RAAF Official Website

A+ A A-

Makarantar Imam Husaini (a.s) Na 1

Rate this item
(0 votes)

Makarantar  Imam Husaini bn Ali (a.s): Na 1


Daga:
Sheikh Saleh Zaria
This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Wannan makala ce a kan wasu darussa daga yunkurin Imam Hussain (A.S). malamai sun bayar da mahimmaci a kan wannan bangare na nazarin yunkurin Imam Hussain (A.S) da kyau, ta dukkan bangarori, saboda dalilai biyu na asasi. Na daya saboda kar wadannan darussa su faku ga mutane, sai su kasa isa zuwa ga manufofin Imam (A.S). Na biyu saboda kar su rika akasta amfana da wannan yunkuri mai albarka ta hanyar ajiye abubuwa ba a mahallinsu ba. A duk surorin biyu sai su yi hannun riga da Imam Hussain (A.S) ba tare da sun lura ba.

Da farko yana da kyau a fahimci cewa Ahlul-bait (A.S) duk abu daya ne. 'Ya'yan babban bishiyar nan ce ta Sakon Allah, wadda da ta yi rassa a tarihin dan Adam tun farkon duniya, ta yadu ta hanyar Annabawa (AS), ta bunkasa a kan Manzo (SAWA) da mataimakinsa Imam Ali (AS), sannan ta fitar da nunannun 'ya'ya su ne tsarkakan Imamai daga Ahlul-baiti (AS). Imamai (AS) wanzajjen hasken Allah ne a doron kasa, masu haskaka duniya da samuwarsu. Don haka ko da Imami bai ce uffan ba a cikin al'umma, samuwarsa kawai hujja ce ga talikai; "Ba don Hujja ba da an shafe kasa da abin da ke cikin ta" (Hadisi).

Don bayanin wannan hakika ne ma daya daga cikinsu (Imam Ali A.S) yake cewa: "Su (Ahlul-Baiti) ne rayuwar ilimi, kuma mutuwar jahilci, hakurinsu na ba ku labarin iliminsu, zahirinsu na nuna muku abin da suka boye, shirunsu na gaya muku hukuncin zancensu. Ba sa sabawa gaskiya kuma basa sabani a kan ta. Su ne turakun Musulunci, kuma madafa. Da su gaskiya ta dawo mazauninta, bata kuma ya kau daga wajensa….." har zuwa inda yake cewa: "Sun fahimci addini fahimtar lura da wayewa, ba kawai ji da hakaitowa ba. Domin masu haiakto ilimi suna da yawa alhali masu wayewa da shi sun karanta." (Nahjul-Balagha).

Daga abin da ya gabata za a iya fahimtar cewa a tushe babu wani bambanci a kan ayyukan Imamai (AS). A asasi shirun Imam Ali da kyaliyarsa a lokacin Khalifofin nan uku na farko daidai yake da yakokinsa da Mu'awuya, da Dalha/Zubair/A'ishat, da Khawarijawa a Siffen, da Jamal da Nahairwan. Duk wadancan kuma basu da bambanci da sulhun Imam Hassan (AS) da Mu'awuya, da fito-na-fiton Imam Hussai da Yazid. Duk wadancan kuma ba su da wani sabani na asasi da hanyar tarbiyyar ruhi da Imam Zainul-Abidin (AS) ya bi, da hanyoyin yada ilimi da da fitar da malamai da Imam al-Baqir (AS) da Imam al-Sadiq (AS) suka bi. Da wannan kiyasta duk hanyoyin Imamanmu masu albarka, irin hanyar Imam al-Kazim (AS) na aikin asiri, da hanyar Imam al-Ridha (AS) na lalama da "shiga a gyara", da hanyar Imam al-Jawad (AS) ta munazara da muhawarar akida da mulhidai masu jayayya da samuwar Allah…. Kai! Har fakuwar Imam al-Asr (AF). Dukkanin wadannan uslubobi suna fadada hanyoyin da'awa ne da Manzo (SAWA) ya fare su. Sabanin kawai na usulubi ne, wanda yanayi ke tilasta irin wanda ya zama dole a bi. Wato kowanensu a shirye yake ya bi hanyar da kowannen ya bi idan yanayinsa ya bukaci haka. (Don cikakken bayani a kan haka duba littafin Sayyin Sadar na Ahlul-Bait: Tanawwu'ul-Adwaar Wa Wahadatul-Hadaf).

Hukuncin Allah da hikimarSa sun hukunta zabawa Imam Hussaini mafi wahalar hanya da ta bambanta da ta sauran Imamai (AS). Hanyar da ta bukaci sadaukar da 'ya'ya da dangi, da mikawa mutuwa zababbun makusanta da masoya, da shahada ta mafi wahalar hanya tattare da wahlahlu da masifu. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa Manzo ya kebe kulawa ta masamman ga Imam Hussaini (AS).

An riwaito cewa a ranar da aka haifi Imam Hussain (wanda ya dace da ranar 3 ga watan Sha'aban, shekaru uku bayan hijira), Manzon Allah (SAWA) ya tarbe shi da dariya da kuka a hade! Sai Asama'u ta tambaye shi dalilin kukansa cikin mamaki, sai y ace mata: "Azzalumar kungiyar nan za ta kashe shi a baya na, kar Allah Ya hada su da cetona." (Bihar al-Anwar).

E' dariyarsa (SAWA) ta murnar haifar masa wannan jika mai albarka ne. kukansa kuwa, na wahalhalun da zai shiga ne; in ka so ka ce, na tsanantar hanyar aikinsa ne!! Don haka ne ma muke cewa ai Manzo ne farkon wanda ya fara kuka da nuna tausayin Imam Hussaini bisa abin da zai same shi a Karbala. Bayani na zuwa nan gaba a kan haka.

Don haka a yunkurin Imam Hussain a kwai darasin kuka da tausasa zuciya. Wannan shi ne abin da zan yi magana a kai nan gaba insha'Allah.

Allah Ya sada mu da alheri.

 Bissalam

Saleh Zaria

 

 

 

Last modified on

23 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel