RAAF Official Website

A+ A A-

Shugabannin Cibiyar Rasulul A'azam Sun Kai Wa Sheikh Turi Ziyara

Rate this item
(6 votes)

A yau Alhamis 08/02/1434 hijiriyya, (12/12/2013 miladiyya) Shugabannin Rasulul A'azam Foundation (RAAF), tare da wadansu daga cikin dalibansu suka kai ziyara ta musamman ga wakilin shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya kuma shugaban 'yan uwa na harkar reshen jihar Kano, Sheikh Muhammad Mahmud Turi, a gidansa da ke Unguwar Goron Dutse a birnin Kano.

Wannan ziyara mai al-barka ta gudana ne karkashin jagoranci Shugaban Cibiyar Rasulul A'azam din ta kasa, Hujjatul Islam wal muslimin Sheikh Muhammad Nur Dass inda aka tattauna muhimman abubuwa da suka shafi hadin kai da kusantar juna.

 

A cikin tattaunawar da wadannan manyan malamai suka yi a farfajiyar Hussainiyyar MARKAZ din, an tattauna yadda Shi'anci yake fadada a wannan lokaci, da ya kamata a amfana da wannan dama da kuma yanayi da Allah (s.w.t.) ya ba mu na riko da Ma’asumai goma sha hudu. 

 

Ba'abar gurinba sai da aka tabo maganar abin da ya shafi SOCIAL MEDIA a wannan lokaci kamar FACEBOOK, inda wadansu suke amfani da wannan shafi don cimma wata boyayyiyar manufa mara kyau da ganin sun rusa wannan MAZAHABA da mabiyanta, ta hanyar yada zantuttuka na banza, da karya da kazafi, don kawai su ci mutuncin wani, ko don su haddasi rikicin addini musamman a tsakanin mabiya mazahabar Ja'afariyya ('Yan Shi'a).

 

A nan ne Jagoran tawagar RASULUL A'AZAM FOUNDATION din Sheikh Muhammad Nur Dass ya kara bayyanawa Sheikh Muhammad Mahmud Turi cewa sun sami wani labari mara dadi da aka danganta shi ga Malam Ibrahim Zakzaky, kuma wai mai maganar yana danganta kansa da cibiyar Rasulul A’azam, inda Sheikh ya bayyana cewar: a hakikanin gaskiya mun barranta da wannan magana da kuma wanda ya yi ta da sunanmu. Mu ba ma tare da irin wannan kuma bamu yarda wani mutum ya fake da sunanmu ya ci mutunci wani mutum ba, ballantana mutum Irin Shiekh Ibrahim Zakzaky, wanda kowa yaga irin gudummawar da yake bayarwa wajan bunkasa wannan mazahaba da hadin kai.

A karshe shi ma Sheikh Muhammad Turi ya yaba da wannan ziyara da ya ambace ta da ziyarar kyautata alaka mai amfani wanda irinsa al’umma take bukata, kana ya yi alkawarin isar wa Sheikh Zakzaky da sakon wannan ziyarar da irin jajantawar da suka yi na rashin jin dadin wadannan kalmomi da wani ya fada a kansa, da kuma nisantarsu da irin wadannan abubuwa marasa kyau a tsakanin 'yan Shi'a baki daya.

Last modified on

24477 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel