da maslahar Musulunci ta wajbata masa yakar kungiyar su Talha da Zubair, karkashin Ummul-Mu’minin A’isha ya yake su? Haka ma ya yaki Mu’awuya da wannan mahangar.

 

8)    Zancen Imam (AS) cewa: “Ku bar ni ku je ku nemi wani ba ni ba” ba ya nuna kau da kai daga hakkinsa, a’a don ya cika musu hujja ne. Kuma ya tabbatar da haka yayin da ya masa bukatarsu daga baya, yayin da ya karba bayan ya gindaya musu sharuddansa kuma sun amince? Sannan kamar yadda ya fada, idan akwai abin zargi shi ne wanda ya kwace hakki ba wanda ya hakura da hakkinsa ba!

 

9)    Dukkan Musulmi –Shi’a da Sunna- sun dace a kan cewa Annabi (SAWA) ya isar da sako, da cewa duk wanda ya karyata haka kafiri ne; don haka duk wani sako da bai isa ga wani ba, wannan ko dai saboda gazawarsa ne ko kuma wani sababi ne da bai shafi aikin isar da sakon da Annabi ya yi ba. Kuma Musulmi sun dace a kan uzurin wanda ya bar wata karantarwar Musulunci ba bisa ganganci ba.

 

10) Imam (AS) yana iya karbar mukamin siyasa da matsayin gudanarwa saboda sauke nauyin dake kansa daidai gwargwadon yadda hali ya samu, haka kuma don karantar da mabiyansa yadda ake tafi da lamurra a kowane irin yanayi.

 

11) Imam ya dauki matakin taimakon Usman ne saboda shi Ali bin Abi Talib ne, mai halin girama, babba dan babba, haihuwar Tauhidi, renon Musulunci, wanda ya sha daga tarbiyyar Annabi (SAWA) tun yarantarsa har ya rabu da Annabi (SAWA). Don haka wannan na daga halin Annabta da ya koya daga Manzo (SAWA).

 

 

 

Na mu Tambayoyin

 

1)    Sanannen abu ne cewa a lokacin Ibin Taimiyya da lokacin Ibin Abdul-Wahab akwai wadanda ba su da labarin karantarwar nan na Wahabiyanci na “Mushrikai Masu Sallah” ko “Musulmi Mushrikai”, shin wadannan da basu san Wahabiyanci kamar mu da muka sani muka ki bi ba, su ma din arna ne Mushrikai?

 

2)    Akwai wadanda har yanzu ba su san wani abu wai shi Wahabiyanci ba, duk kuwa da suna sallah da azumi, kuma sun yarda da abin da Allah da ManzonSa suka yi horo da hani a kai, shin yaya matsayin Musuluncinsu a addininku?

 

3)    Muhammad bin Abdul-Wahab ya fadi cewa shirkan Musulmi ya shafi hatta wasu daga Sahabbai, shin wadanne Sahabban ne irin wannan shirka ya shafa?

 

4)    Me yasa shugabannin Wahabiyawa suke da alaka da kud da kud da makiya Musulunci tun ba yau ba; kuma wannan alaka ta ki raunana, tare da Allah ya ce: “Ba za ka samui mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira ba suna kaunar wadanda ke gaba da Allah da ManzonSa koda kuwa sun kasance iyayensu ne ko ’ya’yansu ko ’yan’uwansu ko danginsu….”?

 

5)    Me yasa ku ke tsananta gaba da Sufaye da ’yan’uwansu ’yan Shi’a, wadanda suke dauwama a zikiri (don tsananin son Allah), suke raya ranar haihuwar Manzon (don tsananin kaunarsa) ko da kuwa sun kasance iyayenku ne ko ’ya’yanku ko ’yan’uwanku ko danginku?

 

6)    Me yasa kuke tsananta gaba ga ’yan Shi’a kuna kirkiran karairayi da kage kage kuna yadawa a kan malamansu da shugabanninsu da mabiyansu saboda kawai suna tsananin kiyayya da manyan makiya Allah da ManzonSa n duniya?

 


 

 


 

[1]Buga misali ya ke yi da dutsen nika irin Labarawan kauye, wanda ke da mariki a tsakiya; inda ake zuba abin da za a nika yana sama, wurin zubowar abin nikan yana kasa; ana juyawa gari ko kullu yana gangarorowa. Imam ya misalta kansa da marikin, wanda sai dai alharai su zubo daga gare shi alhali babu abin da ke iya isa gare shi. Nagartaccen misali ne ga Larabawa.

 

[2]Nahjul-Balagha, huduba ta 48, wadda aka fi sani da Shaqshaqiyya.

 

[3]Hudubar Shaqshaqiyya, a cikin Nahjul-Balagha it ace  huduba ta 48.

 

[4]Nahjul-Balagha, shafi na 201huduba ta 144.

 

[5] Nahjul-Balagha: Huduba ta 83.

 

[6] Nahjul-Balagha: Huduba ta 93.

 

[7] Nahjul-Balagha: Huduba ta 234

 

[8] Nahjul-Balagha: Huduba ta 90

 

[9] Nahjul-Balagha: Huduba ta 143

 

[10] Nahjul-Balagha: Huduba ta 3

 

[11] Nahjul-Balagha: Huduba ta 101

 

[12] Nahjul-Balagha: karshen Huduba ta 185.

 

[13] Nahjul-Balagha: Huduba ta 156.

 

[14]Nahjul-Balagha, huduba ta 48, wadda aka fi sani da Shaqshaqiyya.

 

[15]Nahjul-Balagha, huduba ta 48, wadda aka fi sani da Shaqshaqiyya.

 

 

 

 

 

Last modified on

28 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel