RAAF Official Website

A+ A A-
Webmaster

Webmaster

Website URL:

Sheik Nur Ya Gana Da Daliban Makarantar Hauza Ta Qum

Published in Top News

A ci gaba da ziyarar da ya ke yi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma kamar yadda ya saba a duk lokacin da ya kai ziyara Iran din, Shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam Sheikh Muhammad Nur Dass ya gana da wasu daga cikin dalibai 'yan Nijeriya musamman sabbin daliban da Mu'assasar ta tura karatu birnin na Qum don tattaunawa kan batutuwa daban-daban da suka shafi karatun na su da kuma ba su shawarwari kan yadda za su ciyar da karatun na su gaba da kuma kai ga koluluwar manufarsu ta tafiya birnin ilimin na Qum.

Ga wasu daga cikin hotunan ganawar:

 

 

A ranar Juma'a 1 ga watan Augustan 2014 ne shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam da ke Kano Sheikh Muhammad Nur Dass tare da wasu daga cikin mataimakansa da jami'an Mu'assarar suka kai wa Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahi Ya'aku El-Zakzaky ziyara don isar da ta'aziyyarsu gare shi saboda kisan gillan da sojoji suka yi wa 'ya'yansa su uku da kuma wasu mabiyansa a lokacin da suke gudanar da muzaharar ranar Kudus ta duniya a birnin Zariya.

A yayin ziyarar dai Sheikh Muhammad Nur ya isar sa sakon ta'aziyyarsa a madadin Mu'assasar ga Sheikh Zakzakin yana mai bayyana tsananin damuwa da alhini da abin da ya faru da kuma addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan na su su kuma wadanda suka sami raunuka Allah ya gaggauta ba su lafiya.

Shi ma a nasa bangaren Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara kamar yadda kuma ya yi musu karin bayani kan hakikanin abin da ya faru a yayin muzaharar da kuma yadda sojojin suka kashe masa 'ya'yan nasa musamman biyu daga cikinsu wadanda suka kama su da ransu.

Daga cikin wadanda suke tare da Sheikh Muhammad Nur yayin wannan ziyarar sun hada da Sheikh Bashir Lawal da kuma Sheikh Saleh Zariya da sauran 'yan'uwa masu gudanar da ayyuka daban-daban a Mu'assasar ta Rasulul A'azam.

Ga wasu daga cikin hotunan da aka dauka yayin ziyarar:

 

 

 

 

A yau Juma'a, wacce ta yi daidai da Juma'ar karshe ta watan Ramalana wacce marigayi Imam Khumaini (r.a) Mu'assasin Juyin juya halin Musulunci na Iran, ya sanya mata sunan Ranar Kudus ta duniya, ce Mu'assasar Rasulul A'azam (RAAF) ta gudanar da taron Ranar Kudus din a garin Bauchi karkashin jagorancin shugaban Mu'assasar Sheikh Muhammad Nur Dass.

Shi dai wannan taron wanda aka gudanar da shi tare da rufe tafsririn Alkur'ani mai girma da Sheikh Muhammad Nur Dass din yake yi tsawon watan Ramalana ya sabi halartar 'yan'uwa na garin Bauchi.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron Sheikh Nur ya yi karin haske dangane da halin da al'ummar Palastinun suke ciki da kuma manufar sanya wa wannan ranar sunan Ranar Kudus da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi bugu da kari kuma kan nauyin da ya hau kan al'ummar musulmi kan al'ummar Palastinun musamman a daidai wannan lokacin da yahudawan sahyoniya suke ci gaba da kai musu hare-hare.

Ga kadan daga cikin hotunan taron:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel