RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

An Gudanar Da Bukin Juyayin Wafatin Imam Khumaini (r.a)A Bauchi Featured

Rate this item
(3 votes)

 

A ranar asabar 3 ga watan Yunin nan ne aka gudanar da gagarumin bukin juyayi shekaru goma sha bakwai da rasuwar Mu'assasin juyin juya halin Musulunci marigayi Imam Khumaini (r.a) a babban dakin taro na NUT da ke garin Bauchi don tuntuni kan irin dabi'u da halayen marigayin.

 

Taron dai ya samu halartar darurrukan masoya Imam din wadanda suka taru don nuna juyayi da kuma sauraren jawabin da malaman da aka gayyata za su gabatar a wajen taron.

Daga cikin manyan malamai da bakin da suka halarci taron har da Sheikh Muhammad Nura Dass, Sheikh Bashir Lawal, Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria daga Kano, sai kuma Malam Garba Sokoto (Tudun Wada) wani babban malamin darika kadiriyya a garin Gomben da dai sauran manyan baki da aka gayyata daga garin Gomben da kewaye.

A yayin da yake gabatar da jawabinsa, babban bako mai jawabi a wajen taron Sheikh Muhammad Nura Dass ya yi bayani ne kan matsayin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, da kuma irin darussan da za a iya koya daga rayuwar Ma'aikin (s).

Shi ma a nasa bangaren Malam Garba Sokoto (Tudun Wada) ya yi magana ne Iyalan Ma'aiki (s) da mu'ujizozin Imam Ali (a.s).

 

Baya ga lakcoci da jawaban da aka gudanar a wajen bukin, har ila yau kuma mawaka da masu yabon Annabi ma ba a barsu a baya ba inda suka kawata wajen da fasahar da Allah Ya yi musu na wake. A wajen bukin dai fitaccen mawakin nan Mustafa Gadon Kaya ya rera wakokin yabon Ma'aiki (s)

Last modified on

81 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel