RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

Mu'assasa Ta Kaddamar Da Littafi Mai Suna "Raddin Shubhohi A Kan Ghadir Featured

Rate this item
(2 votes)
Littafin Raddin Shubuhohi Kan Ghadir Littafin Raddin Shubuhohi Kan Ghadir

A kokarin da take yi na ci gaba da wayar da kan al'umma da ilimantar da su Mu'assasar Rasulul Aazam (RAAF) da ke birnin Kano ta kaddamar da wani sabon littafi mai suna "Raddin Shubuhohi A kan Ghadir Da Nassosin Imamancin Ahlulbaiti (a.s)" wanda Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria ya wallafa.

 

Asalin littafin raddi ne a kan irin shubuhohin da Wahabiyawa suke tayarwa a kan nassosin Ghadir da matsayin Ahlul-bait (amincin Allah ya tabbata a gare su) a cikin wannan al'umma.

Littafin ya kunshi gabatarwa, da bayani a kan nassosin Musulunci (na AlKur'ani da Hadisai) wadanda suka shafi Ghadir. Sai kuma abubuwan da suka faru a Ghadir ta fuskokin tarihi da hadisai. Daga nan sai auna zantukan malaman Musulmi kan wannan babban al'amari tare da bayyana littafan Ahlussunna da suka fitar da haka.

Akwai bayanin yadda nassosin Ghadir (tare da dukkanin nassosin Musulunci da suka yi magana kan Alhlul-bait (AS) da matsayinsu) suka fuskanta da yadda Musulmi na zamuna dabam dabam suka yi mu'amala da su -tsakanin wadanda suka ji kuma suka fahimta sannan suka yi biyayya; da wadanda suka ji suka nuna ba su ma fahimta ba, sai kuma wadanda suka karkatar da ma'anoninsu don biyan bukatunsu. Haka nan akwai sassarfa kan abin da ya biyo bayan wafatin Ma'aiki da fahimtar 'yan Shi'a da abin da ya faru din, da kuma matsayinsu a kan haka.

Last modified on

12 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel