RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

A Ranar lahadin nan 5/5/13 Mu'assar Rasulul A'zam ta gudanar da mauludin Sayyida Zahara (AS), wanda ya samu halartar daruruwan jama'a daga dalibanta da sauran masoya Ahlul-Bayt (AS), mazansu da matansu da yaransu.

Published in Latest

A kokarin da take yi na ci gaba da wayar da kan al'umma da ilimantar da su Mu'assasar Rasulul Aazam (RAAF) da ke birnin Kano ta kaddamar da wani sabon littafi mai suna "Raddin Shubuhohi A kan Ghadir Da Nassosin Imamancin Ahlulbaiti (a.s)" wanda Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria ya wallafa.

Published in Latest

Bisa la'akari da muhimmancin aikin hajji a matsayinsa na daya daga cikin rassan addinin Musulunci, Mu'assasar Rasulul A'azam (s) ta fassara da kaddamar da littafin 'Manasik al-Hajj - Ayyukan Hajji -' wallafar Jagoran musulmi Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Al-Husaini Al-Khamene'i (Allah Ya Ja Kwanansa)".

Littafin dai Malam Abdullahi Hasan (Shazi) ne ya fassara shi daga harshen Larabci zuwa Hausa da taimako da sanya idon Sheikh Muhammad Nur Dass da Sheikh Bashir Lawal Zaria.  

 

Littafin ya kasu kashi uku tare da gabatarwa.  

 

Kashi na daya kan Hajjil-Islam (wato aikin hajjin farko ga Musulmi) da yadda ake yinsa.  

 

Kashi na biyu Kan Ayyukan Umrar Hajji da ayyukan da suka jimance shi.

Sai kashi na uku kan Ayuukan hajji dabam dabam, wato abubuwan da suka wajaba da wadanda suka zama mustahabbai a kan mahajjaci; gami da abubuwan da suka wajaba ya gujewa don kubutar da aikin hajjinsa. Duk cikin kalmomi masu saukin fahimta.

Published in Latest

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel