RAAF Official Website

A+ A A-

Kamar yadda ta saba, Mu'assasar Rasulul A'azam da ke da helkwata a garin Kano, Nijeriya ta gudanar da bukukuwan Idin Ghadir, ranar da  Manzon Allah (s) ya nada da kuma zaban Amirul Muminin Ali bn Abi Talib (a.s) a matsayin halifa kuma imamanin musulmi a bayansa kai tsaye, a garin Bauchi da ke jihar Bauchi wanda Makarantar Sumayya ta dauki nauyin gudanarwa.

Wanda taro dai ya sami halartar malaman makarantar ta Sumayya, sauran 'yan'uwa da kuma daliban makarantar da kuma sauran al'ummar musulmi masoya Manzon Allah (s) da Iyalansa tsarkaka (a.s).

Malam Yusuf Saleh Gwani ne ya gabatar da jawabi a wajen bikin.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Read more... 140

A ci gaba da ziyarar da ya ke yi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma kamar yadda ya saba a duk lokacin da ya kai ziyara Iran din, Shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam Sheikh Muhammad Nur Dass ya gana da wasu daga cikin dalibai 'yan Nijeriya musamman sabbin daliban da Mu'assasar ta tura karatu birnin na Qum don tattaunawa kan batutuwa daban-daban da suka shafi karatun na su da kuma ba su shawarwari kan yadda za su ciyar da karatun na su gaba da kuma kai ga koluluwar manufarsu ta tafiya birnin ilimin na Qum.

Ga wasu daga cikin hotunan ganawar:

 

 

Read more... 100

A ranar Juma'a 1 ga watan Augustan 2014 ne shugaban Mu'assasar Rasulul A'azam da ke Kano Sheikh Muhammad Nur Dass tare da wasu daga cikin mataimakansa da jami'an Mu'assarar suka kai wa Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahi Ya'aku El-Zakzaky ziyara don isar da ta'aziyyarsu gare shi saboda kisan gillan da sojoji suka yi wa 'ya'yansa su uku da kuma wasu mabiyansa a lokacin da suke gudanar da muzaharar ranar Kudus ta duniya a birnin Zariya.

A yayin ziyarar dai Sheikh Muhammad Nur ya isar sa sakon ta'aziyyarsa a madadin Mu'assasar ga Sheikh Zakzakin yana mai bayyana tsananin damuwa da alhini da abin da ya faru da kuma addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan na su su kuma wadanda suka sami raunuka Allah ya gaggauta ba su lafiya.

Shi ma a nasa bangaren Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara kamar yadda kuma ya yi musu karin bayani kan hakikanin abin da ya faru a yayin muzaharar da kuma yadda sojojin suka kashe masa 'ya'yan nasa musamman biyu daga cikinsu wadanda suka kama su da ransu.

Daga cikin wadanda suke tare da Sheikh Muhammad Nur yayin wannan ziyarar sun hada da Sheikh Bashir Lawal da kuma Sheikh Saleh Zariya da sauran 'yan'uwa masu gudanar da ayyuka daban-daban a Mu'assasar ta Rasulul A'azam.

Ga wasu daga cikin hotunan da aka dauka yayin ziyarar:

 

 

 

 

Read more... 82

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel