RAAF Official Website

A+ A A-

Yunkurin Musulunci

Rate this item
(0 votes)
Yunkurin Musulunci
Daga:
Sheikh Saleh Zaria
This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

________________________

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Wannan kasida, cikin yardar Allah, zata yi kokarin nazari ne a kan Yunkurin Musulunci har zuwa karni na ashirin da daya.

Yunkurin Musulunci shi ne abin da ‘yan’uwa a nan bangaren ke kira da Gwagwarmayar Musulunci; wanda a turance aka san shi da Islaminc Movement; a labarbce kuma al-harkatul-Islamiyyah.

Al’amarin ‘Gwagwarmaya’ babba ne mai fadin mahanga. Ba al’amari ne da ya ta’allaka da wasu mutane banda wasu ba ko wata kasa banda wata. Gamammen al’amari ne da ya shafi rayuwar kowane Musulmi, ya sani ko bai sani ba.

Don haka kasidar ta dauki wani dan karamin bangare ne daga wannan al’amari mai mahimmancin gaske. Za ta waiwayi yadda babban malami, manzarci, masanin addini da rayuwa, Ayatollah, Allama, Ustaz, Shahid Murtadha Mutahhari ya kalli gwagwarmayar Musulunci: ta’rifinta, iyakokinta, tarihinta da abubuwan da suka kamata mai bin wannan tafarki ya lizimta; duka a takaice. Allah muke roko da ya sa mu dace, Ya kuma kyautata niyyoyinmu.

Ta’arifi

Ustaz al-Shahid, Muratadha Mutahhari (RA) ya kalli yunkurin gwagwarmayar Musulunci a matsayin reshe ne na aikin kawo gyara al-Harka al-Islahiyyah; wanda ba dukkan shi ne  gwagwarmayar Musulunci ba.

Kalmar Islahi kalma ce ta larabci, dake nufin ‘tsari’, ‘daidaitawa’ da ‘gyarawa’. Kishiyar kalmar ita ce Ifsadi, wato ‘lalatawa’, ‘watsawa’ da ‘batawa’.[1] Wannan zai sa a iya ta’arifin Islahi, a shar’ance da: “aikin da yake nufin tsara al’murran mutane, a daidaikunsu ko a jama’arsu, a matsayin su na iyali, anguwa, gari, kasa ko al’umma.”

Akur’ani mai girma ya yi amfani da wannan kalma a kan duk wadannan ma’anoni[2], har da ma’anar: “gyara al’umma”, wanda shi ne mahallin maganarmu. AlKur’ani ya kira Annabawa da Muslihun, wato masu kawo gyara.

Kira zuwa ga kawo gyara kuwa ruhi ne na Muslunci, in ji Ustaz al-Shahid. Kum kowane Musulmi, a matsayin shi na Musulmi, mai kira ne zuwa ga islahi a farkon farawa, ko: “akalla yana daga masu goyon bayan kira zuwa ga Islahi.[3]” Wannan kuwa saboda kira zuwa ga Islahi, banda kasancewarsa sifar Annabawa da Manzanni, daya ne kuma daga cikin daidaikun horo da aikin kirki ne da hani da mummuna (al-Amru bil-ma’arufi Wal-Nahyu anil-munkari), wanda ke cikin rukunin zamantakewa cikin karantarwar Musulunci[4].

 Kawo Gyara Ko HidimaGa Jama’a

A wannan zamanin, in ji Allama, mun ga yadda kawo gyara cikin al’umma ya sami wani babban matsayi a wajen mutane, har suka shiga ba shi muhimmanci; wannan wani abin yabo ne. Sai dai wasu kan wuce iyaka; yayin da suke ganin cewa duk wani aiki ko hidima in dai bai shiga cikin abin da suka kira da aikin kawo gyara cikin al’umma ba, ba shi da wata kima; suke ganin cewa matsayin kowane mutum ya ta’allaka ne da irin yadda ya lizimci aikin kawo gyara cikin al’umma. Irin wannan tunani, a ganin Ustaz al-Shahid, ba ingantacce ba ne. Domin gano maganin sankara (cancer) hidima ce duk da kuwa ba aikin kawo gyara ga al’umma ba ne. Samar da ci-gaba na ilimi hidima ce alhali ba aikin kawo gyara cikin al’umma ba ne. Likitan dake aiki dare da rana don warkar da marasa lafiya, yana aiwatar da hidima ne ga al’umma; amma ba aikin gyara al’umma yake yi ba. Dalilin haka kuwa, kamar yadda Shaikh al-Shahid ke gani, shi ne saboda aikin gyara al’umma na nufin: “Sauya zamantakewar mutane zuwa manufar da ake bukata”; ayyukan wadancan kuwa ba haka suke ba; don haka bai kamata mu ki yabon ayyukan wadancan ba bisa da’awar cewa ba su taka wata rawa wajen ayyukan kawo gyara cikin al’umma ba. Alal missal, ayyukan Sheikh Murtadha al-Ansari, wanda daya ne daga cikin manyan fakihai; ko na Mulla Sadra, wanda daya ne daga cikin manyan masana falsafa Musulmi, duk manyan hidimomi ne masu matukar daraja, a daidai lokacin ba ayyukan kawo gyara ba ne.

Shahid al-Allama ya yi bayani da cewa ayyukan Annabawa, Manzanni da Imamai shi ne kawo gyara, a fagage dabam daban na siyasa, tattalin arziki da zamantakewar  mutane baki daya. Don hak a wurare dabam daban aka kira su da Muslihun. Imam Ali (alaihis-salam) mai kawo gyara ne. Haka Imam Hasan (alaihis-salam) cikin sulhusa da Mu’awuya, haka Imam Husaini yayin arangamarsa da Yazid, haka….haka….

 YUNKURE-YUNKUREN KAWO GYARA A TARIHI

Banda tarihin Manzo (sallallahu alaihi wa’alihi) da Imaman Ahlulbaiti sha biyu (alaihimus-salam), wannan tarihi dake cike da darussa da shiryarwa, za mu sami tarihin Musulunci cike da yukure yunkuren kawo gyara fiye da kowace al’umma, in ban da cewa kawai tarihin na mu ne bai ba wannan janibin hakkin da ya kamace shi na bincike da nazari ba.

Tun akalla shekaru dubu da suka wuce  tunanin bayyanar Muajaddadi da Mai Raya addini, a farkon kowane karni,ya fara yaduwa a tsakanin Ahlusunna da farko, sannan ‘yan Shi’a. Ahlusunna na riwaito wani hadisi daga Abu Huraira dake cewa:

A farkon kowane karni Allah zai tayar wa wannan al’umma da wanda zai jaddada mata  addininta.[5]

Duk da cewa ba a la’akari da isnadin wannan hadisi, ta fuskar tarihi kuma ba a karfafa shi ba, sai dai yaduwar irin wannan tunanin da karbuwarsa a tsakanin Musulmi yana bayyana yadda Musulmi ke jiran mai kawo gyara ko masu kawo gyara a farkon kowane karni; ta yadda wannan ya sa ma’abuta kowane yunkuri da bore a tsakaninsu na sa kansu a wannan matsayi.

A takaice dai muna iya cewa: A ra’ayin Shahid Allama Mutahhari, “Islahi, mai Islahi, yunkurin kawo gyara da jadadda addini, kamar yadda ake kiransa daga baya-bayan nan, duk wasu sanannun abubuwa ne a tsakanin Musulmi.[6]Wannan ya sa Shahid ke ganin cewa nazari na bin diddigi dangane da yunkure-yunkuren kawo gyara ko harkat al-Islamiyya  a tarihance abu ne mai matukar afani, bisa fatan da ya yi na cewa wadanda ke fagen wannan aiki na Annabawa zasu tabbatarwa kansu da na natijar da ake bukata.

Abu ne na daabi’a cewa yunkure-yunkuren da suka nemi kawo gyara ba su kasance daya ba, kuma ba dukansu ne suka kawo gyaran ba. Wasu daga cikin su sun yi da’awar kawo gyara, sun kuma yi aiki a kan haka bias hakika. Amma wasu sun yi amfani ne da sunan kawo gyara wajen kawo fasadi. Yayin da wasu suka fara daidai, amma sai suka karkace daga kasashe.[7]

 Yunkure-Yunkuren Alawiyawa

Shahid al-Allama ya bayar da misali na farko a wannan babi na yunkure-yunkuren kawo gyara a tarihi da yunkure-yunkuren Alawiya a lokutan Khalifancin Umayyawa da Abbasiyawa, inda ya ga cewa mafi yawan wadannan yunkure-yunkure sun kasance: “na kawo gyara ne”, sabanin wasu yunkure-yunkure masu yawa wadanda muninsu ya kai ga sun kalubalanci Musuluncin ne ma baki daya! Dalilin da ya sa Allama ya kira wadancan yunkure-yunkure na Alawiyawa da cewa mafi yawansu na kawo gyara ne, shi ne saboda la’akari da yadda suka iya girgiza fushin al’umma a kan mahukuntan Abbasiyawa ja’irai.

 Yunkurin Shu’ubiyya

Wannan wani yunkuri ne da ya kasance na kawo gyara da farkon al’amarinsa, yayin da ya riki taken Ya ku mutane, hakika mun halicce ku ne daga Namiji da Mace, sai muka sanya ku al’ummu da kabilu (dabam daban) don ku san juna. Lallai mafificin ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi ku takawa wajen kalubalantar bambance-bambancen Umayyawa. Akidarsu ta daidaitawa ne ma yasa aka rika kiransu da Ahalul-Taswiyah. Saboda kuma sun riki waccan aya ta AlKur’ani ya sa ake kiransu Shu’ubiyyah. Sai dai wani abin takaici shi ne suma mabiya wannan tafarki sun fada cikin tarkon abin da suke yaka, yayin da suka karkace suka zama kungiyar kabilanci; wannan ya sa muminai daga cikin su masu son gaskiya da bin Musulunci daidai suka janye. A karshe ma dai mahukuntan Abbasiyawa ne suka rika amfani da wannan kungiya wajen cinma manufofinsu.

 Yunkurin Kawo Gyara Aiki Ne Na Zamantakewa Ko Na Tunani?

Allama Mutahhari ya bayyana cewa wasu daga cikin yunkure-yukuren kawo gyara na Musulunci sun kasance na tunani ne, yayin da wasu suka kasance na zamantakewa. Wato na farkon na kawo sauyi ne na tunani, yayin da na biyun ke kawo sauyi cikin mutane; wasu kuma duka biyun suka hada. Ya bayar da misali da yunkurin Ma’adumin wajen kalubalantar Mangul a Sibzawar dake Khurasan a matsayin yunkurin sauya al’umma. Haka ya bayar da misali da yunkurin Ikhwanul-Safa a matsayin yunkurin sauya tunani.

A karshe Allama  Mutahhari ya yi bayanin wasu yunkure-yunkure a tarihi da suka saba da wadanda ya ambata. Wadancan su na “ci-baya” ne, alhali wadannan na “ci-gaba” ne. ya bayar da misalin wadancan da yunkurin Asha’irawa a karnin hijra na hudu, da yunkurin Ikhbariyyun, daga ‘yan Shi’a, a karnin hijra na goma, da yunkurin Wahabiyya a karnin hijra na goma sha biyu. Irin wadannan duk sun yi amfani ne da wani gurbi na tunani a tsakanin gama-garin mutane wajen cusa gurbatattun tunane-tunanensu game Musulunci cikin raunanan kwakwale.

 GWAGWARMAYA TA FARKO A WANNAN ZAMANI

A tsakiyar karnin hijra na goma sha uku, daidai da karnin miladiyya na goma sha tara ne  guguwar gwagwarmayar Musulunci ta taso a duniyar Musulmi; wadda ta game Iran, Masar Syria, Lebanon, Arewacin Afrika, Turkiyya, Afganistan da Indiya. Bayyanar wannan guguwa ya faru ne bayan lafawarta na tsawon karnoni. Bayyanar ta kuma na matsayin wani mayar da martani ne ga sabon salon yakin yamma ga raunanan kasashe, a ciki har da na Musulmi; wannan sabon salo kuwa shi ne ‘Mulkin Mallaka’; wanda ya bullo ta hanyar siyasa, tattalin arziki da al’adu. Ita kuwa wannan guguwa sai ta zama wani nau’I na yunkurin ‘wayarwa’ da ‘jaddada rayuwa’ a duniyar Musulmi.

 Sayyid Jamaluddin al-Afagani

Shahid al-Allama na cikin wadanda suke ganin cewa ko shakka ba bu Jamaluddin Asad Abadi, wanda aka fi sani Afagani, shi ne farkon wanda ya fara ta da wannan guguwa ta wayarwa a kasashen Musulmi. Shi ne wanda ya tona hakikanin matsalolin zamantakewar da ke addabar Musulmi, ya kuma bijiro da hanyoyin kubuta daga gare su.

Sayyid Jamaluddin ya ja-goranci gwagwarmayar kawo gyara ta fuskokin zamantakewa da tunani. Ya yi nufin samar da wani yunkuri a tunanin Musulmi wanda zai gyara rayuwarsu. Kuma wani abin sha’awa da Sayyid Jamaluddin, shi ne bai takaita da wani gari banda wani ba, ko wata kasa ko wata nahiya ban da wata ba. Ya kasance yana yawan tafiye-tafiye zuwa yankunan Asiya, Turai da Afrika; yana haduwa da kungiyoyi dabam daban a kowane gari. Har ma an ce a wasu garuruwan Musulmi ya shiga har cikin sojoji don ya yi musu tasiri.

Tafiye-tafiyen da Sayyid Jamaluddin ya yi zuwa kasashen Musulmi ne ya sa ya fahimci halin da duniyar Musulmi ke ciki. Yawonsa kuma a yankin Turai ne ya sa ya fahimci duniyar da ya ke ciki da kyau. Kamar yadda hakan ya sa ya gane hakikanin Turawa da manufofin shugabanninsu na goyon bayan kama-karya a kasashe,da mulkin-mallaka daga waje. Irin kafuwar da ya samu ne ya sa ya sami kyakkyawar masaniya da matsalolin duniyar Musulmi da kuma maganinsu.

Sayyid Jamaluddin ya yi matukar yin amfani da wadancan matsaloli biyu –wato kama-karya a cikin gida da mulkin mallaka daga waje- wajen wayar da kan mutane. Ya yi matukar yakar su da tsanani, wanda a karshe har sai da ya bayar da rayuwarsa a wannan tafarki. Ya yi imani da cewa yakar wadannan miyagun abubuwa biyu yana kasancewa ne kawai ta hanyar wayewar Siyasa da shigan Musulmi cikin harkokin siyasa ba ji ba gani.

Ta fuska ta biyu kuma Sayyid Jamaluddin ya yi imani da cewa idan har Musulmi suna son cimma manufofinsu da daukakarsu da darajarsu, to babu makawa sai sun koma zuwa ga Musuluncin asali. Ganin bayan bidi’o’I da karkacewa sharadi ne na asasi a kan wannan. Ya kasance yana kira zuwa ga hadin kan Musulmi; yana tona asirin wasu boyayyun makirce-makirce na ‘yan mulkin mallaka wajen kawo munafunci da rarraba ta fuskar addini da ma wasu fuskokin da ‘yan mulkin mallaka ke yi. Saboda tsananin rikonsa da ka’idojin hadin kai ya kasance ba ya fadar mazhabarsa da garin da ya fito duk yadda aka yi da shi. In an tambaye shi daga ina yake yakan ce daga garin Musulmi; mecece mazhabarsa yakan ce Musulunci.

Ya kasance yana ganin koda an sami wata alaka ta kusanci tsakanin masu kishin addini da mahukunta, matukar dai sun kiyaye kishin addini da kyakkyawar alakarsu da al’umma, to wannan na iya zama aiwatar da ka’idar nan ta furu’a ne mai cewa: ya halatta a yi amfani na’urorin makiyi don maslahar al’umma.[8]

A wani gefe, ra’ayin Shahid Mutahhari na iya kara bayyana game da gwagwarmayar Musulunci idan muka kalli yadda ya yabi matakan Jamaluddin Afagani; a kan haka yake cewa:

Wata baiwa da Sayyid Jamuluddin ke da ita shi ne bayan kasancewarsa wayayye, ya kuma kasance yana kiran mutane zuwa ga samun ilmomin zamani da amfana da wayewar Turwan yamma. Ya kasance yana yakar jahilci da ci-baya na kimiyya da fasaha da masana’antu. A daidai lokacin kuma ya riski hadarin dake tattare da tasirantuwa da wayewar Turawa. Don haka ya kasance yana kiran Musulmi da koyon ilumman sana’o’in Turawa tare da hamayya da tasirantuwa da tunane-tunanensu a kan duniya da al’amurra.[9]

 

Matsalolin al’umma da suka yunkurar da Sayyid Jamaluddin, kamar yadda Ustaz al-Shahid ya hakaito, sun ne:

1-Mulkin kama-karya dake gudana a cikin garuruwan Musulmi.

2-Jahilci da rashin wayewa dake addabar Musulmi, da matsanancin ci-baya a ilmance da yanayin zamantakewa da suke fama da su.

3-Yaduwar miyagun akidu cikin tunane-tunanen Musulmi, da nisantarsu da Musuluncin asali na hakika.

4-Rarraba tsakanin Musulmi ta fuskar mazhabobi da wasu al’amura da ba su shafi addini ba.

5-Mulkin-mallaka da ya yi musu kabe-kabe a gaba.

 

Sayyid Jamaluddin ya yi bakin kokarinsa wajen fitar da hanyoyin magance wadancan matsaloli. Ya yi amfani da abubuwan da suka samu a lokacinsa, irin su tafiye-tafiye, alakoki, laccoci, yada littafai da buga mujallu da kirkirar kungiyoyi da mu’assasosi dabam daban don aiwatar da ayyuka a wannan fanni. A takaice hanyoyin da Ustaz al-Shahid ya bayyana cewa Sayyid Jamaluddin ya bi wajen magance matsalolin duniyar Musulmi a lokacin sun ne:

1-Yaki da son-kan ‘yan kama-karya.

2-Ganimantuwa da ilumma da sannai na zamani.

3-Komawa ga Musulunci na asali.

4-Imani da Musulunci da dogara da shi.

5-Yaki da mulkin-mallaka daga waje.

6-Kira zuwa ga hadin kan Musulmi.

7-Samar da ruhin jihadi a cikin al’ummar Musulmi.

8-Magance matsalar jin rauni a gaban Turawa da ya addabi Larabawa.

 Har ila yau Shahid Mutahhari ya bayyana manyan manufofin Sayyid Jamauddin al-Afgani kamar haka:

1-Musulmi su zama wayayyun mutane, wadanda suka san zamunansu, suka kuma lakanci sana’o’in zamani.

2-Samar da wata al’ummar Musulmi ‘yantacciya, wadda ta kubuta daga duk wani kang na harshe, yanki, mazhaba ko wani abu daban; wadda mutanenta suke ‘yan’uwan juna.

3-Kubutar da Musulmi daga tabaibayin ‘yan mulkin mallakan wajen da ‘yan kama-karyan cikin gida.

4-Musuluncin asali na Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa’lihi), wanda ya tsira daga duk wasu jone-jone da shige-shigen ra’ayoyin mutane, ya zama shi ke hukunci cikin mutane.

5-Musulmi su anfana da ilumman masana’antu da kimiyya da fasahar Turawan Yamma amma da kiyaye ruhin Musulunci da kore irin tunanin Turawan game da duniya.

6-Musulmi su siffantu da ruhin jihadi, su dawo da ruhin nan na su na izza da daukaka; ta yadda ba za su karbi zalunci, kaskanci da danniya ba.

 Mutum Tara Yake:

Shahid ya bayyana cewa a iyakla saninsa Sayyid Jamaluddin Afgani bai bayyana ra’ayinsa game da tsarin iyali da tsarin karatuttukan Musulunci ba. Don haka, in ji Shahid :

Ba mu san yadda Sayyid Jamaluddin ke kallon wadancan tsare-tsare da ma’aunin Musulunci ba”.

Haka nan Allama ya bayyana cewa Sayyid Jamaluddin bai waiwaiyi falsafar siyasar Musulunci, yanayinta da hange-hangenta ba, duk kuwa da ya kasance mai matukar yakar ‘yan mulkin mallaka da ‘yan kama-karya. Wata kila, Allama ya ci gaba da cewa, saboda nutsuwarsa cikin yaki da mulkin-mallaka da kama-karya ne ba su ba shi daman yin haka ba.[10] Wata kila ya yi imani ne da cewa fada da mulkin-mallaka da kama-karya shi ne mataki na farko a gwagwarmayar Musulunci, da cewa matukar Musulmi sun yi nasara a matakin farko, to lokacin ne za su san abin da za su yi a mataki na biyu. Ta iya yiwuwa kuma, in ji Allama, mu dauki hakan a matsayin nakasa a cikin ayyukan Sayyid Jamaluddin.

 Sheikh Mugammad Abduhu

Wani mutum da Ustaz al-Shahid ya kalla daga cikin ‘yan gwagwarmaya a wannan zamanin, kuma wanda ra’ayin Shahid game da shi ke iya ba mu hoton tunaninsa game da gwagwarmayar Musulunci a karnonin baya-bayan nan, shi ne Sheikh Muhammad Abduhu. Ya kasance almajiri kuma abokin Sayyid Jamaluddin Afagani. Sheikh Muhammad Abduhu ya yi imani da cewa duk abin da ke gare shi a wannan tafarki daga Sayyid Jamaluddin ne.

Allama al-Shahid ya bayyana cewa bayan Sheikh Muhammad Abduhu ya rabu da Sayyid Jamaluddin ya koma Masar, abin da ya shagalta tunanisa a lokacin  shi ne al’amarin Musulunci da Bukatun Zamani. Ya kasance yana tunani kan hanyar da za ta hada Musulunci da ilimin zamani da ci-gaba a tsakanin al’ummar Masar. Wannan kuwa saboda ganin yadda wasu malaman addini suka daskare ne.

Sheikh Muhammad Abduhu, sabanin Sayyid Jamaluddin, ya kasance yana jin wannan nauyi ne a matsayin malamain addini; don haka ya kasance yana neman hanyar da zata kubuta daga gazawa da wuce-gona-da-iri a wannan fagen. Wannan ya sa Sheikh Muhammad Abduhu ya bijiro da wasu al’amura da Sayyid Jamaluddin bai bijiro da su ba; kamar Fikihul-Mukarin, wanda ya hado ra’ayoyin malaman mazhabobin sunna guda hudu da wasun wannan. Haka ya kasance yana da ra’ayi na masamman dangane da Ijma’I na furu’a, wanda ya saba da ra’ayin da ya yadu tsakanin malamai a lokacin. Wannan kuwa duk don amsa wasu bukatu ne da suka taso daga baya. Haka shi ya zo da cewa ka’idar nan ta Shura da ke Musulunci ita ce ka’idar Dukuradiyya wadda Turawa suka bijiro da ita bayan saukar Musulunci da karnoni.

Har ilau Sheikh Muhammd Abduhu, kamar Sayyid Jamaluddin, ya yi kokarin tabbatar da cewa Musulunci na iya zama akida mai shiryarwa, kuma tsaikon tunani na al’umma, ta yadda zai tabbatar musu da dacewarsu ta duniya da lahira. Haka nan ya yi ta kokarin bayyana wasu amfanoni na zamantakewa ga wasu ibadun Musulunci kamar salla, azumi, zakka, hajji da ciyarwa.

Shima, irin Sayyid Jamaluddin, ya yi aiki wajen samar da hadin kan duniyar Musulmi da ya nisanta daga bambance-bambancen launin fata, harshe, mazhaba da wurin zama.

Manyan bambance-bambancen dake tsakanin Shiekh Muhammad Abduhu da Sayyid Jamaluddin abu biyu ne:

1-Sayyid Jamaluddin na ganin wajibcin bore da juyin-juya hali; alhali Sheikh Muhammad Abduhu na ganin kamata ya yi a bi a hankali.

2-Sayyid Jamaluddin na ganin kamata ya yi a matakin farko a fara da kalubalantar ‘yan mulkin mallaka da ‘yan kama-karya; domin dole ne a tsige tushen fasadi daga tushensa tun farko; alhali Sheikh Muhammad Abduhu, masamman a karshe rayuwarsa bayan ya koma Masar, yana ganin tarbiyya da karantarwa shi ne aikin farko kafin dulmiya cikin tsagwaron harkokin siyasa. Wannan bambanci, ta iya yiwuwa ya samo asali ne a kan kasancewar abin da kowane daya daga cikin wadannan manyan mutane biyu ya yi ya cika na dayan ne; wannan kuwa bayan ganin duk sun hadu a kan:

1-Wajibcin komawa zuwa ga mabubbugar asali ta Musulunci da kalubalantar tushen karkacewa.

2-Fassara hukunce-hukuncen Shari’a da abin da ya dace da zamani, sabanin rufe ido da bin duk hanyar da magabata suka bi ba tare da tantancewa ba.

3-Nisantar rarraba da kungiyanci.

4-Ta’akidi a kan raya asalin ijtihadi da bude kofarsa.

4-Kokari wajen sanin ruhin addini na hakika; sabanin busasshen kallon da aka saba da shi a da.

Bayan wadannan bayin Allah biyu akwai manyan ‘yan gwagwarmaya biyu daga Ahlusunna da Allama Murtadha Mutahhari ya yi nazari a kansu; wadannan kuwa su ne Sheikh AbdulRahman Kawakibi, dan kasar Syria. Da Ikbal Lahori dan kasar Indiya. Inda za mu dauki kowane daya mu dubi yadda Ustaz al-Shahid ya kalle shi da mun kara samun haske a kan nazarce-nazarcen shi a kan yunkurin Musulunci a karnonin baya-baya nan. Sai dai haka ba zai  yiwu ba; na farko saboda karancin lokaci, na biyu kuma saboda haka zai sa mu fita daga haddin abin da muke magana a kai.

Sai dai ya zama dole a nan mu dan yi ishara da wani al’amari mai mahimmanci da Shahid al-Allama ya fada dangane da guguwar sauyi da ta taso a kasashen Musulmi daga baya-bayan nan.

Ya bayyana cewa babu wasu gwaraza fitattu daga kasashen larabawa in ba wadannan ukun ba. In ma wasu sun bayyana, to wadanda suka ci gaba da hanyar da shi Sayyid Jamaluddin al-Afgani da Muhammad Abduhu da Sheikh AbdulRahman Kawakibi suka fara ne, kuma ambatonsu bai karfafa ba. Ya ci gaba da bayanin cewa akwai wasu mutane a kasashen larabawa da suka yi da’awar kawo gyara da gwagwarmaya irin su AbdulHamid bin Yadis  daga Algeira, da Tahir al-Zahrawi daga Syria daAbdulKadir daga Maroko da Jamaluddin al-Kazimi daga Syria da wasun wadannan, illa ba su iya aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata ba. A nan Shahid al-Allama tambayoyi ya yi game da abin da ya haifar da haka da cewa: mai ya sa wasu mutanen banda wadancan ukun, wadanda za mu iya dauka a matsayin gwarazan kawo sauyi, ba su bayyana ba a kasashen larabawa? Kuma wadanda suka bayyana mai yasa ba su yi aikin ta ingantacciyar hanya ba? Tun farko ma, mai yasa ruhin gwagwarmaya ya yi rauni a garuruwan Musulmi, masamman larabawa? Mai ya sa kungiyoyin kabilanci na larabci da irin su jam’iyyar Ba’ath da tunanin gurguzu suka fi tasiri a zukatan matasan larabawa fiye da gwagwarmaya?

Amsar da ya ba wadannan tambayoyi ne ke da mahummanci gare mu, kuma suke kara bayyana mana irin yadda yake kallon mabubbugar tunanin gwagwarmaya.Ya ce:

Yayin amsa wadancan tambayoyi kowa na iya kawo amsarsa bisa dogaro da dalilansa na masamman. Amma ni, a kashin kaina, ina ganin babban dalilin da ya sanya gwagwarmayar Musuluncin da Sayyid Jamaluddin al-Afgani ya fare shi ya rasa mahimmancinsa da tunzurarwarsa shi ne yadda mafi yawan masu da’awar kawo gyara, bayan Sayyin Jamaluddin da Muhammad Abduhu, suka rungumi akidar Wahabiyanci, da yadda suka kange kawunansu a  kuntataccen tsaiko nan na tunanin wannan tafarki (na Wahabiyanci). Wadannan sun sauya waccan gwagarmaya ta kawo gyara ne suka mayar da ita gwagwarmayar Salafiyya; sannan yayin binsu ga Sunna din ma suka sauko zuwa bin Ibin Taimiyya. A hakika sun sauya ka’idar nan ta komawa zuwa ga Musulunci na hakika zuwa komawa zuwa ga Hambaliyya, wadda ake dauka daga cikin mazhabobi marasa zurfin mahanga a Musulunci. Da haka sai suka juya akalarsu daga fito-na-fito da ‘yan mulkin mallaka da ‘yan kama-karya zuwa yaki da akidun da suka saba da na Hambaliyya masamman na Ibin Taimiyya.[11]

 MALAMAN  SHI’A  DA  AKIDAR  GWAGWARMAYA

Ya zuwa yanzu duk abin da muke magana kan tunanin kawo sauyi da gwarazan gwagwarmaya a duniyar Musulmin Ahlusunna. Sai dai ana da sabani a kan ainihin mazhabar Sayyid Jamaluddin al-Afagani, wasu sun tafi a kan cewa shi Ahlusunna ne, wasu kuwa suka ce shi Shi’a ne. Ko ta halin kaka dai, Allama Shahid Mutahhari na daga cikin wadanda suke ganin shi Shi’a ne.; don haka, kamar yadda ya fada da kan shi, ya kawo shi cikin jerin mujaddadan  Sunna ne saboda mafi yawan aikace-aikacen shi a garuruwansu ya aiwatar da su.

Amma dangane da yunkure-yunkuren kawo gyara a tsakanin ’yan Shi’a, wannan ya saba kwata-kwata da yadda yake a tsakanin ’yan Sunna a ra’ayin Allama Shahid Murtadha Mutthhari; domin a wajen Shi’a wannan aiki na daukar wani salo ne na daban. Sai dai duk da haka, su ma sun ja-goranci yunkure-yunkuren kawo gyara dake bisa tsari, kuma wanda ya haifar da natija. Shahid na ganin tsarin ’yan Shi’a na kawo gyara ya fi zurfi kwarai da tushe. Har ma yake cewa:

Ba ma ganin yunkure-yunkuren kawo gyara irin yunkurin Tabacco a tsakanin Ahlusunna, wanda aka kalubalanci mulkin mallakar Biritaniya karkashi ja-gorancin malaman addini; wanda kuma shi ne ya haifar da karewar wani mulki na kama-karya a Iran.[12]

 Haka, In ji Shahid, ba ka ganin sauyi irin sauyin nan na thauratul-Ishrin na Iraki, wanda ya kalubanci wani shiri na ’yan mulkin-mallakan Birtaniya a kan wannan kasa ta Musulmi; wanda shi ne ya haifar da samun ’yancin Iraki. Ko irin sauyin nan na thauratul-dostur mai kalubalantar kama-karyan mahukuntan Iraniyawa; ko irin yunkurin da ya haifar da gwamnatin Musulunci ta yanzu a Iran, wanda malamai, karkashin ja-gorancin Imam Khumaini, suka ja-goranta.

Duk wadannan yunkure-yunkure sun faru ne a hannun malaman Shi’a, wadanda a lokuta da dama, kamar yadda Ustaz al-Shahid ya tabbatar, da wuya za ka ji suna zantuka kan  gwagwarmaya. Misali yunkurin Tabacco da malaman Shi’a suka fare shi a Iran, nasararsa ta kasance ne a hanun babban marja’in Taklidi al-Haj Mirza Hassan al-Shirazi. Thauratul-Ishrin kuwa da malaman Shi’a a Iraki suka fare shi don yakar turawan mulkin-mallakar Ingila, ya kasance ne karkashin ja-gorancin babban mujtahidi Sayyid Mir Muhammad Taki al-Shirazi. Thauratul-dostur kuwa da ya faru a shekarar miladiyya ta 1905, ya kasance ne karkashin ja-gorancin Mulla Muhammad Kazim al-Khurasani da Sheikh Abdullahi al-Mazandarani, wanda ke cikin malaman Najaf a wannan lokacin. Har ila yau wasu manyan malamai biyu na da matukar tasiri a wannan yunkuri na dostur, in ji Allama al-Shahid, wadannan kuwa su ne Sayyid Abdulllahi al-Bahabahani da Sayyid Muhammad Tabataba’i.

 JUYIN  MUSULUNCI  A  IRAN

Ya zuwa yanzu za mu iya kusantar inda muka dosa a wannan kasida. Domin mun matso kusa kwarai, inda zamu duba yadda Ustaz al-Shahid ke kallon juyin Musulunci da ya fara tun a shekara ta 1963 a Iran, kuma ya sami nasara a watan Febrarun shekarar miladiyya ta 1979.

Ya zama dole a nan mu fadi cewa: abin da kowa ya sani ne cewa, juyin Islama da ya sami nasara a kasar Iran, wanda a sakamakonsa aka kifar da daya daga cikin miyagun gwamantocin ’yan kama-karya da karnukan farautar Yamma, ya tabbatar da hasahen masu gwagwarmaya na yakinin samun nasara a karshe. Juyin ya canza akalar duniyar Musulmi, kuma ya zama ja-gora wajen haskaka zukatan ’yantattu a ko’ina cikin duniyar Musulmi.

 Dukkan Kungiyoyi na da Hannu a Juyin

Allama Shahid Muratadha Mutahhari ya bayyana cewa juyin Musulunci a Iran bai takaita da wani gungu na mutane su kadai a Iran ba, bai kuma kadaita da ma’aikta (kamar juyin Faransa) ko manoma (kamar juyin da ya faru a Rasha a wani lokaci da ya wuce) ba; haka juyin ba na ’yan jami’a ko ’yan kwadago kawai ba ne. Maimakon haka, in ji Allama, shi juyi ne da talaka da mawadaci, mace da namiji, dan birni da dan  kauye, dalibin jami’a da malamin addini, mai ilimi da jahili duk suka hadu suka gudanar da shi daidai wa daida. Ya ce tasirin bayanan shugbannin juyin daidai ne a wajen mutane.[13]

 Manufofin Juyin Musulunci Na Iran

Wani abu mai mahimmanci da zai iya nunawa mai sauraro irin yadda Ustaz al-Shahid ke la’akari da gwagwarmayar kawo sauyi, shi ne yadda ya kalli manufofin juyin Islam. A yayin bayyana manufofin juyin Islam, ya bijiro da wasu tambayoyi ne kamar haka: shin wace manufa juyin Islam a Iran ke nufi? Shin Dumukuradiiya ake nufi? Shin so ake a yanke hannun ’yan mulkin mallaka daga Iran? Ko so ake a kare abin da ake kira yau da hakkin dan Adam? Shin ana son gamawa da rashin adalci da magance fifita wani sashi a kan wani bisa zalunci ne? Shin ana son tsige tushen zalunci ne? ko so ake a yaki bautar duniya? Ko me ake nufi?

Amsar wadannan tambayoyi suna tabbata idan aka yi la’akari da asasan wannan juyi da bayanan da shugabannin juyin suka yi ta yadawa; amma a dunkule, in ji Allama, ana iya amsawa da “I” da “a’a”. ‘I’ cewa duk wadancan wani sashi ne daga manufofin juyin. Kuma a’a,  manufofin juyin musulunci basa iyakantuwa da wadancan bukatu; domin juyin Musulunci manufofinsa ba iyakantattu ba ne; domin Musulunci baki dayansa gamamme ne da ba a daidaita shi; kuma Musulunci ba ya karewa da isa zuwa wadancan manufofi. Amma wannan ba ya nufin cewa ta fuskar tsare-tsare da dabaru juyin Islama ba ya gabatar da wasu manufofi, ko ba ya lura da matakan cimma manufofin.

Ustaz al-Shahid ya ci gaba da fitar da manufar gwagwarmayar Musulunci daga Nahjul-Balagha, inda ya fitar da zancen Imam Ali (alaihis-salam) mai cewa:

Don mu dawo da dokokin addininKa, kuma mu bayyana gyara a garuruwanKa; ta yadda wanda ake zalunta daga bayinKa zai aminta; kuma a tsayar da haddodinKa da aka daina aiki da su.[14]

A karshe Shahid Murtadha Mutahhari ya bayyana cewa duk mai aikin kawo gyaran da iya samun nasarar aiwatar da wasu ka’idoji hudu, to kuwa zai yi nasara. Wadannan ka’idoji kuwa su ne:

1-Ya iya fuskantar da tunane-tunane da ra’ayoyi zuwa Musulunci na asali, kuma ya iya karya bidi’o’I da karakace-karkace daga zukata.

2-Ya iya samar da kyakkyawan sauyi a rayuwar gama-garin mutane, ta hanyar samar musu da abinci, matsuguni, kiwon lafiya, ilimi da tarbiyya.

3-Ya iya tabbatar da cewa ka’idojin daidaitawa da ‘yan’uwataka shi ke shugabanci cikin alakokin zamantakewa tsakanin mutane.

4-Ya tabbatar da dokokin Allah da shari’ar Musulunci a cikin al’umma.[15]

 Shugabannin Gwagwarmayar Musulunci

Ba abu ne na jayayya ba, in ji Allama Mutahhari, cewa kowace irin gwagwarmaya na bukatar ja-goranci. Sai dai abin tambaya a nan shi ne: idan hakikanin gwagwarmaya ta zama ta Musulunci, manufofinta suka zama Musulunci; to yaya ya wajaba shugabancinta ya kasance? Wadanne irin mutane ne suke iya zama shugabannin ta?

Sai Shahid ya amsa da cewa: wannan bayyanannen abu ne. Shi ne cewa, bayan sun zama suna da siffofin shugabanci da ya hau kan kowane shugaba, su kuma dole su kara da:

1-Samun cikakkiyar masaniya da Musulunci.

2-Su san manufofi da falsafar dabi’u, da zamantakewa da siyasa.

3-Su zama suna da cikakkiyar masaniya da yadda Musulunci ke kallon rayuwa. Ma’ana nazarin Musulunci game da samuwa, halitta, Mahalicci, mafari da makoma. Da nazarin Musulunci a kan mutum da al’ummar dan Adam.

4-Su sami cikakken riska a kan tunanin Musulunci. Ma’ana riskar ra’ayoyin Musulunci kan yadda ya wajaba mutum ya zama, yadda ya wajaba ya rayu, yadda ya kamata ya gina kansa da al’ummarsa, wa zai yaka kuma da wa zai yi hamayya. A takaice dai su san amsar Musulunci kan hanyar mutum da yadda ya kamata ya bi ta.

Bayan Shahid ya kawo wadannan tanaje-tanaje na shugabannin gwagwarmaya, sai ya rufe da cewa:

Sanannen abu ne cewa ba wanda zai iya daukar nauyin irin wannan shugabanci da wadannan siffofin da sharudda sai ya zama ya tarbiyyantu ne daga kokon tunanin Musulunci; sai ya san AlKur’ani da Sunna, ya san furu’a da sannan Musulunci, cikakken sani. A kan wannan babu wanda ke iya shugabancin gwagwarmayar Musulunci sai malaman addini.[16]

MATSALOLIN  GWAGWARMAYAR  MUSULUNCI

Wani abu mai mahimmanci ga kowane yunkuri shi ne sanin yadda za’a magance matsalolin da ka fuskanto shi. Harkar gwagwarmaya ma na fuskantar irin wadannan matsaloli; wadanda, a ra’ayin Allama, aikin shugabannin ta ne su samar da kariya da rigakafin wadannan matsaloli. Allama ya kara da cewa:

Tabbas ne cewa matukar shugabanin gwagwarmayar Musulunci suka kasa magance matsalolin gwagwarmaya, ko suka yiwa al’amarin rikon-sakainar-kashi, to kuwa ko dai gwagwarmayar ta watse, ko ta sauya ta zama wata harka ta daban da ke haifar da akasin natijar da ake so.[17]

Daga nan sai Shahid ya shiga kasafto matsalolin gwagwarmaya kamar haka:

1-Shigowar bakin tunane-tunane: wannan, in ji Allama, na iya shigowa cikin sahun ‘yan gwagwarmaya daga makiya ko masoya. Daga makiya yana shigowa ne a lokacin da suka ga alamun nasara ga wannan harka, ko haduwar hankulan mutane zuwa gare ta, ko fifikonta a kan sauran kungiyoyi; to a lokacin da suka fahimci rashin yiwuwar rusa ta ta waje, sai su yi kokarin rusa ta ta ciki. Misalai a kan haka cikin tarihinmu na Musulunci na da yawa, Allama ya kawo wani sashi daga cikin. Ta hanyar masoya da mabiya kuwa, yana faruwa ne a yayin da wasu mabiya suka jahilci manufofin harka; ko suka rungumi wasu akidun  Turawa suka yi kokarin basu siga ta Muslunci. Allama ya ambaci maganin wannan annoba da cewa shi ne ilmantar da mutane hakikanin Musulunci. Da daukar matakan da suka dace wajen ihtiyadi da kiyayewa sosai.

2-Zarbabiya: Dangane da wannan Allam Shahid ya bayyana cewa daukar madaidaiciyar hanya da matsakaicin matsayi a kowane abu yana da matukar wuya; domin, kamar yadda ya ce,  matsakaiciyar hanya a tafiya na da matukar kunci. Don haka idan ba a kiyaye ba, za sami masu wuce iyaka da yawa a cikin harka, abin da zai iya haifar mata da matsaloli masu yawan gaske. Shagaltar da mutane da ilimi na matukar taimakawa wajen rage wannan hali na wuce iyaka. Imamai sun yi hani da gullanci da tsananin gaske; domin cutarwarsa ga addini bai kasa cutarwa nasibanci ba.

3-Rashin cika aiki: Wannan na bayyana ne so tari, in ji Allama, a lokacin da shugabannin gwagarmaya suka ja mutane har zuwa kawar da azzalumai; to a wasu lokuta bayan sun kau da fasadi, sai kawai su koma shagulgulansu, sun dauka cewa komai ya kare daga nan. A karshe sai wasu su zo su rike akalar al’amurra, a lokuta da dama ba su kan bi manufofin ‘yan gwagwarmaya ba. Ustaz al-Shahid ya misalta musu yin haka da mutumin da aka kwacewa gona, sai ya yi ta wahala wajen kwato gonarsa, bayan ya kashe kudi da lokaci ya kwato ta, sai kuma ya ki noma ta ya bar wasu na nomawa. Ya ce abin da ya faru da shugabannin thauratul-Ishrin ke nan a Iraki, da shugabannin thauratul-Dostur a Iran, wadanda bayan sun yi nasara sai suka janye, a karshe wannan ya yi matukar taimakawa wajen jefa Iraki a halin da take ciki yanzu. 

4-Rashin Bayyanannen Tsari na gaba: A kan wannan Allama Mutahhari ya bayar da wani misali mai kyau dake bayyana abin da yake nufi karara. Ya ce misali mu ne mu ke da wani gini da muke son mu rushe, saboda ya lalace muke so mu sake wani mai kayu a madadinsa. A nan  zamu zama muna da surori biyu a kwakwalenmu; mummunar sura ta tsohon ginin nan, da kyakkyawar sura ta sabon da muke son yi. Dangane da mummunar sura, ba ya bukatar wani dogon bayani; domin mun san irin cutarwar da muke fuskanta. Amma game da sabon ginin da muke son yi, a nan dole ko dai mu sami injiniyan gini da zai yi mana wani tsari bayyananne; ko ya zama da ma muna da tunanin wani ginin da muka ga ingancinsa kuma mu ke son mu yi irinsa. To a bangaren gwagwarmaya, a kan sami wasu lokuta da wasu ke gabatar da kyakkyawan tsarin rushe zalunci da tsinge tushen barna; alhali ba su da wani bayyanannen tsari na gina adalci da islahi. Malaman addini su ne injiniyoyi, in ji Ustaz al-Shahid, wadanda al’umma ke jira su bayar da tsarin gini. Matukar kuwa suka kasa yin bayani da kowa ke iya gani game da abin da suke son ginawa, sai dai kawai fadar cewa: ‘za mu gina muku mafi kyawun gini’ to kuwa hakika za su bar wa al’umma wani gibi na shakka a kansu. Don haka dole ne kowace harka ta gabatar da tasre-tsarenta ga mutane su gani ba tare da wani boye-boye ba.

5-Rashin Kyakyawar Niyya: wani abu kuma da Allama ya sanya shi cikin annobobin gwagwarmayar tabbatar da addini shi ne wanda ke da alaka da ruhi. Wato niyya da kuduri. Allama ya ce:

Duk wani yunkuri na Allah, ya wajaba ya fara don Allah, ya kuma ci gaba don Allah. Kar ma’abuta gwagwarmaya su bari wani abu ya yi tasiri a cikin tunaninsu in ba Allah ba. Wannan ne kawai zai sa su dogara al’amuransu ga Allah.[18]

 SHARUDDAN NASARAR ‘YAN GWAGAWRMAYA

Allam Murtadha Mutahhari ya fitar da sharuddan nasarar gwagarmaya daga maganganun Imam Ali (alaihis-salam) . Imam ya fadi cewa:

Babu mai tsayar da horon Allah sai wanda ba ya sake da saussautowa,  kuma ba ya rikida kuma ba ya bin gurace-gurace.[19]

Wajen sharihin wannan magana ce Ustaz al-Shahid ke cewa:

Maganar da ake yi a nan game da tsayar da hukunce-hukuncen Allah ne. Magana ce a kan wani al’amari da masu aikin kawo gyara, ‘yan gwagwarmaya da masu kishin addini suka dade suna furta shi. Shi ne zance a kan wajibcin tsayar da dokokin Allah a duk lokacin da al’umma ta kai matsayin da ba ta riko da dokokin Allah. Zance ne dake alaka da wanene zai iya aiwatar da wannan aiki na Annabawa da Manzanni. Shin kowane mutum na iya yin sa tare da irin yanayin da muke ciki na ruhi da halayya?

Daga nan sai ya shiga daukar wadannan sharudda daya bayan daya yana bayaninsu kamar haka:

1-Nisantar Sake da Sassuci: A nan Ustaz al-Shahid ya bayar da misali da shi mai maganar kansa. Inda ya ce akwai lokutan da aka nami Imam Ali (alaihis-salam) shi da ya kyale Mu’awuya a matsayin shi na gwamna don wata maslaha ta siyasa. Amma sam, Imam ya ki mika wuya da wannan bukata. Ya kira hakan da “sake da sassuci”. A wasu lokuta kuma wasu mabiya da abokai sukan zo su yi ta ambaton Imam da lakabobi na yabo da sunaye iri-iri, tare da kau da kai daga kura-kuran da suka gani daga wasu ma’aikatansa; amma Imam Ali ya rika hana su ta mafi tsananin hanya, yakan ce musu:

 Kar ku yi mau’amala da ni da neman sake (jan-hankali),  kuma kar ku magana da ni da kalmomin da kuke amfani da su a kan masu girman kai.[20]

 2-Nisantar Jirwaya da Tasirantuwa: Shahid al-Allama ya yi sharhin wannan da tasirantuwar   dan gwagwarmaya da yanayin da yake son gyarawa. Ya bayyana cewa duk wanda ke son gyara raunin mutane, to ya wajaba ya tsarkake kansa daga wadannan illoli da rauni; kamar yadda mawaki ya fada:

 Mara tsoron Allah dake horon mutnane da takawa   

                                    Kamar likitan dake ba mutane magani ne alhali ba shi da lafiya

 Idan har a wasu lokuta mara lafiya na iya warkar da wani mara lafiyan, to a al’amarin ruhi ba haka abin  yake ba, in ji Ustaz al-Shahid.

 3-Yakar Gurin Bautar Mutane: Allama ya fassara wannan da ‘yantuwar ruhi daga duk wani gurin biyayya da bautar mutane. Dan gwagwarmaya kar ya sa ran ganin mutane na bauta masa dabbaka dokokin Allah a doron kasa ba ya kasancewa a hannun masu irin wannan nau’I na guri.

 Allah Ya ba mu sa’a baki daya. Walhamdu Lillahi Rabbil Alamin

 

 

 


[1]Shahid Murtadha Mutahhari, al-Harkatul-Islamiyya Fi Karnil-Rabi’u Ashar al-Hijri, shafi na 10.

[2] Ana iya samun haka a surar Bakara, aya ta 11 da ta 220; da Surar A’araf, aya ta 56,58 da 170; da Surar Hud, aya ta 88 da 111; da Surar Kasasi, aya ta 19.

[3][3]Shahid Murtadha Mutahhari, al-Harkatul-Islamiyya Fi Karnil-Rabi’u Ashar al-Hijri, shafi na 11.

[4] Ibid. shafi na 11.

[5] Ibid, shafi na 16.

[6] Ibid.

[7] Ibid, shafi na 17.

[8] Ibid, shafi na 25.

[9] Ibid.

[10] Ibid, shafi 37.

[11] Ibid, shafi na 55.

[12] Ibid.

[13] Ibid, shafi na 70.

[14] Ibid, shafi na 80.

[15] Ibid.

[16] Ibid, shafi na 83.

[17] Ibid, shafi na 88.

[18] Ibid.

[19] Nahajul-balagha, fasalin kananan kalmomi, hikima ta 107.

[20]Nahajul-balagha, huduba ta 11/107.

More in this category: Kaddara Da Hukumcin Allah »

61 comments

 • Phyday

  Off, treating an underlying form is adequately to veto erectile dysfunction. In other cases, http://freesildenafilsamples.com/ buy viagra sample or other direct treatments muscle be needed

  Phyday Comment Link
 • clomid price

  Love the website-- really user friendly and great deals to see!

  clomid price Comment Link
 • cialis 20mg

  I used to be suggested this web site by way of my
  cousin. I'm now not certain whether or not this publish is written by him as no one else
  know such unique about my trouble. You're incredible!
  Thank you!

  cialis 20mg Comment Link
 • pharmacy express

  What's up friends, how is everything, and what you wish for to
  say about this piece of writing, in my view its really remarkable in support of me.

  pharmacy express Comment Link
 • cialis coupon

  Passion the site-- extremely user pleasant and great deals to see!

  cialis coupon Comment Link

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel