RAAF Official Website

A+ A A-

Shugabanci A Shi'a

Rate this item
(1 Vote)

Shugabanci A Shi'a:


Daga:
Sheikh Saleh Zaria
This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Tsarin shugabancin al'ummar musulmi bayan Manzo (SAWA) shi ne kashin bayan sabanin fahimtar dake tsakanin Shi'a da sauran bangarorin Musulmi masamman Ahlussunna.  Wannan ne ya sa na ke ganin cewa yana da kyau na dan gabatar da takaitaccen bayani kan wannan tsari na shugabancin al'umma a bayan Manzon Allah (SAWA), masamman kuma a lokacin Ghaibatul-Kubrah ta Imamul-Hujja da ta kebance mu ’yan Shi'a, ba tare da la'akari da iyakokin garuruwa da harsuna da nahiyoyi ko kasashe da mukan gindaya su a wasu lissafe lissafenmu na al'amurran duniya ba. Nake cewa:

Bayan shugabancin Allah (SWT) da Manzo (SAWA) da dukkan Musulmi suka dace a kai, babu mai shakka kan kasancewar Imaman Ahlul-bait goma sha biyu (Ma'asumai) su ne shugabannin ’yan Shi'a bisa Nassi.

Wato tun farko bisa Asala (wato tushe) Allah kadai ke da shugabanci "Ku dakata! halitta da shugabanci naSa ne Shi kadai”. Wannan kebanci shi ne abin da gabatar da KHABAR {Lahu} a kan MUBTADA' {al-Khalku Wal-Amru} ke lizimtawa a bisa ka'idar Nahawu. Wato a ka'ida cewa za a yi AL-KHALKU WAL-AMRU LAHU. An jinkirta al-Mubtada' (Al-Khalku Wal-Amru) ke nan, kuma an gabatar da Khabar (Lahu). Juya wannan ka'ida kamar yadda ya zo a ayar (na cewa: Alaa! Lahul-Khalku Wal-Amru) ya lizimta abin da suke kira da HASRU ko KASRU (wadanda duk suke da ma'ana daya na kadaice abu da muta'allikinsa a magana) a fannonin Nahawu da Balaga.

Idan ka fahimci wannan da kyau, zai yi maka sauki ka fahimci cewa shugabancin duk wani taliki daga talikai yana zuwa ne a layin kasa na wannan shugabanci ba a daura da shi ba. Wato shugabancin Annanabawa da Manzanni duk suna zuwa a kasan shugabancin Allah ne kuma bisa horonSa kawai. Wannan ne cikakken Tauhidi ke lizimtawa a Musulunci. Wannan ne ya sa kake ganin a duk inda Annabawa suke kiran mutanensu zuwa ga yi musu da'a suke gabatar da kira ga takawa: "YA MUTANENA KU JI TSORON ALLAH KU BI NI" Wanda wannan kira na su kan zo bayan kira zuwa ga Tauhidi: "YA MUTANENA KU BAUTAWA ALLAH SHI KADAI, BA KU DA WANI ABIN BAUTA SAI SHI". Wato bin Annabi cikan bautar Allah Shi kadai ne, kuma (bin na sa) na daga Takawa.

Bisa wannan tsarin za ka kalli biyayyar Ahlul-Bait (AS) da Annabi ya yi ta dora mutane a kai cikin ingantattun hadisai, irin na Thakalain, wanda a ciki ya jona wajibcin binsu da bin AlKur'ani. Wato babu yadda za a iya bin AlKur'ani ba tare da bin Ahlul-Baiti ba, haka lazimin bin Ahlul-Bait shi ne bin AlKur'ani.

To tunda Allah Ya hukunta takaita adadin Imamai da goma sha biyu, bisa hikimar da Shi Ya fi saninta, zai zama dayan Imaman nan zai yi tsawon rai kenan. Sai Allah Ya hukunta na karshensu, Sahibul-Amri Wal-Zaman (Rayukan Dukkan Talikai Fansa Gare shi), ya zama MAI-DOGON-ZAMANI; wanda kuma wata boyayyiyar hikima ta Allah ta hukunta tsawaitar fakuwarsa. Wannan dole zai haifar da shugabancinsa ga mabiyansa ya zama ta hanyar wasu (wato dai ba kai tsaye ba). Hankali da Shari'a kuma na tilasta ya zama shi ne mai zaben wadannan wakilai; saboda abin da ya gabata na cewa dama wannan shugabanci reshe ne na shugabancin Allah a kan bayinSa.

Duk ’yan Shi'a, daga malamansu har gama-garinsu, sun dace a kan cewa Imamul-Zaman ya fara shugabantar ’yan Shi'a ne ta hanyar nasabta Na'ibai hudu da za su rika kai-komo tsakaninsa da mabiyansa. Wannan shi aka kira da muddar Karamar Fakuwa wadda ta saura har na tsawon shekaru saba'in.

 

 WILAYATUL-FAQIH

 

 Ta bayyana a baya cewa cikan tauhidi shi ne yarda da kadaicin Allah a shugabancin bayinSa, kamar yadda AlKur’ani mai girma ya tabbatar: “Ku saurara! halitta da shugabanci na Shi ne Shi kadai.” Hatta shugabancin Manzanni da Imamai yana kasan wannan shugabanci ne ba daura da shi ba; don haka ake alamta su da BAYIN ALLAH kafin ambaton shugabancinsu. Mukan ce “Annabi Bawan Allah ne kuma ManzonSa” haka nan “Imamai Bayin Allah ne kuma WaliyyanSa.” Haka dai!!

Shugabancin Annabawa da Imamai yana da wata Khususiyya da ta bambance ta da ko wane irin shugabanci koma bayan nasu. Wannan kuwa shi ne cewa nasu shugabancin ne na Ma’asumai, wadanda muradansu ba ya taba sabawa da muradun Allah Madaukaki. Wannan ne dalilin da ya sa ka ji Allah na cewa: “Ku bi Allah kuma ku bi Manzo da ulul-Amri (wadanda su ne Ahlul-Bait)”. A wani waje ya nuna cewa wanda ya bi su Allah Ya bi. Kai har ma mutum ba shi da zabi kan duk abin da suka hukunta. Isma din nan kuwa wata halayya ce ta musamman da Allah Ya halitta tare da su, wadda take taimaka musu wajen nisantar duk abin da bai kamata ba, tare da ikonsu a kan haka.

Don haka nadin Allah ya tabba ga ManzonSa da WassiyyanSa Ma’asumai (AS). Su ne shugabannin daukacin talikai, kuma mahukunta. A hannunsu akalara abubuwa suke. Sauran mutane kuma mabiya ne gare su, wadanda ke karkashin kulawarsu.

Daga kan wadancan kuma babu wanda ke da akalar shugabancin mutane sai wanda Allah (SWT) ko Manzo ko daya daga Wasiyyansa suka nada; a lokacin sai wanda suka nada din ya zama mai shugabanci kan abin da suka nada shi a kai. Wadanda suka nada kan abubuwa mabambanta kuwa sun kai nau’i bakwai kamar haka:

1-Shugabancin Faqihai Masu adalci a kan mutane ta fuskokin da bayani zai zo a kansu.

2- Shugabancin Iyaye a kan ’ya’yamsu.

3- Shugabancin kakanni a kan jikokinsu (a lokacin rashin iyayensu maza).

4- Shugabnacin wanda aka yiwa wasiyya a kan wadanda aka yi wasici a kansu.

5- Shugabancin maza a kan matansu.

6- Shugabancin mamallakan bayi a kan bayinsu.

7- Shugabancin wakilai a kan wadanda suke wakilci a kansu. 

Shugabancin Faqihai Masu Adalci

Babin maganarmu shi ne shugabancin Faqihai masu adalci a kan al’ummar Musulmi a lokacin fakuwar Imamul-Assr (AF).

A lokacin Karamar Fakuwa, Imam al-Asr Waz-Zaman ya shugabanci mabiyansa ta hanyar wasu wakilai hudu da ya nada da kansa, kuma ya ambace su da sunayensu kamar haka:  (1) Abu Amr Uthman bin Sa’id al-Amari, (2) Abu Ja’afar Muhammad bin Uthman al-Amari, (3) Hussaini bin Ruh; da (4) Ali bin Muhammad al-Samari. Tarihin kowannensu da hanyar da Imam ya nada su da kuma yadda suka gudanar da wakilcinsu, duk wadansu abubuwa da suka fita daga haddin wannan makala. Illa dai yana da kyau a san cewa an tattaunasu, mai son karantawa sai ya neme su a muhallin da ya dace.

A lokacin Babbar Fakuwar Imam al-Zaman kuwa, ya danka shugabancin mabiyansa ne a hannaun Fakihan da suka cika sharudda. Su ne Na’iban Imam Mahdi (AF), wadanda ke da wilaya a kan dukkan muminai ta dukkan fuskkokin da Imamai ke da ita.

Riwayoyi masu yawa daga Ma’asumai (AS) ne ke tabbatar da wannan shugabanci, daya daga cikinsu it ace wadda ta zo a takardar dake dauke da sa hannunsa (AF), wadda ta fito a Ikmal-al-Din na Saduk (shafi na 484), da cikin littafin al-Ghaibah na Sheikh al-Tusi (shafi na 198) da littafin al-Ihtijaj na Tabrisi (juz’i na 2, shafi na 283); wadda a ciki Imam ke cewa: “Amma game da abubuwa masu bijirowa, a kansu ku koma ga masu riwayar hadisinmu. Domin su ne hujjojina a kanku, kuma ni ne hujjar Allah a kansu.”

Haka nan riwayar Abu Khadija, wanda ya riwaito cewa: Abu Abdullahi ya ce min: “Ku nemi wani daga cikinku, daga wanda ya san wani abu daga hukunce hukuncenmu, sai ku sanya shi mai hukunci a tsakaninku, lallai ni na nada shi mahukunci a kan ku, don haka ku mika masa wuya.” (Wasa’ilul-Shi’a, juz’i na 18, shafi na4, hadisi na 5).

A wata riwayar da suke yiwa lakabi da Makbulatu Umar bin Hanzalah, bayan an tambayi Imam abin da mabiyi zai yi a lokacin fakuwarsa, sai ya ce:  

Ya lura daga cikin ku, wanda ya riwaici hadisanmu, yake da nazari a halal da haram dinmu, kuma ya san hukunce hukuncenmu, sai su yarda da shi a matsayin mahukunci. Lallai na nada shi a matsayin mai hukunci a kanku. Idan kuma ya yi hukunci da hukuncinmu, sai (wani) ya ki karba daga gare shi, to hakika (wannan) mai wasa ne da hukuncin Allah, kuma mu ya yiwa tawaye. Wanda ya yi mana tawaye kuwa mai yiwa Allah tawaye ne, wannan (matsayi) kuwa ya kai haddin shirka (hada wani) da Allah (Wasa’ilul-Shi’a; juz’i na 17, shafi na 98-99, babi na 11, hadisi na 1).

Hadisan wadannan babin suna da yawa, wasu sun kasafto kusan talatin a talife talifensu, illa dai wasu na magana ne a kan shugabancin kansa ba tare da la’akari da nau’in shugaban ba, wasu kuma suna magana ne a kan shugabancin Imamai. Wadannan da muka jero sun isa zama hujja a kan shugabancin Faqihai adalai. 

Siffofi Da Sharuddan Mujtahidi Shugaba

Tasirin sharuddan kamala ga kowane shugaba ba boyayyen abu ba ne. A matsayin addinin Musulunci na addinin da ya damu da KARKO fiye da damuwarsa da GAYYA, ya gindaya karfafan sharudda ga duk mutumin da zai hau kujerar khalifantar ma’asumai. Wannan shi ne abin da gamammiyar dokar nan ta AlKur’ani mai cewa: “Yanzu wanda ke iya shiryarwa ya kamata a bi, ko wanda ba ya iya shiryarwa sai dai a shiryar da shi? Me ya same ku kuke hukunci haka?” take hukuntawa. Wadannan sharudda su ne:

1-       Ilimi mai zurfin da ya kai haddin Ijtihadi: wanda kuma aka same shi a daya daga mashahuran cibiyoyin ilimi na Shi’a dake Kum ko Najaf. Ana iya fahimtar isa zuwa wannan marhala ta hanyar shaidar manyan malaman da kowa ya mikawa wuya a fagen ilimi; ko ta hanyar shaidar shari’a (wato shaidu biyu masu adalci daga kwararru a wannan fannin) ko ta hanyar tawaturi, shi neyawaitar labari da yaduwarsa da suka samo asali daga kakkarfar madafa.

 

2-       Adalci: Shi ne lizmtar shari’a ta hanyar kiyaye wajibai da gujewa manyan zunubbai da kanana. Tare da kau da kai daga duniya da kyale-kyalenta da rashin nuna karkata zuwa ga tanaje tanajenta ta fuskar son tara dukiya da son mulki.

 

3-       Zama Namiji: saboda ba a tanaji mace don irin wannan mawuyacin aiki ba. Duk da cewa tana daman kaiwa kowane irin mataki na ilimin addini (kamar yadda take da wannan dama a dukkan fannin ilimi) har ta zama Mujtahida da za ta iya dogara da kanta wajen daukar hukunce hukunce ba tare da ta bukaci yin takalid da wani Mujtahidi ba, sai dai abin da ya shahara ne a tsakanin malamanmu –kai har da malaman Ahlussunna ma- cewa ba a dora mata nauyin irin wancan shugabanci dake bukatar dukkan lokutan shugaba ba.

 

4-       Tsarkin haihuwa: Saboda irin tasirin da dattin asali da rashin tsarkin tsatson da dan zina ke fama da shi -komai kyawun halinsa kuwa- ke iya yi a tsarkakakken matsayin shugabancin addini.

 

5-       Kwarewa a ayyukan zamantakewa: saboda abin da matsayin shugabancin marja’i ke lizimta na mu’amala da nau’o’in matsalolin mutane mabambanta na al’umma, irin wanda babu mai iya gudanar da shi daidai sai mai cikakkiyar kwarewa a kan rayuwar zamantakewa da dukkan nau’o’inta.

 

6-       Kwarewar Siyasa: Ta yadda zai iya fitar da kudurorin da suka dace da kowane irin yanayi daidai da yadda dabi’ar duniyarmu ta yau mai sassabawa ke lizimtawa.

 

 Akwai wasu sharuddan da ake ambata a mahallinsu, illa dai a fahimtarmu suna komawa ne ga daya daga wadannan da aka ambata, kamar yadda wasun wadannan din ke iya zama rassan wasu, ya danganta da yadda aka kalli lamarin. 

 

Ayyukan Shugaba Faqihi A Lokacin Ghaiba

 

A dunkule duk abin da ya hau kan Imami ya hau kan Faqihi a lokacin fakuwar Imami din. Wannan shi ne abin da tahkiki ke tabbatrwa. Wadannan abubuwa kuwa sun shafi sassan addini da duniya kamar haka:

 

1-       Fatawa: Shi ne tushe a ayyukan Faqihai. Aikinsu ne su yi amfani da kwarewarsu wajen fitar da fatawoyi a kan ibadu da mu’amaloli don amfanin mabiya. Kuma wajibi ne mabiya su bi fatawoyinsu, ta yadda wanda ya yi gaban kansa a ibada ko mu’amala, alhali shi ba shi da kasau mai tsoka a ilimi da zai sa shi a matsayin da ya dace, to ayyukansa batattu ne, har sai sun cika wasu sharudda masu wuyan cikawa.

 

2-       Tasarrufi a dukiyar Imam: Wato rabin Khumusi kenan, wanda shi ne Sahamin Imam. Haka yana da daman tasarrufi da dukiyar da aka rasa mamallakinta, da gadon wanda ba shi da magada da sauran irinsu.

 

3-       Alkalanci: Su ne alkalai a husumomi da sabanin dake faruwa tsakanin muminai. Don haka wajibi ne mabiya su kai kararraki da korafe korafensu ga mujtahidai ko masu magana da harshensu a duk inda suke da iko. Wanda ya kai shari’arsa wajen wasunsu a irin wannan yanayi, to ya karbi hukuncin Dagutu, wanda Allah Ya hore mu da kaurace musu. Kuma duk hakkin da ya karba haramiya ne a gare shi. Amma a halin da mujtahidi ba shi da iko (kamar yawa yawan kasashenmu a yanzu), to yana iya halatta mutum ya nemi hakkinsa ta yin amfani da cibiyoyin hukunci na yanayinsa, matukar babu wata mafita.

 

4-        Tsayar da Haddodi da Ta’azirat: Mafi yawa daga muta’akhirai (wato malaman da suka zo daga baya) daga malamanmu sun tafi a kan cewa Faqihai na da hakkin tsayar da haddodi da tsawatarwa (ta’azirat) a lokacin Ghaiba. Kai wasu ma sun hakaito shuhura ga wannan ra’ayin, wannan kuwa saboda rashin kaidi ko togiya a nassosin haddi da umumin (wato gamammen hukuncin) riwayoyin babin.

 

5-        Dukiyar Marayu: Abin dacewa ne a mazahabarmu cewa marayun da basu da waliyyi ko wasiyyi ko wakili daga waliyyinsu, kulawar dukiyarsu da kare ta daga salwanta yana hannun Fakihan da suka cika sharudda ne. Kai wasu na ganin haka na daga abin da kowa ya sani a mazahaba.

 

6-       Dukiyar Dolaye da Mahaukata: Wadanda ba su da mai wilayar shari’a a kansu. Sai hakkin kula da dukiyar ta koma hannun Faqihin da ya cika sharudda.

 

7-        Dukiyar Wanda Ya Faku: da dukkan nau’o’insa uku; wato a) wanda ba ya nan kuma ana da labarinsa, sannan ana sa ran dawowarsa. Sai dai wani lamari dake bukatar tasarrufi a dukiyarsa ta taso, kuma babu wani waliyyi ko wasiyyi ko wakili da ke da hakkin wannan tasarrufi; b) Wanda aka san inda ya tafi, sai dai ba a da ikon sanin halin da yake ciki da lokacin dawowarsa saboda nisan tafiyarsa ko kulle shi da aka yi; c) Wanda aka rasa labarinsa gaba daya. A duk wadannan Faqihi na da hakkin tasarrufi a dukiyarsu don magance matsalar da ta so.

 

8-       Auren Budurwai Da Dolaye Da Mahaukata Wadanda Basu da Iyaye da Kakanni Maza: Wannan mahallin sabani ne; amma akwai masu ganin cewa Faqihi na da hakkin aurar da wadancan nau’o’in mata ta hanyar zama waliyyinsu, bisa la’akari da cewa shi ne mai wilaya a kan dukiyoyinsu (ba ta kiyasi ba, sai dai ta la’akari da gamayyar ma’anar nassosin wadancan din ne da wadannan).

 

9-       Duk Abin da Ya Tabbata Cewa Yana Hannun Imam Na Kula Da Lamurran Mutane: Kamar sayar da kadarorin wanda bashi ya yi masa yawa, da sakin matar wanda ya bata bayan bincike da makamantansu, horonsu da yakin kare kai (wasu na ganin har fara jihadi ma, sai dai abin da ya shahara ne cewa babu mai hakkin fara Jihadi sai Ma’asumi). Wannan ya ginu bisa ijma’i ne ta hanyarmu.

 

10-     Duk Wani Aiki Da Ba Makawa A Yi Shi: Bisa dalilin hankali da Shari’a, kamar tasarrufi da wakafofin da suka ta’allaka da kowa da kowa, sauke wasiyyan mamata a lokacin da suka rasa sharuddan wasiyya, nade naden wasu mukamai da Faqihi ya ga bukatarsu da sauran irinsu.

 

 A lura da cewa ko wane daya daga abubuwan nan da na ambata, sun ginu ne bisa hadisan da maluma ke tattauna su a zauren karatuttuka masu zurfi na Fikihu da Usul (wato abin da ake kira da Bahathul-Kharij). A dabi’ance za a sami sabanin nazari a nan da can a tsakanin malamai a kan wadannan ayyuka na Faqihi.

 

 Bambanci Tsakanin Shugabanci Ma’asumai Da Na Faqihai

 

Daga abubuwan da suka gabata, mun fahimci nau’in shugabanci a Shi’a, wanda ya fara daga Allah Madaukaki da Ma’suman al’umma (wato Manzo da Ahlul-bait A.S), sai na Na’iban Mahadi na masamman da gamammun Na’ibai (wato Faqihai). Haka nan takaitaccen bayani ya gabata a kan dalilan shugabancin Faqihai Adalai, da iyakokin shugabancinsu, da nauyin da ya hau kan mabiya a kan wannan shugabanci. Lokaci ya yi da za mu tattauna kan ishkalin da ka iya bayyana ta hanyar karanta abubuwan da suka gabata. Wannan kuwa shi ne cewa, idan har mun yarda da cewa Imamai ma’asumai ne, kuma waninsu, komai iliminsa, ba ma’asumi ba ne, to ta wace fuska shugabancin wanda ba ma’asumi ba ke daidaita da shugabancin ma’asumi? Menene lamunin kuskuren da ka iya faruwa a hukunce hukunce da kudurorin su Fakihan? Domin adalci ba ya kore yiwuwar kuskure!!

Babu shakka wannan babbar tambaya ta ja hankalin malamai da manazarta, kuma sun tattauna ta ta fuskoki dabam daban. Abin da ke faruwa shi ne, shi shugabancin Fakihan ai ma’sumai ne suka tsara shi don haka hangen wannan matsala ba za ta taba gushewa daga tunaninsu ba balle sama mata magani.

Amsa wannan ishkali yana nan a hanyar fitar da hukunci da daukar kudurori da shari’a ta shatawa su Fakihan, wanda ke cikin faffadan babin nan na Usul al-Fiqh. A bisa tushe, asasn da ake gina Shari’a –a hanayar Ahlul-Bait (AS)- hudu ne. Su ne:

1-AlKur’ani:Shi ne Littafin Allah da Ya saukar da shi ga ManzonSa na karshe, Annabi Muhammad (SAWA), wanda kuma yake kunshe da shiriya da tsarin rayuwar Musulmi a ciki. Barna ba ta zuwa masa ta bayansa ko ta gabansa. Allah Ya kare shi daga gurbata na kari ko ragi, sabanin sauran littafan da aka saukar kafin shi. ’Yan Shi’a, kamar sauran Musulmi, sun yi imani da cewa wannan AlKur’ani dake hannun  mutane warwatse a garuruwa shi ne ainihin AlKur’anin da Allah Ya saukar, ba ragi ba kari. Wanda ya dangana musu wani abu sabanin haka makaryaci ne mai son tayar da fitina a tsakanin Musulmi, ko mai yiwa makiya Musulunci hidima ta hanyar sa shakku a Littafin Allah Ta’ala. Kar a kula wasu ra’ayoyi ko wasu zantuka da hadisan karya da suke fitowa daga nan da can ta dukkan bangarorin Shi’a da Ahlusunna, masu nuna gurbatar AlKur’ani. Irin wadannan ra’ayoyi da riwayoyi ya wajaba Musulmi su yi watsi da su, su kuma karyata su.

2-Sunna: Shi ne zancen Ma’asumi, da aikinsa da abin da aka yi a gabansa ya yi shiru. ma’sumai a wajen ’yan Shi’a su ne Annabi (SAWA) da tsarkakan Iyalansa, Ahlul-Bait (AS). Tace hadisai da fayyace su ya zama dole, saboda karairayi da tatsuniyoin Yahudawa da Kiristoci da makaryata da masu kirkiran labarai sun cika littafan hadisan Musulmi. Haka nan abubuwan da ’yan siyasa da masu bautar mulki da son tara abin duniya suka kirkira na karairayi suka danganawa Annabi (SAWA) don samawa kansu shari’anci da kubutar da laifukansu duk sun sami gindin zama a cikin hadisan dake hannun Musulmi. Hanyoyin tantace hadisai sun hada da nazarin isnadansu (wato masu riwayarsu) don sanin masu gaskiya da makaryata, ko masu mantuwa da rudaddu daga cikinsu. Ilimin da ke daukar nayin haka shi ake kira da Ilmul-Rijal ko al-Jarhu Wal-Ta’adil. Sai kuma ta hanyar matanin riwaya, inda ake auna shi da AlKur’ani, idan ya saba masa sai ayi watsi da shi. Wannan shi ne abin da ma’asuman suka yi horo da shi. Akwai sauran ma’aunan da ake tantance hadisai da su an yi bayaninsa a Ilmul-Diraya, da aka fi sani da Mustalahul-Hadith a tsakanin ’yan’uwanmu Ahlussunna. Babban bambancin dake tsakanin Shi’a da Ahlussunna a nan shi ne cewa su Ahlussunna sun takaita bincikensu da wasun Sahabbai, wato ba sa binciken Sahabi komai rauninsa, saboda akidarsu ta adalcin dukkan Sahabbai. Alhali ’yan Shi’a ba sa ganin ingancin fitar da wani wanda ba ma’asumi ba daga wannan ka’ida. Ana tattauna dalilan kowane bangare a makaranta.

3- Ijima’i: Ahlussunna na ganin cewa idan al’umma ta dace a kan wani al’amari, to wannan al’amarin ya zama ingatacce saboda abin da suke riwaitowa cewa Annabi (SAWA) ya ce: “Al’ummata ba ta dacewa a kan kuskure”. A bisa wannan asasi, al’umma za ta zama kamar Annabi ne da aka aiko, wadda ma’asumiya ce da ba ta kuskure. Irin wannan ittifaki shi ne abin da suke kira da Ijma’i, kuma suna mu’amala da shi kamar wahayi da Allah Ya saukar. ’Yan Shi’a kuwa ba sa ganin ingancin wannan hadisi. Don haka Ijma’i a wurinsu shi ne haduwar al’umma a kan wani lamari bisa sharadin shigan Ma’asumi cikin haduwar ta su. Wannan sharadi shi ne babban bambancin dake tsakanin Shi’a da Ahlussunna kan Ijma’i. Wani bambancin kuma shi ne cewa ’yan Shi’a na ganin cewa Ijima’i ba hujja ba ne a kashin kansa, a’a wani abu ne dake bayyana ra’ayin Ma’asumi saboda shigarsa cikin Ijma’in. Al’umma ba ta iya zama ma’asumiya don dacewarta a kan wani abu, illa dai shigan Ma’asumi cikin dacewar ne ya inganta abin da ta dace a kai. Wannan ne yasa wasu ke ganin babu wani abu wai shi “Ijma’i” a hanyar daukar hukunce hukunce a Shi’a; da cewa abin da ake kira Ijma’i bai wuce wata hanya ta sanin Sunna ba.

4- Hankali: Shima daya ne daga wuraren da ’yan Shi’a suka yi hannun riga da bangarorin Ahlusunna a wannan fannin. Wannan na nufin akwai hukunce hukuncen da suna nan a Shari’a amma masdarinsu na farko shi ne hankali. Kamar abin da ya shafi hikimomin shari’anta shari’a (al-Milakat ko Falsafatul-Ahkam) da abubuwan da hukunce hukunce ke lizimtawa (Lawazimul-Ahkam) kamar bahasin Mukaddimatul-Wjib dake cikin Usul al-Fiqh, misalin dalilin aiwatar da abubuwan da suka zama dole don tafiya Hajji ga wanda ya sami iko, na daga yin fasgo, da neman Biza da sayen Tikitin Jirgi da sauransu. Duk wadannan hankali ke hukunta su a karkashin “Wajibcin samar da mukaddimar aikin da ya zama wajibi a Shari’a.” Misali da mai bawa zai hori bawansa da ya debo dawa a rumbu. Sai ya ki debowa, sai mai gidansa ya yi masa ukuba. Da masu hankali suka tambayi dalili sai bawa ya ce musu “ai bai ce na nemi tsani ba”! Da masu hankali sun hukunta cewa ya cancanci ukuba bisa dalilin cewa “ai horon debo dawa a runbu ya kunshi horo da amfani da tsani a matsayinsa na mukaddimar dole na yiwuwar aikin.” A takaice a irin wadannan ne hankali ke zama masdarin daukar hukunci a Musulunci bisa fahimtar Shi’a

A lokacin kokarin fitar da hukunci ta wadannan hanyoyin, Faqihi, a matsayinsa na wanda ba Ma’asumi ba, yana iya isa zuwa ga yakini ko ya saura cikin taraddudi. A nan menene mafita? Shin akwai wani tanaji da Shari’a ta yi don wannan ko a’a? Ba shakka Shari’a ta tanaji mafita, ta hanyar samar da wasu hanyoyi da ka’idoji da Mujtahid bi wajen zai dora mukallidai a kan abin da zai kubutar da su, ya haifar musu da yakini kan cewa sun sauke abin da ya hau kansu na Shari’a. Hankali ma ya dace da Shari’a a kan wajibcin samar da irin wannan hanya.

Kamar yadda ilimin Usulul-Fikihi ke koya mana bangaren farko da bayani a gabata a kansa, wanda kuma ake kira da Usul al-Istimbatiyyah, a matsayin nagartattun hanyoyin fitar da hukunce hukuncen dake da bayyanannun nassosi (al-Ahkam al-Waki’iyyah), haka nan yake koya mana hanyar kykkyawan amfani da wadannan ka’idoji na bangare na biyu da ake kira da al-Usul al-Amaliyyah ko wadanda guda hudu ne kamar haka:

1- Al-Bara’a: Shi ne yanayin da zai dora mukallafi a matsayin da zai kubutar da shi daga nauyin da ya hau kansa na Shari’a, wanda kuma aka kasa samun hukuncinsa a daya daga asasan nan hudu na Usul al-Istimbatiyyah. Misali mutumin da ake bi bashin wani adadi na sallah da bai fayyace ba, amma ya san dai bai kasa na lokaci kaza ba (kamar shekara biyu), amma ta iya yiwuwa ya wuce haka. A irin wannan hali adadin sallar shekara biyu shi ne abin da zai kubutar da shi daga bashin sallar da ake binsa. Idan ya yi ya kubuta daga nauyin Shari’a da ya hau kansa.

2- Al-Istishab: Shi ne yanayin dake ba mutum daman ginuwa a kan yakinin da ya gabata a lokacin da shakka ya biyo bayansa. Misali idan mutum ya san wancan ruwan yana da tsarki, bayan wani lokaci sai ya yi shakka kan ko yana nan a bisa tsarkinsa ko wani abu ya najasta shi? A nan zai hukunta masa halinsa na farko –tsarki- ya yi watsi da shakkan da ya zo daga baya. Saboda babu inda shakka ke iya warware yakini.

3- Al-Takhyir: Shi ne halin da mutum zai zama bisa zabi, ta yadda zai zabi daya daga hanyoyin da kowacce daga cikinsu tana iya zama hanyar aiwatar da bukatar Shari’a a lokacin da fifita daya daga cikinsu ta dalilan hukuncin al-Waki’i ya ta’azzara. Misali a lokacin da muke shakkar nauyin da ya hau kanmu a tsakanin Juma’a da Azahar a ranar juma’a a lokacin Gaibatul-Kubrah. A nan sai ya zama mukallafi yana da zabi tsakanin yin sallar Juma’a ko Azuhur, duk wadda ya yi ya wadatar.

4- Al-Ihtiyat: Shi ne halin da mukallafi ke daukar matsayin da zai tabbatar masa da sauke nauyin Shari’a. Misalin kwalabe biyu dake gaban mu, muna da tabbas cewa daya daga cikinsu giya ce daya kuma ba giya ba ce, amma ba mu san wacce ce giyar ba kuma wacce ce ba giyar ba. A nan Ihtiyadi na hukunta guje wa duk kwalaben biyu. A wani lokaci Ihtiyadi na iya bukatar maimaita aiki, kamar a inda muke shakka tsakanin cika sallah da kasaru ta fuskar rashin sanin hukuncin ko muta’allikinsa (kamar nisan tafiya), a nan sai mu yi Sallah da sigogin biyu: mu yi daya kasaru, daya kuma cikakkiya.

Idan wadannan suka bayyana, za mu fahimci cewa a shugabancin Marja’i ma yiwuwar kuskure na da nisa, saboda yana aiki ne da kwakwalwar Ma’asumi. Ko ta halin kaka dai, idan duk da haka aka sami wata kafa da kuskure ya samu –bayan daukar duk matakai da cikan dukkan sharudda- sai ka’idar “Kuma babu laifi a kanku bisa abin da kuka yi kuskure a kansa” da ta zo a fadar Allah Madaukaki mai cewa: “…Kuma babu laifi a kanku bisa abin da kuka yi kuskure a kansa, sai dai (kuna da laifi) a kan abin da zukatanku suka ganganta. Allah Ya kasance Mai gafara da jinkai.” (al-Ahzab 33:5); da ka’idar: “Ya Ubangijinmu kar Ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure…” da ta zo a aya ta 286 ta cikin surar Bakara, su yi aikin su. Wato sai uzuri ya samu tsakanin shi Mujtahidin da mukallidin.

 

Last modified on

37 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel