RAAF Official Website

A+ A A-

Cibiyar Rasulul A'azam (s) Ta Gudanar Da Maulidi A Panbegua

Rate this item
(0 votes)

A ranar Juma'a, 31 ga watan Junairun shekrar 2014 Makarantar Khairul-Bariyya reshen Panbeguwa dake karamar hukumar Kauru a Kaduna State bisa jagorancin shugaban makarantar Mal.Auwal Abdu Saminaka, wadda kuma take karkashin Mu'assasar Rasulul- A'azam ta gudanar da bikin mauludin Manzo (SAWA) tare da yaye zangon farko na daliban makarantar.

 

Taron ya sami halartar manyan gari irin su Sarkin Tudunwadan Panbegua mal. Umar Alhassan dn Kansilan Dawaki ta karamar hukumar Kubau Alh. Saminu da sauran dattawan gari da malamai da suka sami halartar taron, kamar yadda kuma malaman da suka halarta su ne shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam Sheikh Nur Dass da Mal. Saleh Zaria, babban sakataren Mu’assasar.

 

An gabatar da karatuttukan AlKur'ani daga dalibai masu sauka maza da mata. Hakan an gabatar da laccocin Mauludin da hadin kan Musulmi da addu'o'in zaman laifiya a kasa da duniya baki daya.

 

A na shi jawabin, Mal. Saleh ya yi jawabi a kan wasu daga abubuwan da Manzo  (SAWA) ya karantar kuma ya dora al'umma a kai, masamman janibin ilimi da ilmantarwa bisa shaidar wasu ayoyi daga AlKur'ani da suka bayyana manufar aiko Annabi (SAWA) da tilawar ayoyin Allah ga mutane, da tsarkake zukatansu sannan da karantar da su.

 

Malam ya yi tsokaci mai sosa rai a kan ci bayan da al'ummar duniyar take fuskanta daga barazanar ilimin zamani da ba dora shi a kan imani da addini na gaskiya ba, inda manyan kasashen duniya da suka mallaki wayewar ilimin zamani da kimiyya da fasaha suka karkata duk iliminsu da fasahar zuwa yada fasadi da kafircewa Allah a duniya. Wanda ya fi wannan ban haushi -in ji malamin - shi ne irin mummunan ci bayan da al'ummar mu ta musulmi take shaidawa a yau a sakamakon sakaci da fadada ilimi ta dukkan fuskokin na addinii da na zamani, alhali babu addinin da ya gina mutanensa a kan ilimi irin Musulunci, sannan babu shugaban da ya dora mabiyansa a kan turbar iliimi kamar yadda Manzon Tsira (SAWA) ya dora al'ummar Musulmi.

 

A karshe malam ya bayyana cewa matukar ba samar da daidaiicin hada imani da addinin gaskiya tare da ilimi ba, to duniya ba za ta shaida zaman lafiya da adalci ba, kuma amatukar al'ummar musulmi suka ci gaba da yiwa imummuka rikon sakainar-kashi, ba za su taba cimma dogaro da kai da samun cikakken 'yanci a rayuwarsu ta duniya ba, sannan ba za su taba bautaa Allah daidai ba sai da nagartaccen ilimin ba irin kalkalar zamani ba.

 

 

Sheikh Nur Dass kuwa ya yi takaitaccen bayanin godiya ne a wajen taron, inda ya karfafa gwiwar daliban da aka yaye da cewa wannan wani mataki ne na kara kaimi don ilimi yana da fadi. Sannan ya jinjinawa shugaban makaranta da malaman ta a kan himmarsu wajen koyar da daliban da tarbiyyantar da su. Ya kuma yabawa iyayen yara da himmar da suke bayarwa ga ilmin 'ya'yansu, tare da kwadaitar da su a kan ci gaba da haka. A karshe mallam ya yabawa shugabannin al'umma, masamman sarkin tundunwada kansilan Dawaki a kan goyon baya da suke ba makaranta, ya kuma roke da ci gaba da taimakawa makaranta da matsayin da suke da shi.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

-

-

-

-

-

-

-

 

25 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel