RAAF Official Website

Error
  • JUser: :_load: Unable to load user with ID: 42
A+ A A-

Mu'assasar Rasulul A'azam Ta Gudanar Da Maulidin Fatima al-Zahra (a.s) A Kano Featured

Rate this item
(5 votes)
Malamai A Wajen Taron Maulidin Malamai A Wajen Taron Maulidin

A Ranar lahadin nan 5/5/13 Mu'assar Rasulul A'zam ta gudanar da mauludin Sayyida Zahara (AS), wanda ya samu halartar daruruwan jama'a daga dalibanta da sauran masoya Ahlul-Bayt (AS), mazansu da matansu da yaransu.

 

Babban mai jawabi, Sheikh Bashir Lawal, ya tabo sassa masu yawa na rayuwar Sayyida Zahra (AS), da yadda ta zaman abin kyin maza damata, bias asasin kasancewarta tsattsarka kuma tsaikon tsarki kamar yadda AlKur'ani da ingantattun hadisai suka tabbatar. Malamin ya nuna takaicin yadda a wasu lokuta ake samun rauni dada wajen wani na sashin Musulmi ta fuskar mu'amala da Fatima da sigar da ya kamata, wanda hakan ke samo asali daga abubuwan da Ummayawa suka kirkira suka cusa a akidar musulmi na fifita wasu a kan tsarkakan jikokin Ma'aiki (SAWA). 

 

Daga nan kuma sai jawabin maraba da baki wanda Sheikh Bashir Lawal, mukaddashin shugaban Mu'assasar ya gabatar. 

 

Sauran wadanda suka gabatar da laccoci a taron sun hada da Sharif Shibli, wanda ya yi ta'akidi a kan fifikon Fatima da kasancewarta tsaikon tawassuli a cikin addu'ar da Imamai suka karantar da mabiyansu ma cewa: "Allah, da hakkin Fatma da babanta; da mijinta da 'ya'yanta; da sirrin da aka adana a tare da ita...." Sharif ya yi ishara da munafuncin da wasu masu riwayawar hadisi suka siffantu da shi na jona duk wata daraja ta tsarkakan Ahlul-Bait (AS) da abin da ke gurbata shi a ruwayoyinsu. 

 

A karshe Shekh Saleh Zariya ya yi jawabin karshe, inda ya yi takaitaccen bayani a kan taron da ya halarta dangane da fadakar musulmi dake fadada a duniyar Musulunci da nauyin da ya hau kan malamai dangane da haka. Ya nakalto wani sashe na jawabin ja-goran juyin Musulunci a Iran Ayatollahil-Uzma Sayyid Ali Khami'nae, wanda ya kira malamai da su sauke nayin da ya hau kansu na jagorancin wannan bukata da kishirwar 'yanci dake bayyana daga al'ummar Musulmi. Malamin ya yi ta ishara da kiran ja-goran na kulawa sosai da sabuwar dasisar makiya na tayar da sabanin Shi'a-Sunna don karkatar da akalar wannan yunkuri na alheri; don haka jagoran ya kira malamai da kar su ji tsoron komai saboda nasara ta su ce matukar sun ci gaba da tafiya a tafarkin kawo gyara. 

An gudanar da wannan taro ne a dakin taron Hauzar Baqirul-Ulum dake Danbare, Kano

Last modified on

79 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel