RAAF Official Website

A+ A A-

Cibiyar Rasulul A'azam (s) Ta Gudanar Da Maulidi A Saminaka

Rate this item
(1 Vote)

A ranar Asabar 1/2/2014 makarantar Khairul-Bariyya, Sabuwar Hanyar Bauchi, Saminaka, Kaduna State wacce take karkashin Mu’assasar Rasulul A’azam ta gudanar da bikin Maulidin Manzon Allah (s).

Bikin dai ya sami halartar Malamai daga Mu'assasa da suka hada da Sheikh Nur Dass, shugaban Mu’assasar da kuma Sheikh  Saleh Zaria babban sakataren Mu’assasar. Sannan a bangaren manyan gari kuma sun hada da: 1-Uban Makaranta (shine) magajin garin Samina kuma sarkin Zamfarwa Alh. Sulaiman. 2-Sarkin sabon garin, wanda shi ne dagacin yankin da makarantar take. malam Yakubu Yahaya. 3-Sarkin Katirje Alh. Abba. 4-Limamin Katirje Mal. Umar. 5-Na'ibin limmamin Katirje Mal. Abdul-Qadir (wanda shi ne mahafin shugaban makaranta). 6-Sarkin Unguwar Makama mal. Mahmud Kiyaye.

Mahalarta daga daliban makarantar: Daliban makarantar Khairul-Bariyya daga cibiyoyinta dabam daban ne suka sami halartar wannan taro tare da iyayensu; misali daga kauyukan Tagwaye, Anguwar Yarima, Wagaho, 'Yan-Tama, Doka, Dan Alhaji, Unguwar Bawa, Ka yarda, Pambegua, Dandaura, Barwa, Anguwan Noma, Kogo, Sabon Kudi, Gadama, Katakau da sauransu.

An saurari karatuttuka daga daliban da aka yaye har na tsawon awa biyu, sannan an saurari wakokin yabo daga mawaka dabam daban irin su shugaban makarantar Mal. Auwal Saminaka da mal. Ibrahim Dabai. Sannan an gabatar da jawabai daga bakin Sheikh Nur Dass, wanda ya tunatar da masu sauraro janibin rayuwar Manzo (SAWA) da mahimmancin ilimi, da Sheikh Saleh Zaria wanda ya bayani kan rayuwar Imam al-Sadiq (AS) a matsayin halqar tsakiya na daya daga igiyoyin da Manzo (SAWA) ya barwa al'umma, wato ma'asuman da za su fassara addini da sahihin fassara. Haka nan Uban makaranta, magajin garin Saminaka Alh. Sulaiman ya yi jawabin godiya. Liman Mal. Umar da na'ibinsa mal. Abdul-Qadir duk sun gabatar da addu'o'i ga daliban da aka yaye da sauran mahalarta taro. Sarkin Sabon gari ma yayi jawabin maraba da baki. Shugaban makaranta kuwa, wato Mal. Auwal Saminaka, wanda shi ne kirjin biki, shi ya shugabanci taro.

Wannan taro dai yau kusan shekaru biyar kenan yana maimaitua, kuma a kowace shekara yana kara armashi ne.

A wajen taron an raba takardun sheda, inda Sheikh Nur Dass ya mika wa wasu dalibai maza, kuma Uban Makarntar, Sarkin Zamfarawa, Magajin Garin Saminaka ya mika takardun shedar ga dalibai mata.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

-

--

-

-

--

--

-

--

-

 

 

Last modified on

38 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel