Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ya bude wannan taron inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewar riko da koyarwar Musulunci da kuma kasantuwa a fage a matsayin wasu abubuwa guda biyu masu muhimmanci wajen kawo karshen makirce-makircen makiya a kan al'ummar musulmi.
Yayin da ya ke ishara da bayyana wajibcin kiyaye matsayi na addini, shata manufar da ake son cimmawa, nesantar sanya fata cikin alkawurran kasashen yammaci da kuma makirce-makircen da suke kullawa wajen haifar da rikici na kabilanci da mazhaba da kuma rashin yin watsi da matsalar al'ummar Palastinu a matsayin abubuwan da wajibi ne a ba su muhimmanci wajen tabbatar da irin farkawar da al'ummar musulmi suke samu.
Yayin da ya koma kan gagarumin nauyin da ke wuyan malaman Musulunci a wannan lokacin da al'ummar suka farka, Ayatullah Khamenei ya kirayi malaman da su taka tsantsan ainun a lokacin da suke sauke nauyin da ke wuyansu na shiryar da al'umma.
Kafin bude taron dai sai da Jagoran ya gana a kebe da wasu daga cikin manyan malaman da suka halarci taron. Daga cikin malaman da suka gana da Jagoran har da Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya.