RAAF Official Website

A+ A A-
Webmaster

Webmaster

Website URL:

A ci gaba da gudanar da tarurrukan juyayin Ashura a Husainiyar makarantar hauzar Bakirul Ulum da ke karkashin Mu'assasar Rasulul A'azam (s) da ke karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Nur Dass, a yammacin yau ne aka gudanar da taron rana ta hudu na juyayin inda Sheikh Muhammad Nur Dass ya gabatar da jawabi a wajen taron.

A lokacin jawabin nasa bayan bayanin matsayin Imam Husaini (a.s) har ila yau Sheikh Muhammad Nur ya yi karin haske dangane da irin nauyin da ke wuyan 'yan'uwa mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) wajen ciyar da wannan tafarki gaba da suka hada da kokarin wajen neman ilimi da abin da yi don rufa asirinsu da kuma shiga cikin harkokin na ayyuka na gwamnati da na al'umma don kiyaye mutumcinsu da kuma lamunce ci gaban Shi'anci.

Kafin jawabin Sheikh din sai da Sidi Bashir daya daga cikin daliban makarantar ya gabatar da jawabin share fage;

 

 

 

Hotunan Bikin Ghadir A Husainiyar Hauzar Baqirul Ulum

Published in Top News

Kamar yadda ta saba, Mu'assasar Rasulul A'azam da ke da helkwata a garin Kano, Nijeriya ta gudanar da bukukuwan Idin Ghadir, ranar da  Manzon Allah (s) ya nada da kuma zaban Amirul Muminin Ali bn Abi Talib (a.s) a matsayin halifa kuma imamanin musulmi a bayansa kai tsaye, a Husainiyar Makarantar Hauzar Baqirul Ulum da ke Dambare.

Taron dai ya sami halartar shugaban Mu'assasar Sheikh Muhammad Nur Dass, sakataren Mu'assasar Sheikh Saleh Muhammd Sani Zari'a da sauran muminai maza da mata da suka zo daga bangarori daban daban na Nijeriya bugu da kari kan daliban makarantar.

Sheikh Saleh Zariya ne ya gabatar da jawabi a wajen bikin.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

An gama dukkanin shirye-shiryen tarbar watan Muharram, watan da jini ya yi nasara a kan takobi, watan da jikan Manzon Allah (s) Imam Husaini (a.s) da iyalansa da sahabbansa suka sadaukar da rayukansu waje kare addinin Musulunci daga kokarin gurbata shi da Banu Umayya suka yi, a Husainiyar Hauzar Bakirul Ulum da ke Dambare.

Kamar yadda aka saba kowace shekara, an lullube Husainiyar da bangarori daban-daban na makarantar da ke nuni da alamar shigowar watan na Muharram.

Ga wasu daga cikin hotunan 'yan'uwa a lokacin da suke gudanar da ayyukan sanya bakaken kyalle a Husainiyar:

 

 

 

 

 

 

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel