RAAF Official Website

A+ A A-

Sheik Bashir Lawal Ya Ci Gaba Da Raddi Wa Littafin Shubuhohin Shi'a A Mahangar Shari'a

Rate this item
(4 votes)

A ranar Talata 26/11/2013, ne Sheikh Bashir Lawal Kano, ya dora a kan Raddin da yake yiwa wadansu JIGAJIGAN malaman Izala su hudu (4) wadanda suka hadu karkashin wani jigo daga cikinsu, suka rubuta wani Littafi mai suna (SHUBUHOHIN SHI'A a MAHANGAR SHARI'AH).

Ga malaman da suka hadu wajan rubuta littafin:-
1. Sheikh Abdulwahab bn Abdallah bn Muhammad
Imam Ahlussunati waljama'a
2. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kwamanda Janar
na Hisba
3. Dr Ahmad Murtala na sashin nazarin addinin
muslunci a Jami'ar Bayero Kano
4. Sai mutumin da Littafin ya bayyana da sunansa,
wai shi : Abu Abdullah Hamza Uba Abubakar
Kabawa.
Ga duk mai bibiyan al'amuran kungiyoyin addini a Kano ya san wadancan guda ukun na farko, kana sun kasance MARAJ'U kuma MADOGARA ga kusan duk wani dan Izala da yake Kano, don da an fade su to za ka ga Magana ta kare. Amma duk da haka abin mamaki da takaici sai ga shi wai acikin littafin da bai wuce shafi 248 ba, suke jin cewa wai sun gama da Shi'a don abin kunya. Kuma wani abin sha'awa 'yan uwa sai suka yiwa littafin babi goma sha biyu (12) adadin Imamanmu cikin ma'asumai (14) da muke da su cikin wannan addinin namu na musulunci. Kana kowane malami daga cikinsu ya bada shawarar yadda ya kamata ayi amfani da wannan littafi na su, misali:-Wani daga cikinsu ya bayar da shawara tare da rokon hukuma da ta sanya shi a manhajar makarantu sabo da yara su san yadda 'yan shi'a suke da  shubuhohi akan wadannan hadisai Ingantattu.
Haka ma Wani malamin ya ce ya kamata a fassara shi zuwa sauti saboda ma su gandar karatu, kamar
a memory, CD, DVD. Da dai sauransu, Alhamdu lillah, kamar yadda na fada a baya shi ma
SHEIKH BASHIR LAWAL KANO a yanzu haka ya yi nisa wajan mai da martini na ILIMI, da BAHASI mai
fadi da fito da dalilai gamsassu daga cikin littattafan Ahlussuna da Alqur'ani mai girma, don gamsar da mai sauraro, ko mai kanllo ta faifan DVD, ta yadda duk abin da aka fada za a nuna maka littafin don ka koma ka duba da kan ka.
Kuma abin sha'awa sai suka tsara littafin na su Fasali-fasali har goma sha biyu (12) wato adadin Halifofin manzon Allah (s.a.w.a) guda goma shabiyu (12) daga cikin Ma'asumai goma sha hudu (14) da muke da su a cikin wannan addini na muna musulunci.
Kamar yadda muka fada cewa malam ya yi nisa wajan wannan hidima ta kare wannan addinin na musulunci da Annabinmu, don haka a fasali nafarko mai taken:-
SHUBUHOHIN SHI'A A KAN HADISIN HALIFOFI GOMA SHA BIYU(12), TARE DA WAR-WARESU DA
DALILAI INGANTATTU.
In da malam ya yi sama da talatin (30), a kan wannan FASALI. Kuma insha'allahu kowane Fasili za a mayar da shi littafi mai zaman kansa, kuma mu ma muna rokon Gwamnati da ta sanya littattafan na mu a tsarin manhajar makarantu, kamar yadda 'yan uwanma suka nemi a saka na su littafin a manhajar makaranta.
Kana a ranar talata 26/11/2013, malam ya dora BAHASINSA a kan FASALI na biyu (2), mai taken:-SHUBUHOHIN SHI'A A KAN HADISIN SAYYADINA UMAR (R.A) NA BADA SHAWARAR HANA RUBUTA
TAKARDA LOKACIN RASHIN LAFIYAR MANZON ALLAH (s.a.w.a.) DA WAR-WARESU DA DALILAI
GAMSASSU.
Kuma dukkanin wadannan darussa suna nan suna shiga hannun jama'a, kuma su jama'ar za su yi
alkalanci, lokacin da suka ji abinda ku salafawa kuka fada, da kuma abin dam u shi'a muka fahimta, da abin da kuke cewa shubuha a ciki wadannan Hadisan da ku kanku kuka ce ingantattu ne.
In sha'allahu za mu ci gaba dad an gutsuro muku kadan daga cikin abin da yake faruwa a majalisin
da ake gabatarwa a MASALLACIN RASULUL A'AZAM dake Dawanau a Birnin Kano.

 

Last modified on

49 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel