RAAF Official Website

A+ A A-

Kaddara Da Hukumcin Allah

Rate this item
(0 votes)

 Kaddara Da Hukuncin Allah

 

Daga
Saleh Muhammad Sani Zaria
P.O. Box 4167 - Kano
E-Mail: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

 

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin-Kai

Shin me ke alakar mutum da ayyukansa? Shi akwai wani boyayyen karfi mai suna Kaddara wanda shi ke hukunta kowane abu a wannan duniya a ciki har da mutum da ayyukansa, ko kuwa al’amarin sabanin haka ne, wato mutum na da cikakken ‘yanci a duk dabi’u, halayen da  ayyukansa da kudurta makomarsa da kansa? Ko kuwa akwai wata akida ta uku da keda karfin hado duk biyun da gina matsakaicin matsayi, mai yarda da kaddara mai iko ta ko’ina, da kuma yarda da ‘yancin dan Adam wajen ayyana makomarsa?

Mafi yawan Musulmi sun kasu kashi biyu wajen amsa wannan tambaya. Wasu na ganin cewa ayyukan mu na mu ne Allah ba shi da wani iko a kan su. Don haka mu muke ayyana makomar mud a kanmu. Wandann sune Mu’utazilah. Alhali wasu na ganin sabanin haka, shi ne cewa duk yyukanmu a hakika na Allah ne mu mahallin aikin neb a mud a wani tasiri a kan duk abin da muka aikata. Masu wannan akida su ake kira da Asha’ira.

Wadannan akidu biyu sun yi matukar tasiri a rayuwar mabiyansu, ba kawai na ilimi ba, har ma na aiki, zamantakewa, mu’amaloli da kallon su ga rayuwa. Masu akidar Zabin Mutum na tafiya a hankali a wannan rayuwar, suna jin wani nau’i na ‘yanci da ayyuka tukuru don rayuwa, suna jin kalubale a duk abin day a fuskancesu. Akasin haka, wadanda suka yarda da kidar jabar na cikin halin dar dar koda yaushe. Suna jin dewa basu da ta cewa a gaban kaddara sai lallaba. Don haka sun kan kau da kai daga duk wani sababin waje kan al’amura.

Daga cikin al’amuran irin tasirin da wadannan akidu ke bayyana akwai al’amarin ciwon kanjamau. Masu imani da jabar na ganin tun da ta bayyana cewa wannan cuta mai kisa ce, to da zaran mutum ya kamu da ita an kaddara masa mutuwa, kaddarar Allah kuwa bat a sauyawa. A dabi’ance mai irin wannan akida ba zai taka wata mahimmiyar rawa wajen magance wannan cuta ba, kai! Kila ya yi wa’azin mika al'amurra ga Allah da kin kula duk wani dalili na waje!! Sabanin haka, wanda ya yi imani da zabin mutum dole ya zama cikin fadi tashi da hada hankali ga duk abin da zai magance masa cutarsa. Ta iya yiwuwa ya ga cewa in y adage zai iya rabuwa da cutar baki dayanta.

Kowane bangare na kokarin kafa dalilinsa na hankali da AlKur'ani, tare da kokarin bata dalilan daya bangaren.

Dalilin  Asha'irah: Suka ce ai tauhidin rububiyya na hukunta cewa baa bin da ke faruwa a duniyan nan, a ciki hard a ayyukan mutu, sai abin da Allah Ya so, don haka yarda da zabin mutum a kan ayyukansa na kore asalin tauhidin rububiyya kuma yana iyakance ikon Allah. Ban da wannan kuma, ga tarin ayoyi dake tabbatar da cewa babu abin da ke faruwa a wannan duniya face abin da Allah Ya hukunta. Ayoyi irin su:

Kuma mabudan gaibu a wurinSa suke, ba wanda ya san su sai Shi. Ya kuma san abi da ke tudu da (wanda) ke ruw. Babu wani ganye da zau fadi sai Ya san shi, kuma babu wata kwaya a cikin karkashin kasa sai Ya san ta, kuma (wani abu) danye ko busasshe face yana cikin littafi mabayyani (6:59).

Da fadar Allah Madaukaki:

Ka ce: 'Ya Allah Sarkin sarauta, Kana ba da mulki ga wanda Ka so, kuma kana tube mulki ga wanda Ka so, Kana daukaka wanda ka so, kuma Kana kaskantar da wanda Ka so; (dukkanin) alheri a hannunKa yake, lallai Ka mai iko ne a bisa komai.  (3:26).

Da FadarSa:

..Suna cewa: 'shin za mu sami wani abu daga nasara kuwa?' Ka ce: 'Hakika daukacin al'amari na Allah ne.' Suna boyewa cikin zukatansu abin dab a sa bayyanawa cewa: 'Da dai muna da wani abu na nasara dab a a kasha mu a nan ba.' Ka ce: 'In kun kasance a cikin gidajenku, da wadanda aka rubutawa mutuwar sun fito zuwa makwantansu.... (3:154).

Gama inda Allah Ya fito karara ya fadi kddara, inda ya ce:

Babu wani abu face a wajen mu akwai taskokinsa, kuma ba ma saukar da shi sai dai kaddara sananne (15:21).

Da cewa:

Kuma hakika Allah Ya sanyawa kowane abu iyaka (kaddara)." (65:3).

Da cewa:

Kowane abu mun halicce shi bisa kaddara. (54:49).

Har ma da shiryarwa da batarwa, kamar yadda Ya ce:

Sai Allah Ya batar da wanda Ya so, Ya kuma shiryar da wanda Ya so. (14:4)

Har ma suna iya kafa dalili game da cutuka da fadar Allah Madaukaki:

Ba wani abu na masifa da zai samu a cikin kasa, kuma ba wadda za ta same ku face ta kasance (a rubuce) cikin littafi tun kafin mu samara da ita, lallai wannan a wajen Allah mai sauki ne. (57:22)

 

Dalilin Mu'tazilah: Su kuma, a na su bangare suka ce; ko a tsakanin 'yan Adamu, ba a kama mutum da abin da bai yi ba. to haka ma abin yak e a wajen Allah; a ce ya tilasta mutane aikata abu sannan ya yi musu ukuba a kan aikin da shi Ya yi, wannan shi ne babban zalunci Allah kuwa Ya tsarkaka daga zalunci; hankali ya tabbatar da haka, kuma ayoyi da hadisai sun tabbatar da hukuncin hankali. Bugu da kari, ga tarin ayoyi dake tabbatarwa kowane mutum da abin day a aikata ba tare da nuna shsshigin Allah cikin ayyukan ba. Ayoyi irin:

Hakika Mun bayyana masa hanya, ko dai (ya zama) mai godewa ko mai butulci. (76:3).

Kuma ka ce: 'Gaskiya daga Ubangijinku take, to wanda ya so sai ya bad a gaskiya, wanda kuma ya so sai ya kafirta, hakika kam Mun tanadar wa azzalumai wuta.. (18:29)

Kai! akwai ma inda ya fito karara ya bayyana bayyanar ayyukan mutane ta hannunsu ba tare da shiganSa ba, inda Ya ce:

 

Barna ta bayyana a kan kasa saboda abubuwan da hannuwan mutane suka aikata don a dandana musu sashin abin da suka aikata ko watakila su dawo (hanya). (30:41).

Har ila yau ya ba mutane zabin abin da suke so a tsakanin duniya da lahira da fadarSa cewa:

Wanda ya kasance yana nufin ribar lahira to za Mu kara masa a kan ladansa, wanda kuwa ya kasance yana nufin ribar duniya, to za mu ba shi alhali a lahira ba shi da wani rabo. (42:20)

Da cewa:

Wanda ya kasance yana son dunoya ne (kawai) to sai Mu gaggauta wa wanda Muka so abin da Muka so daga cikinta; sannan Mu sanya masa jahannama ya shige ta yana abin zargi (kuma) korarre (daga rahamar Allah). Wanda kuwa ya nufi lahira ya kuma yi aiki domin ta alhali yana mumin, to wadancan su aikinsu ya zamanto abin godewa ne a wyrin Allah. (17:18-19).

Wadannan akidu biyu masu karo da juna na Asha’irah da Mu’tazilah su ne mafi yawan Musulmi suka runguma tun bayan Sahabbai, a karnin farko na Musulunci. Syn yi ta rikice rikice a zamuna daban daban bisa tasirin wani sashe na mahukunta, wadanda a lokuta sukan zabi dayan akydun su nemi tilasta shi a kan jama’a saboda ya danne musu mutane daga yunkurawa don yun hamayya da mulkinsu, wanda so tari na zalunci ne.

A hakika wadannan bangarori ba su iya ansawa juna amsar da kowane kewa dan’uwasa ba. Maimakon haka kowannen su ya mayar  da hankali ne a kan raunin abokin hamayyarsa sai ya shimfida karfinsa a nan ba tare da ya iya magance tashi matsalar ba. An ce wata rana Gailan al-Dimashki –wanda ke kare akidar kadariyyah- ya taba tsayawa a kan Rabi’atul-Ra’ayi –malamin Jabar- ya ce: ‘Kai ne ke da’awar cewa Allah na so a yi sabo ko (yana ishara bisa akidar Ash’irawa na cewa ayyukan bayi na Allah ne).’ Nan take sai Rabi’ah ya amsa masa da cewa: “Kai ne wanda ke da’awar cewa ana sabawa Allah ne don an fi karfinsa (ishara zuwa akidar Mu’utazilawa ta zame hannun Allah daga ayyukan  bayi). Haka habaice habaice sun gudana tsakanin malaman bangarorin biyu a kan wannan mas’ala; wata rana an ce Abu Ishak al-Farayini –dan jabariyyah- ya taba shiga majlisin alkali Abdul-Jabbar –Bamu’utazile-; suna hada ido sai Alkali Abdul-Jabbar ya yi shagube da cewa: ‘Tsarki ya tabbata ga wanda ya tsarkaka daga alfasha.’ Kamar yana masa habaici kenan da cewa ‘akidarka ta jabariyyah’ na hukunta dangana zalunci ga Allah, alhali Allah Ya tsakaka daga haka. Kafin ya rufe bakinsa sai Abu Ishak ya amsa da cewa: ‘Tsarki ya tabbata ga wanda ga wanda ba abin da ke gudana a masarautarsa sai abin da Yake so.” Wato cewa ‘kai kuma ka ragewa Allah da’irar mulkinSa da akidarka ta kadariyyah.

Kallon kowane bangare daga waje da nufin daidaita ayoyin, wanda shi ne aikin malaman da suka san abin da suke yi, zai tilasta hada karfin su biyu waje guda da magance inda suke da matsala. Da haka dole a dauki matakin “al’amari tsakanin al’amura biyun”, wanda shine akidar jikokin Ma’aiki (S.A.W.A), kuma da haka ma Sahabbai suka fahimci rayuwa a bayan ma’aiki kamar yadda haka zata tabbata.

Abin da wannan  akida ta uku ke cewa shi ne imani da kaddara ba ya lizimta jayayyar sabubba cikin faruwar al’amurra daga ciki har da ayyukan ‘yan Adam; wannan na faruwa ne kawai idan muka janye hannun mutum gaba daya –kamar yadda Asha’irah suka yi-, alhali babban kuskure ne mu ce Allah na yin kowane abu ba tare da wata hanya ba. A’a Allah Yana kaddara abubuwa ne ta hanyar sabubbansu da dalilansu na masamman. Haka nan idan muka dogara al’amura –a ciki har da ayyukan mutane- ga sabubba su kadai da zare hannun Allah gaba daya –kamar yadda akidar Mu’utazilah ke hukuntawa- to mun sami matsala da tauhidin rububiyyah mai hukunta sanin Allah ga komai da ikonSa a kan komai ba tare da wani kaidi ba.

Don haka mutum mahluki ne mai ‘yancin yi ko bari amma da ma’anar cewa an ba shi tunani da iko. Mutum ba Kaman dutse ba ne da ake tankwarawa ana juya shi kamar ‘robot’ ba shi da wani zabi ko katabus a kan abin da ya ke aikata ko kin aikatawa. A’a, koda yaushe mutum na samun kan shi a tsakanin hanyoyi biyu ne don ya zabi wadda yake so da cikakken ‘yancinsa da Allah ne Ya ba shi. Ba’a tilasta shi a kan bin wata da barin wata. Abin da ke bayyana masa hanyar da zai bi a rayuwa shi ne yanayin tunaninsa. Da wannan ne iyakokin ‘yanadamtaka ke bayyana, kuma ake iya ganin siffofin halayya da tarbiyya.

Don haka ayoyin da Asha’irah suka zo da su masu nuna cewa komai ke faruwa a duniya daga allah ne, haka ne bisa sharadi. Haka ma wadanda mu’utazila suka zo da su. Ayyukan dan Adam na daga kaddarorin na daga al’amurran dake ta’allake da sabubba, amma wannan bai kore hannun Allah kwata-kwata daga ayyukansa ba, tunda ai shi Ya halicce shi kuma yake gudanar da al’amuransa.

Wannan ita ce akidar Sahabbai bayan Annabi (SAWA).  Zamu iya fahintar haka ta wasu riwayoyi kamar haka:

1-Ya zo a cikin sharhin Nahjul-Balagha cewa: wata rana Umar ya yi tafiya zuwa Sham, kafin ya shiga sai labarin ballewar wata annoba a garin ya iso gare shi, sai ya shawarci wadanda ke tare da shi, sai gaba dayan su suka dace a kan cewa kar a shiga in banda  Abu Ubaidah bin Jarrah, yayin da yace wa Umar: ‘Haba sarkin muminai! Kana gudu ne daga kaddarar Allah?’ sai Umar ya amsa masa da cewa: ‘E ina gudu daga kaddarar Allah zuwa wata kaddarar ta Allah.’ Nan take wani mutum ya tabbatar musu da cewa ya ji Manzo (SAWA) na hana wadanda ke cikin garin da annoba ta balle da fita, da hana wadanda ke waje da shiga. Wannan ya yanke taraddudin da Umar ke cikin na shiga ko kin shiga, don haka sai ya koma.[1]

2-An riwaito cewa wata rana Imam Ali bin Abi Dalib (AS) ya kasance zaune jikin wani garu, sai ya karkato zai fadi, sai Imam ya tashi daga nan ya koma wani wajen, sai wani ya ce mishi: ‘Ya Amirul-Mu’uminin! Kana gudu ne daga hukuncin Allah?’ sai Ali (AS) ya ce masa: ‘E, ina gudu daga hukuncin Allah zuwa kaddarar Allah.’ Wato Allah ne ya kaddara in na zauna gini ya fado min in wahala ko ma in mutu; haka Shi ne ya hukunta in na gudu na tsira da rayuwata da lafiya na.

3-An tambayi Annabi (SAWA) a kan hirzozin da ake amfani da su don magani[2] shin suna iya sauya kaddara? Sai Manzo ya amsa da cewa: “Su ma ai kaddara ne.

Ya zuwa yanzu muna kusantar ainihin abin da ya tara mu a nan.

 

AJALI

Idan aka rubutawa mutum lokacin mutuwarsa akwai abin da ke iya sauya shi? Lokacin da zamu nemi maganin cutar mu ko kare kanmu daga abin da ka iya kashe mu, me muke nufi? Cewa wannan mataki na iya sauya makomar ajali?

Daga dogon zancen da ya gabata a kan kaddara, rabin amsar wannan tambaya na iya faruwa cewa ‘E, muna iya sauya makomar hukunci da karrar Allah da wani hukuncin da kaddarar ta shi, ta hanyar riko da sabubba; irin su ganin likita, shan magani, tsafta, rigakafi da sauran hanyoyin da ilimi ya tabbatar suna taimakawa a wannan fanin.

Don haka ta bayyana karara, bari mu bar AlKur’ani ya yi mana magana kan ajalin kamar yadda ya yi mana kan Kaddara. AlKur’ani mai girma ya kasa ajali zuwa kashi biyu, ajali mai sharadi da mara sharadi.

Ajali Mara Sharadi: Shi ne cewa zaman mutum a wannan duniya na da iyaka, wanda in ya cika dole ya bar ta:

Babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, lokaci (ajali) ne kayyadajje.. 3:145)

Ajali Mai Sharadi: Shi ne wanda ya ta’allaka da wani sababi daga sabubba na zahiri ko na badini. Shi yana sassauyawa. Ana tsawaita shi da gajarta shi. A kan shi tare da na n afarkon ne Allah ke cewa:

Allah Shi ne wannan da ya halicce ku daga tabo, sannan Ya hukunta muku wani ajali alhali ambataccen ajali na wajensa, sannan duk da haka kuna jayayya. (6:2).

Duk da malaman tafsiri sun kai su kawo game da bambancin wadannan ajalai biyu, sai dai bin diddigi da taro riwayoyi bisa fahimtar hakikanin hali na fifita fassarar ‘yan gidan Manzo (Ahlul-baiti AS). Wannan saboda ‘Mutan gisa ne suka fi sanin abin da ke gidansu’. A bisa wannan fassara ce muka iya kasa ajali gida biyu da ambaton su ya gabata.

Don haka lokacin da muke neman dauki daga abin da ke barazana ga rayuwarmu ko lafiyarmu da sabubba na zahiri, irin likitoci, magunguna, rigakafi da sauransu, ko na ruhi kamar addu’a, tawassuli da sauransu, muna fatan samun sauyi ne daga abin da ke sauyawa na ajali; dukkan su kuwa –mai sauyawa da mara sauyawa- daga Allah ne.

Hadisi daga Imam al-Sadik (AS), wanda yana cikin ‘yan cikin gidan Annabi (SAWA), na bayyana cewa:

Masu mutuwa saboda zunubai sun fi  yawa a kan masu mutuwar ajali. Haka masu tsawon rai saboda ihsani sun fi masu tsawon rai na shekaru[3]

Akwai irin wadannan hadisan da suka fito suna bayyana sauyin kaddara da ajali ta hanyar addu’oi, tawassuli da ayyukan alheri; wasu kuma na nuna karanta shekaru, talautawa da jarraba da cutuka da nau’o’in takurawa, a sababin wasu zunubbai. Mafi yawa nan an san su.

 

SAKAMAKO

Na yi kokarin bayyana cewa babu wani abu a Musulunci da ya hana kula da lafiya ta kowace fuska; ta fuskar rigakafi ne ko ta fuskar neman magani, tabbatar da lafiyar mutum ta hanyar gwaji ne da sauran hanyoyi da ilimin zamani ya sauwaka ta wannan fuska. Haka na kalli dalilan da wasu Musulmi, masamman malamai daga cikinsu, ke kokarin bayyanawa na cewa wadancan matakai sun yi karo da su; irin su kaddara da ajali.

Kan wannan mai cutar kanjamu, da ma duk wata cuta kowace iri ce, ba kawai yana da daman daukar matakan da suka kamata ba ne, a’a wajibi ne a kan shi. saboda sake da haka shi ne ainihin jefa kai ga mahalaka, wanda Allah Ya hane mu a cikin AlKur’an da cewa:

 

Kuma ku jefa kanku ga mahalaka.

Wannan aya ta hado wadanda suka kamu da wadanda ba su kamu ba. Sake, rikon sakainar-kashi da rashin kula da kai da cutar da kewa mutum irin wannan illa duk sun sabawa wannan aya da ire iren ta.


 


[1] Ibin Abil-Hadid, Sharh Nahjul-Balagah,Huxuba ta 132.

[2] Imam al-Gazzali ya ce tambayar a kan hirzozi ne da magani.

[3] Allamah al-Majlisi, Biharul-Anwar, juz’I na 5, shafi na 140.

 

 

 

 

60 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel