RAAF Official Website

A+ A A-

A yau Juma'a, wacce ta yi daidai da Juma'ar karshe ta watan Ramalana wacce marigayi Imam Khumaini (r.a) Mu'assasin Juyin juya halin Musulunci na Iran, ya sanya mata sunan Ranar Kudus ta duniya, ce Mu'assasar Rasulul A'azam (RAAF) ta gudanar da taron Ranar Kudus din a garin Bauchi karkashin jagorancin shugaban Mu'assasar Sheikh Muhammad Nur Dass.

Shi dai wannan taron wanda aka gudanar da shi tare da rufe tafsririn Alkur'ani mai girma da Sheikh Muhammad Nur Dass din yake yi tsawon watan Ramalana ya sabi halartar 'yan'uwa na garin Bauchi.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron Sheikh Nur ya yi karin haske dangane da halin da al'ummar Palastinun suke ciki da kuma manufar sanya wa wannan ranar sunan Ranar Kudus da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi bugu da kari kuma kan nauyin da ya hau kan al'ummar musulmi kan al'ummar Palastinun musamman a daidai wannan lokacin da yahudawan sahyoniya suke ci gaba da kai musu hare-hare.

Ga kadan daga cikin hotunan taron:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Read more... 46

A nan ana iya ganin hotuna daban-daban na shekarun da aka jima ana gudanar da Jerin Gwanon Ranar Qudus don amsa kiran marigayi Imam Khumaini (r.a)

 

Matsa Nan Don Ganin Hotunan

 

Read more... 46

A yau ne aka gudanar da Jerin Gwanon Ranar Qudus ta duniya don amsa kiran marigayi Imam Khumaini (r.a) a mafi yawa daga cikin kasashen musulmi da ma wadanda ba na musulmin ba.

Ga wasu daga cikin hotunan jerin gwanon da aka yi a birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

 

Ana Iya Matsa Wannan Link Din Don Ganin Hotunan

Read more... 84

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel