RAAF Official Website

A+ A A-

Jami'an Cibiyar Rasulul A'azam Sun Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga Sheikh Zakzaky

Rate this item
(0 votes)

A ranar Juma'a 1 ga watan Augustan 2014 ne shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam da ke Kano Sheikh Muhammad Nur Dass tare da wasu daga cikin mataimakansa da jami'an Mu'assarar suka kai wa Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahi Ya'aku El-Zakzaky ziyara don isar da ta'aziyyarsu gare shi saboda kisan gillan da sojoji suka yi wa 'ya'yansa su uku da kuma wasu mabiyansa a lokacin da suke gudanar da muzaharar ranar Kudus ta duniya a birnin Zariya.

A yayin ziyarar dai Sheikh Muhammad Nur ya isar sa sakon ta'aziyyarsa a madadin Mu'assasar ga Sheikh Zakzakin yana mai bayyana tsananin damuwa da alhini da abin da ya faru da kuma addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan na su su kuma wadanda suka sami raunuka Allah ya gaggauta ba su lafiya.

Shi ma a nasa bangaren Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara kamar yadda kuma ya yi musu karin bayani kan hakikanin abin da ya faru a yayin muzaharar da kuma yadda sojojin suka kashe masa 'ya'yan nasa musamman biyu daga cikinsu wadanda suka kama su da ransu.

Daga cikin wadanda suke tare da Sheikh Muhammad Nur yayin wannan ziyarar sun hada da Sheikh Bashir Lawal da kuma Sheikh Saleh Zariya da sauran 'yan'uwa masu gudanar da ayyuka daban-daban a Mu'assasar ta Rasulul A'azam.

Ga wasu daga cikin hotunan da aka dauka yayin ziyarar:

 

 

 

 

Last modified on

82 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel