RAAF Official Website

A+ A A-

An Gudanar Da Bikin Ghadir A Sokoto

Rate this item
(0 votes)

A anar Litinin 13 ga watan Oktoban Mu’assasar Rasulul A’azam (s.a.w.a) reshen jihar Sokoto ta gabatar da bikin Idin Ghadir na bana wanda aka gudanar a babban dakin taro na Pinnacles dake hanyar GRA Sokoto. Taron ya sa mu halartar mabiya Ahlul-Bait daga garin Sokoto da kewaye, tare da wakilai daga Talata Mafara, Yawuri da Gwadabawa. Haka wasu limaman Kirista guda biyu sun halarci gayyatar da aka yi musu. Wanda ya shugabanci taron shi ne Prof, Zaki na Jami'ar Sokoto, sannan wanda ya gabatar shi ne Abdurrahman Umar Matawaale, malami babbar kwalejin koyarwa ta Shehu Shagari dake Sokoto, sannan babban mai jawabi Shi ne Sheikh Saleh Zaria.

 

Jawabin taron ya kunshi takaitaccen bayani a kan lamarin Ghadir da ayar da ta umurci Manzo da nada Ali (AS) a matsain magajin Manzo (SAWA) da aiwatar da umarnin Allah da Manzo ya yi na daga hannun Ali kowa ya gan shi yana sanar da shi a matsayin shugaban al'umma a bayansa kamar yadda Manzo ya kasace a lokacin rayuwarsa, da saurkar ayar cikan addini da cikan ni'ima da wannan nadi.

 

Daga nan jawabin ya yi nazari gamme da wannan matsayi da Allah Ya yi horo da Manzo ya tabbatarwa Imam Ali da shi ta wannan siga, da cewa wani zango ne na shugabancin da Allah Ta'ala ya tanaje shi tun farkon halittar mutum; wannan shugabanci dake matayin amsa dabi'antacciyar bukatar mutum na a kama hannunsa wajen cimma kamalar da yake nema a rayuwa, kuma wadda ake rudar da shi da yawa a kanta, ta hanyar suranta masa kadancewar a yawan dukiya ko mulki ko mukami ko yawan 'ya'ya ko kyawawan mata da sauransu.

 

Bukatar shugabanci, inji mai babban mai jawabi, bukata ce babba kuma ta dabi'a ga mutum, don haka a ka ga yana bayyana ta a ko yaushe ya samu kansa a rayuwar zamantakewa a duk mataan rayuwarsa, babu bambanci tsakanin lokacin wayewarsa da rayuwar sa ta daji da kogo, hatta a lokacin da ya kasa fahimtar mahimmacin suturta al'aurarsa, ya fahimci mahimmacin shugabanci, Wannan ya nuna Allah Ya tanadar masa nagartaccen shugabanci da zi sadar da shi ga dukkan kamala. Wannan shi ne sugabancin Ma'asumai kai tsaye ko ta hanyar wakiltarwa.

 

A karshe mal. ya bayyana rashin yiwuwar yankewan wannan shugabanci matukar akwi mutum biyu a doron kasa, daya sai ya zama mai shiryar da daya zuwa ga hanyoyin kamalarsa da dacewarsa ta hakika. Wannan shi ne lazimin kasancewar Allah ALLAH (MAWADACI, MAI TAUSAYI KUMA MAI MANUFA DA HIKIMA A KAN HALITTARSA DA GUDANARWARSA) da zaman bawa BAWA  (MAI RAUNI KUMA MABUKACI YA ZUWA MAHALICCINSA KUWA MA'ABUCIN NI'IMARSA).

 

Doha imani da sakamakon Ghadir wannan ma'anar shi kadai ke hada mtuum da wannan shugabancin na mahaliccinsa. Idan kuwa aka kau da kai daga wannan, wannan yana nufin zama cikin dimuwa da rashin MARJA'IYYA RASHIDIYA wadda za ta zama lamunin daidaitar al'umma da kare t daga bin son zuciya da rarraba da rauni. Abin da k faruwa a duniyar Musulmi ta yau a kan halin wadanda suka yi da lamarin Ghadir da wannan siga, da wadanda suke daukan shi a babin falaloli (hakan) sheda ta fuskar tsari da shugabanci, sheda mai karfi a kan wannan hakika,

 

A taron shugaban Northern Christian E;ders Forum shiyyar Sokoto, Rev, Alka Mika'ilu Tara ya yi bayanin godiya da gayyatar da aka yi masa, da nuna gamsuwa da irin usulubin Mu'assasar  Raulul-A'azam wajen wa'azzuzzuka da kokarin samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da mazahabobi/

 

Daga shugabannin Kirista da ya halarci taron akwai Pastor Abubakar na Gwadabawa ECWA Church.

 

A nashi jawabin shugaban RAAF reshen Sokoto mal. Kabiru Danhili ya godewa mahalrta taron da bakin da suka amsa gayyatar su, masamman mabiya addinin Kirista,

Last modified on

57 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel