RAAF Official Website

A+ A A-

Sheikh Saleh Ya Gabatar Da Takarda A Kwamitin Rikicin Zaria A Madadin RAAF

Rate this item
(0 votes)

A yau Alhamis ne Cibiyar Rasulul A'azam (RAAF) da ke birnin Kano ta gabatar da takarda a gaban kwamitin da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa don binciko musabbabin rikicin da ya faru a Zaria, tsakanin sojoji da 'yan kungiyar Harkar Musulunci.

Babban sakataren kungiyar ta RAAF Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya ne ya gabatar da takardar a madadin shugaban kungiyar Sheikh Muhammad Nur Dass.

Ga kadan daga cikin abubuwan da Sheik Saleh ya fadi a wajen zaman:

Sheikh Ya bayyana cewa Gwagwarmaya Zakzaky ke yi kuma yaki yarda ya mayar da gwagwarmayarsa shi'a. Saboda haka su basa tare da shi'a. Suna shi'a ne Zalla.
Shugaba ya tambayeshi banbancin sunna da shi'a inda ya bayyana cewa imamanci.
Ya bayyana cewa kafin a fara sunna, Shi'a aka fara.
Shugaba ya tambayeshi banbancin MRA da IMN? Ya ce su sun yarda da dokokin Nijeriya kuma suna binsu. Sabanin IMN.
Ya bayyana cewa duk abubuwan da za su yi suna sanar da jami'an tsaro da kuma Gwamnati. Sannan sun gina masallacinsu don kauyewa rikici tsakaninsu da masu masallatai. Ya ce masallacin da su na Dawanau. Sannan suna da wani karamin masallaci a Hayin Malam Bello. Da kuma wani masallacin a Kwana huku Kano da sauransu.
Ya kuma bayyana rashin jin dadinsa game da wadanda suka gabatar da takardun suka nemi a hana Shi'a a Nijeriya gaba daya. Ya ce wannan ya sabawa tsarin mulkin Nijeriya wanda ya baiwa kowa daman yin addininsa matukar bai ci mutuncin wani ba.
Ya bayyana cewa IMN ta yi amfani da karfi a kansu don hanasu abin da suke yi amma ba su yi nasara ba.
Lauyan Soji ya tambayeshi me ya karanta a Iran? Ya ce geology
Point of correction 
Theology ne ba geology ba
Lauyan Soji sun tambayeshi ko yana goyon bayan rufe hanya? Ya ce A'a. Amma yana Allah wadai da kisan da sojoji suka je Gyallesu da darur Rahma suka yi.
Ko ya yarda da auren Mutu'a? Ya ce eh ya yarda da shi.
Ko ya yarda da Qudus day? Ya ce eh ya yarda da ita.
Ko ya taba ganin Zakzaky? Ya ce eh har sau hudu.
Ko ya amince da Zakzaky ya kawo Shi'a a Nijeriya? Ya ce haka ake cewa.
Ko akwai wata kungiya wadda ita ce ke jagiranta duk 'yan Shi'a a Nijeriya? Ya ce babu.
Amma suna nan suna kokarin hada kungiyar har sun tuntubi Zakzaky.
Ya tambayeshi kungiyoyin shi'a nawa ne a Nijeriya? Ya ce bai sani ba. Sai Lauya ya ce masa ga taku ga kuma ta Zakzaky. Sai ya ce zakzaky Movement ne ba shi'a ba.
Ya tambayeshi ko a ina suke samun kudi? Ya ce su suke hada kudinsu. Kuma za a ga wannan a tsarin mulkinsu da suka bai wa JCI.
Lauyan Soji ya tambayeshi ko suna da makaranta? Ya ce eh suna da ita. Ya ce wane tsarin koyarwa suke amfani da shi, na Nijeriya ko na Iran? Sai ya ce ai makarantarsu ba ta Boko bace.
Lauyan JNI ya tambayeshi ya tambayeshi ko matan Annabi na iya yin sabo? Ya ce Eh, za su iya yi.
Ko ya amince cewa Hizbullahi 'yan Shi'a ne? Ya ce Eh. Ko zai yarda cewa 'yan ta'adda ne? Ya ce ba 'yan ta'adda bane.
Amma ya ce zakzaky na nesa basa iya zuwa wajensa.
Lauyan JTI ya tambayeshi ko Annabi dan shi'a ne? Ya ce A'a.
Ya kuma kara tambayarsa cewa tunda ya soke rufe hanya ko zai iya sanar da mutanen Zakzaky cewa wannan abu da suke yi ba daidai bane? Ya ce eh zai iya.
Ya kuma tambayeshi ko zai yi bayanin taqiyya? Ya ce wata abu be da Alkur'ani ya yi magana a kanta. Wadda mutum ke yi lokacin da yake tsoron faruwar wani abu a kansa.
Ko yana goyon bayan jawabin da Zakzaky ya yi na cewa wasu sahabbai sun gudu ranar Uhudu da badar? Ya ce bai ga wannan ba amma idan ya ci mutuncin Sahabbai to wannan ya sabawa koyarwar Shi'a.
Me zai ce game da Shehu Usman da Abdullahi Fodiyo da Muhammad Bello? Ya ce yana girmamasu sosai.
Ya ce Babansa ne ke daukarwa Shaikh Gumi littattafai, saboda haka babansa dan Izala ne kuma mahaifiyarsa cikakkiyar yan Tijjaniyya ne, kuma shi dan Shi'a ne. Saboda haka ba bu dalilin da zai soki wani.

Last modified on

3 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel