RAAF Official Website

A+ A A-

A ci gaba da gudanar da tarurrukan juyayin Ashura a Husainiyar makarantar hauzar Bakirul Ulum da ke karkashin Mu'assasar Rasulul A'azam (s) da ke karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Nur Dass, a yammacin yau ne aka gudanar da taron ranar farko ta juyayin shahadar Imam Husaini (a.s) inda Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria ya gabatar da jawabi a wajen taron.

A lokacin jawabin nasa Sheikh Saleh Zaria yayi bayani dangane da dalilan yunkurin Imam Husain da kuma fitarsa zuwa Karbala.

 

 

 

 

Read more... 57

An gama dukkanin shirye-shiryen tarbar watan Muharram, watan da jini ya yi nasara a kan takobi, watan da jikan Manzon Allah (s) Imam Husaini (a.s) da iyalansa da sahabbansa suka sadaukar da rayukansu waje kare addinin Musulunci daga kokarin gurbata shi da Banu Umayya suka yi, a Husainiyar Hauzar Bakirul Ulum da ke Dambare.

Kamar yadda aka saba kowace shekara, an lullube Husainiyar da bangarori daban-daban na makarantar da ke nuni da alamar shigowar watan na Muharram.

Ga wasu daga cikin hotunan 'yan'uwa a lokacin da suke gudanar da ayyukan sanya bakaken kyalle a Husainiyar:

 

 

 

 

 

 

Read more... 36

Kamar yadda ta saba, Mu'assasar Rasulul A'azam da ke da helkwata a garin Kano, Nijeriya ta gudanar da bukukuwan Idin Ghadir, ranar da  Manzon Allah (s) ya nada da kuma zaban Amirul Muminin Ali bn Abi Talib (a.s) a matsayin halifa kuma imamanin musulmi a bayansa kai tsaye, a garin Sokoto da ke jihar Sokoto wanda a babban dakin taro na Pinnacles dake hanyar GRA Sokoto.

Taron ya sa mu halartar mabiya Ahlul-Bait daga garin Sokoto da kewaye, tare da wakilai daga Talata Mafara, Yawuri da Gwadabawa. Haka wasu limaman Kirista guda biyu sun halarci gayyatar da aka yi musu. Wanda ya shugabanci taron shi ne Prof, Zaki na Jami'ar Sokoto, sannan wanda ya gabatar shi ne Abdurrahman Umar Matawaale, malami babbar kwalejin koyarwa ta Shehu Shagari dake Sokoto, sannan babban mai jawabi Shi ne Sheikh Saleh Zaria.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Read more... 37

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel