RAAF Official Website

A+ A A-

Ma'anar Ghadir: Wilaya Da Imamanci

Rate this item
(1 Vote)

MA’ANAR GHADIR: WILAYA DA IMAMANCI

 

Gabatarwa

Rubutun da na yi mai taken Eid el-Ghadeer: Bukin Cakan Addini, wanda ya fito a shafi na 23 na jaridar Leadership ta Hausa, bugu na 319 ta ranar 24 ga Zul-Hijja, 1433 (9 ga Nuwamba, 2012) ya ja hankalin mutane da yawa. Kwalliya ta biya kudin sabulu dangane da makalar, saboda dalilin rubuta ta shi ne sanar da mutane matsayin ’yan Shi’a kan wannan biki da dalilin da ya sa suke yinsa.

 

Martanonin da suka biyo baya, ta hanyar sakonnin da na samu, sun kasrkasu tsakanin masu yabo da masu suka da ’yan ba-yabo ba-fallasa. Kowanne daga wadannan martanoni ina da misalansa. Wanda zan yi magana a kai a wannan karon shi ne kashi na biyun; wato masu suka. Misaliinsu shi ne martanin da wani mai suna Nasurussady Kasuwar Bacci Kaduna ya rubuta kuma jaridar Leadership Hausa ta buga a fitowarta ta 311 a ranar 23 ga Nuwamba 2012, wanda marbucin ya siffanta rubutunsa da “bayani a ilmance”.  Da ma dai dan’uwan ya dan yi tawali’un siffanta rubutun nasa da “bayani a almajirance” da ya fi samun uzurin harde-harden da rubutun nasa ke fama da su.

 

A kan haka, duk da cewa ba martini na kai tsaye zan bayar a kan rubutunsa ba, sai dai kasancewar galibin ’yan wannan bangaren sun yi kama da Nasurussady ta wajen kalubalentarsu ga akidar Shi’a, don haka zan sanya rubutun nasa ya zama misalin irin tarnakin da irin wannan nau’in na masu yaki da duk abin da ya sabawa fahimtarsu suke fama da shi na rashin natsuwa su fahimci abin da abokan hamayyarsu suke fadi, don su shimfida tattaunawarsu da martanoninsu a kai.

 

Duk da haka, ina tunatar da cewa tun a shekar ta 1996 na rubuta littafi mai suna Raddin Shubuhohi A Kan Ghadir da Nassosin Imamancin Ahlul-Bait (AS) a matsayin martini a kan shakkokin da wani Bawahabiye daga Sokoto ya tayar a lokacin. Littafin ya samu karbuwa matuka, ta yadda har sai da bukatun jama’a suka sa aka sake buga shi a shekara ta 1998, kuma har yanzu yana nan a yaryade a tsakanin jama’a. Abin da ke cikin martanin ya dagargaza duk irin wadannan shubuhohi da rudanonin dake rikirkita tunanin mutane irin su Nasurussady. Ba zan koma ta kansu ba a yanzu.

 

Lamarin Ghadeer A Wajen Musulmi

Duk da haka ina godiya ga Nasurussady a kan abin da ya rubuto, don kuwa ya ba ni uzurin fadada zantawa a kan wannan bangare da wasu suka dade suna rabewa dashi wajen yada tuhume tuhume marasa tushe a kan Shi’a, ba tare da sun mallaki mafi karancin masaniya a kan ainihin abubuwan da ’yan Shi’a suke cewa a kan lamurran da su (masu gadandamin) ke tayarwa ba.

 

Galibin masu jayayya dangane da lamarin Ghadder ba su damu da jayayya a kan kasancewarsa idi ba -kamar yadda Nasurussady ya damu da haka ba. Kila don fahimtar rashin amfanin haka ga abin da suke son tabbatarwa, ko kuma saboda sun fahimci abin da ake nufi da Idi dangane da Ghadeer yana nufin bukin tunawa da wannan babban lamari tare da farin cikin nuna godiya ga Allah a kan Kammalar Addini da Cikar Ni’ima a ranar. Don haka irin wannan biki bai kasa irin bukukuwan Mauludi da shiga sabuwar shekarar Musulunci da wasu Musulmi ke yi ba. Da haka, ta bayyana a she Musulmi suna da idoji (da wannan ma’anar) a gefen na karama da babbar Sallah. Da alamu matsalar abokina a kan wannan, shi ne kasa bambacewa tsakanin ma’anoni biyu na kalmar IDI, wato ma’anar idin Sallah (wanda kalmar idi da ma’anar fikhu take nufi) da idin bukukuwan tunawa da wasu lamurra masu darajaa idon wasu musulmi, kamar idin Ghadeer (a wajen Musulmin Shi’a) da idin Mauludi (a wajen galibin Musulmin duniya ban da Wahabiyawa), kai har ma da bukuwan daidaiku irin bikin samun karuwar aure da haihuwa, wadanda duk za a iya kiransu idoji ne (da ma’anar lugga da take nufin farin ciki). Sinadarin “biki” da “murna” da ma’anonin biyu suka hadu a kai shi ya halatta a kira kashi na biyu da IDI. Irin wannan yana daga matsalolin rashin fahimta da irin wannan nau’in na masu jayayya da Shi’anci suke fama da ita. A kan wannan za a iya dora rashin fahimtar Uthmanul-Khamis da abokin mu ya nakalto, wanda ya kasa bambance wurare da ake amfani da kalmar “maula” da ma’anar shugaba da amfani da ita a kan ma’anar “masoyi”. Da ya fahimci haka da ya san bambancin ma’anar kalmar a duk inda aka yi amfni da ita a AlKur’ani ko a hadisi (na cika bayani a kan haka a shafi na 22-45 a cikin wancan littafi nawa da na bayyana).

 

Shakka a Kan Ingancin Nassosin Ghadeer

Wasu daga masu karyata lamarin Ghadeer sun yi kokarin kawo shakka a kan ingancin tafisirin ayar Isar da Sako da ayar Cikan Addini a kan lamarin Ghadeer. Abokina Nasurussady ya kasa hatta kwafo wannan ra’ayi, sai ya kare da cewa “wallahi ba malamin sunnah da ya fassara su a kan khalifancin Ali (ra)”. Alhali ni a makalata na jero kadan daga malaman Ahlussunna da suka fadi saukar ayoyin a kan lamarin Ghadeer da Wilayar Ali, ba kan khalifancinsa ba (bayani a kan bambanci tsakanin ma’anonin biyu yana zuwa nan gaba kadan). Ban sani ba ko malamai irin su Wahidi (a cikin Asbab an-Nuzuul) da Suyuti (a cikin al-Durrul-Manthur) da Ibin Asakir (a cikin Tarikhu Dimashka) da Badaruddin al-Ainy (a cikin Umdatul-Kari Sharhin Bukhari) da Shaukani (a cikin Fatahul-Kadeer) da ire-irensu da suka rubuta fassaarar ayoyoin a kan Imam Ali da lamarin Ghadeer duk ba Ahlussunna ba ne a wajen irin su Nasurussady?

Na’am, da gaske ne cewa akwai malaman Ahlussunna da suke fassara ayoyin da sabanin abin da muke magana a kai, kamar fadin saukar ayar Cikar Addini a ranar Arfa, wannan kenan yasa ayoyin cikin jerin gwanon ayoyin da malamai ke da sabanin fassara a kansu. Irin wadannan kuwa da ma malamai sun saba aikin kwatanci ne a kansu wajen ganin yiwuwar hade su idan haka zai yiwu, ko fifita wata fassara a kan wata idan ba za su iya haduwa ba; da haka sai lamarin ya zama na ijtihadi a tsakanin malamai. Ayoyin AlKur’ani da yawa kuwa suna da wannan sigar (na yi kokarin kawatanta fuskokin tafisiran wadannan ayoyin a littafina na Raddin Shubuhohi a kan Ghadir mai so sai ya koma ya duba). Wannan duk a tsakanin malaman Ahlussunna kenan. Amma malaman Shi’a sun dace da kalma daya a kan saukar wadannan ayoyi a kan lamarin Ghadder kuma suna zance ne a kan Imamancin Ali (AS).

 

Bangaren dake tabbatar da Wilayar Ali (AS) daga nassin hadisin Ghadir kuwa ba ya karyatuwa duk yadda ma jayayya ya kai da jayayyarsa. Saboda yana cikin mutawatiran hadisai (su ne hadisan da maruwaitansu suka yawaita, ta yadda ba zai yiwy su hadu a kan karya ba). Irin wadannan hadisai kuwa su ba su da yawa a tsakanin dukkan Musulmi. Takarkarewa wajen karyata su kuwa ba zai bari a yarda da wani abu na Musulunci ba. Mafi karancin Sahabban da aka ambaci ruwaiyarsa daga bakinsu sun ketare saba’in.

 

Sai dai duk da haka dakarun dake da matsala da tsarkakan’Yan-Gidan Annabi (SAWA), irin su Ibin Taimiyya (a cikin Minhajus-Sunna) da Ibin Hajar al-Haithami (a cikin Sawa’ikul-Muhrika) sun yi ta kiki-kaka waje karyata bangarorin addu’ar da ta biyo bayan nadin Imam Ali (AS), mai cewa “Allah Ka taimaki wanda ya taimake shi (Ali) Ka watsa aniyar wanda ya ki taimaka masa”. Wannan ba abin mamaki ba ne kuwa idan aka yi la’akari da irin mu’amalar Ibin Taimiyya na kokarin karyata duk abin da yake nuna fifikon ’Yan-Gidan Annabta kamar yadda Ibin Hajar al-Askalani ya adi game da shi  (a cikin Lisanul-Mizan 6/319) ya yi karyata nagartattun hadisai a raddin da yayiwa Allama al-Hilli a cikin Minhajus-Sunna. Abin mamaki shi ne yadda mabiya Ibin Taimiyya, wato ’yan bangaren su Nasurussady, suka yi biris da yadda malaman hadisi irinsu Ibin Hajar suka fadakar a kan yadda Shehinsu ke iya karyata ingantaccen hadisi (ko dai bisa jahilci da kuskure ko mantuwa kamar yadda Ibin Hajar ke gani ko saboda yadda kiyayyar Ali da ’ya’yansa take rufe masa ido kamar yadda muke gani). Ko ta halin kaka dai, wannan ya nuna su a masu riko da Shehunnai koda sun sabawa Sunna.

 

Ma’anar Hadisin Ghadeer

Wani abu da irin su Nasurussady ba sa fahimta shi ne cewa sakon Ghadeer da ’yan Shi’a ke imani da shi shi ne ayyana Imami bayan Manzo (SAWA), ba nada mujarradin shugaban gwamnati (Khalifa) ba. Nauyin Imamanci kuwa, a fahimtarsu, ya wuce nauyin Khalifanci, duk kuwa da cewa idan Imami ya rasa akalar Khalifanci sauke nauyin Imamanci yana zama masa mai matukar wahala, sai dai duk da haka sashen aikinsa na Imamanci yana nan daram. Sannan ’Yan Shi’a suna da imanin cewa ba a iya kange Imami daga mukamin Imamanci, amma ana iya hana shi isa zuwa ga mukamin Khalifanci, hakan kuma zai wahalshe shi a aikinsa na Imamanci (kamar yadda bayani ya gabata) sannan al’umma za ta galabaita a sakamakon rashin ma’asumin Khalifa.

 

Don haka ’yan Shi’a sun yi imani da cewa munasabar Ghadder shi ne matakin karshe da Allah Ya hori ManzonSa (SAWA) da ya danka amanar Imamanci a hannun Imam Ali (AS) a bayansa, saboda shi kadai ne ya cancanci wannan matsayi da dukkan mizanoni cancantar shugabanci irin wannan. Alkur’ani ya bayyana biyu daga cikin wadannan ma’aunai da cewarsa “Kuma Annabinsu ya ce da su: ‘Hakika Allah Ya nada muku Daluta ya zama shugaban.’ Sai suka ce ‘ta yaya zai zama mai shugabanci a kan mu alhali kuwa mu muka fi cancantarta, kuma ba shi da yalwar dukiya ba?’ sai ya ce: ‘Hakika Allah ne Ya zabe shi, kuma Ya kara masa yalwar ilimi da karfi, kuma Allah Yana bayar da mulkinSa ga wanda Ya so, kuma Allah Mawadaci ne Masani’ (Bakara/247). Nagartaccen tarihi ya tabbatar da Imam Ali (AS) a matsayin wanda ya fi kowa yalwar ilimi da garzontaka bayan Annabi (SAWA). Imamanci, a tsarin wannan fahimta, ahadi (wato alkawari) ne na Allah (kamar yadda aya ta 24 da cikin Surar Bakara take tabbatarwa), wadda babu wanda Allah ke mika shi a gare shi sai ma’asumi (wanda ya tsarkaka daga zunubbai da kurakurai da mantuwa). Shi kuwa ma’asumi babu mai ayyana shi sai Allah kamar yadda Yake fadi da kanSa a cikin AlKur’ani: “Idan wata hujja ta zo musu sai su ce: ‘ba za mu yi imani ba har sai anzo mana da irin abin da aka zowa Manzannin Allah da shi , alhali  Allah Shi Ya fi sanin inda Yake aje sakonSa…” (al-An’am/124).

 

 Matsayin da ’yan Shi’a suke yin ikirarinta ga Imamansu shi ne wannan matsayin da mutane ba su da hannu wajen zaben ma’abocinsa; saboda ya kunshi nauyin (a) tabbatar da isar da sakon Allah (SWT) ta cikakkiyar fuska ba tare da kuskure ba; (b) sahihin fassarar addini, wanda ya nisanta daga shubuha da kurakurai balle ganganta ragi da kari a cikin karantawar addini; (c) dorawa daga inda Manzo (SAWA) ya tsaya wajen isar da al’umma zuwa kamalar da cancanta bisa nagartaccen jagoranci da ya nisanta daga duk nau’o’in kurakrai ta dukkan fuskoki, (d); kutsawa cikin tarnakoki da mawuyatan yanayoyin da makiya kan kirkira da fita daga cikinsu lafiya ba tare da raunanar Musulunci da Musulmi a sakamakon raunin jagora ko kuskurensa ba. A dunkule aikin Imami shi ne ainihin aikin Annabi, bambanci kawai shi ne a karbar Wahayi, wanda ya kare da shugaban halitta (SAWA). Zai yi sauki a iya fahimtar cewa irin wannan shugabaanci yana bukatar tanaji na masamman daga Allah Ta’ala, kuma ba zai yiwu a yarda da cewa Annabi (SAWA) ya bar duniya ba tare da tabbatar da wannan tanaji da fayyace shi sanka-sanka ba. Don haka, a tsarin imanin Shi’a, Annabi (SAWA) ya fayyace wannan shugabanci tun farkon bayyana da’awarsa a lokacin saukar ayar Tswatar da Dangi Makusanta mai cewa “Kuma ka tsawatar da danginka makusanta (Shu’ara 214), inda Annabi (SAWA) ya tara danginsa makusanta ya bayyana musu sakonsa. Wasu ruwayoyi sun tabbatar da nadin Imam Ali (AS) a matsayin wazirin Manzo kuma abin wasicinsa kuma Khalifansa a bayansa (gamayyar wadannan mukaman duka shi ne Imamanci). Sannan hadisai masu yawa da manzo yayita nanatawa a kan wannan matsayi sun tabbata a mahallinsu. Na ambaci wasu hadisan Wilayar Ali a makalar da ta gabata, wadanda abokina ya bayyanasu da rashin inganci ba tare da ya ambaci malaman da suka raunanasu, da inda aka fitar da raunanawar da kai’dar da raunanawar ta ginu a kai da nau’in raunanawar ba. Da ya fadi haka da ya ji inda gizo ke saka a kan raunana hadisai da yadda siyasar bangaranci da ta’assubanci suke da tasiri a kan kirkiran ka’idojin raunanwa da inganta hadisai. Allah dai shi ne kawai gatan gaskiya.

 

Ko ta halin kaka dai, sabanin da ’yanuwa Ahlussunna suke da shi da Shi’a a kan wannan shi ne rashin ganin ingancin wasu daga cikin irin wadannan hadisai, da fassara wasunsu sabanin yadda Shi’a suke fahimta. Warware irin wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar tattaunawar wadanda suka fahimci inda gizo-ke-saka dangane da kowane bangare, da yarda da cewa sabanin dake tsakani na fahimta ne, wanda akwai irinsa hatta a tsakanin ’yan bangare daya. Koda ba a samu dacewa a kan fassara daya ba, za a san cewa kowa yana tafiya ne a kan dalilin da ya inganta a wajensa, saboda da haka yana da ladan kokarin neman gaskiyarsa ko da bai same ta ba (kamar yadda hadisin Bukhari ya fitar daga Manzo). Wannan tsari ya kunshi bambancin fahimta tsakanin Shi’a da Ahlussunna a kan wanda keda fifiko tsakanin Imam Ali (AS) da Abubakar (RA) da Umar (RA). Kowa yana da hujjarsa da take tilasta masa ganin rashin ingancin hujjar dan’uwansa a kan haka. Kofaar tattaunawa har yanzu tana nan a bude a kan haka.

 

Khalifancin Abubabakar da Umar

A kan haka zancen matsayin Khalifancin Abubakar (RA) da Umar (RA) da galibin masu jayayya da Shi’a suke yawan bijirowa da shi ba shi da mahalli a irin wannan tattaunawar, saboda ba wanda yake yi musu da da’awar Imamanci ko isma kamar yadda muke yiwa Ahlul-Bait (AS) kuma muke tabbatarwa da kwararan dalilai. Abin da ’yan’uwa Ahlussuna suke da’awarsa gare su shi ne hakkin Khalifanci bisa dalilan zaben al’umma ba tare da bayyannen nassi daga AlKur’ani ko sallamammen hadisi daga Manzo (SAWA) ba. Hadisan da wasu kan kawo a kan Khalifancin su, kamar hadisin “ku yi koyi da biyun bayana Abubakar da Umar” da hadisan da ake ruwaitowa kan Abubakar shi kadai, kamar hadisin da ke horon matar da ta tambayi Manzo (SAWA) kan wata mas’ala ya ce ta tafi ta dawo, tace idan ba ta same shi ba fa ya ce ta samu Abubakar, da ire-irensu duk ba karbabbu ba ne hatta a bisa ka’idar Ahlussunna, saboda an ruwaito hadisan da suka fi su karfin isnadi (ta tsarin Ahlussuna) daga Abubakar (RA) da Umar (RA) suna inkarin cewa Annabi ya nada su. Misali a kan haka shi ne abin da masu tarihi suka ruwaito na cewa Abubakar (RA) a lokacin mutuwarsa ya yi fatan ace ya tambayi Manzon Allah ko Ansar suna da wani nasibi dangane da Khalifanci (Tarihin Tabari. 3/431). Haka ma hadisin da Ibin Umar ya ruwaito Umar bin Khattab yana fadi a gadon mutwarsa, lokacin da aka ce masa ka nada khalifa mana, sai ya ce: “Idan na yi nadi wanda ya fi ni ya yi –yana nufin Abubakar- idan ban yi ba wanda ya fi ni ma bai yi ba –yana nufin Annabi - (Muslim. 3/1454). Kara da cewa ba a taba nakalto inda Abubakar (AS) da Umar (RA) suka taba fadin cewa Manzo ya nada su a matsayin khalifofi ba, hatta kuwa a ranar Sakifa a lokacin da jayayya ta yi zafi tsakanin Muhajirun da Ansar a kan lamarin Khalifanci (bayan wafatin Annabi). Wadannan duk sun yi karo da duk wani nassi da ake da’awarsa a kan khalifancinsu. Don haka ne ma malamai da manazarta daga Ahlussunna suka fi karfafa nazarin zabe a matsayin majinginar Khalifancin Abubakar (RA), da nadin Abubakar (RA) a matsayin majinginar khalifanci Umar (RA) da zabin galibin mambobin kwamitin mutane shida da Umar (RA) ya kafa a matsayin majinginar khalifancin Uthaman (RA). Saboda ra’ayin nadinsu daga Manzo (SAWA) yana kewaye da tambayoyin da ba sa amsuwa.

 

Matsayin Imam Ali (AS) da daukacin Banu Hashim dangane da khalifancin Sakifa da adanda suka biyo bayan shi kuwa sananne ga duk wanda ya yi nazarin abubuwan da suka gudana bayan wafatin Manzo (SAWA). Hatta Bukhari (5/177) da Muslim (3/1380) sun ruwaito cewa Imam bai yi Mubaya’a ba har sai bayan wafatin Fatima (AS). Amma me yasa daga baya ya hakura ya yi mubaya’a? Shi da kansa ya bayyana dalilansa a wurare da yawa cikin Nahjul-Balaga, masamman a hudubar Shakshakiyya, da cewa saboda hakan shi ne maslahar Musulunci take hukuntawa. A matsayin shi na Imami kuwa, da ma wannan mataki yana daga aikinsa, wato fayyace ainihin matakin da ya kamata a lokacin da ya kamata da daukar matakan da za su tabbatar da lamunin ci-gaban Musulunci da kare cikin gidan shi daga hargitsi da zubar da jinin da ba shi da wani amfani.

 

Haka ma zancen gudanar auratayya tsakaninsu ba shi da alaka da wannan zancen, don dai akwai auratayya a tsakanin Musulmi. Duk kuwa da cewa ruwayoyin auren Umar (RA) da wata ’ya ga Ali (AS) suna da matsaloli da yawa ta fuskar isnadi da ma’ana tare (saboda tazarar shekaru dake tsakanin Umar da yarinyar da ake da’awar ya aura, da sabanin ruwayoyin tarihi a kan samuwar wannan ’yar ga Ali duk suna haifar da matala ga ruwayoyin). Duk da haka idan ma da hakan ya inganta, ai Imam Ali (AS) ma’asumi ne wanda ake fahimtar hukuncin duk abin da ya aikata.

 

Haka zancen cewa Ali ya sawa ’ya’yansa sunan Umar da Abubakar, shi ma dai ba ya taimakon ra’ayin masu sabani da Shi’a da koamai. Saboda in banda sunan Annabi, ba inda aka ruwaito mana cewa Sahabbai suna sawa ’ya’yansu sunayen junansu da nufin wata kara ko soyayya; don kuwa ba wani abu dake nuna cewa mizanonin kara da soyayya a tsakanin Sahabban da suke sa’annai ne ya kunshi sawa ’ya’yan sunayen junansu kamar yadda lamarin yake a kasar hausa. Da kuwa lamarin haka yake to da wannan ya nuna cewa kenan su Abubakar da Umar ba su da kara kuma ba sa son Ali, tunda ba su sawa ’ya’yansu sunansa da sunan Fatima da Hassan da Hussaini ba. Abin fahimta a nan shi ne cewa sunaye irin su Umar da Uthaman suna daga sunaye masu kyau a tsakanin larabawa. Abubakar kuwa lakabi ne ba suna ba (asalin sunansa Abdullahi), don haka bai inganta cewa Imam Ali ko wani daga Sahabbai ya sawa dansa suna Abubakar ba.

 

A karshe ina fata dan’uwana Nasurussady, da ire irensa, za su fahimci cewa mafi alherin abin da zai hada kan Musulmi shi ne usulubin bude zukata ga juna, da yarda da musuluncin duk wanda ya furta Kalmar Shahada ya kiyaye shika-shikan Musuluncin nan  da aka dace a kansu, da baiwa juna uzuri a kan inda aka samu rashin fahimtar juna, da yarda da cewa kowa yana bakin kokarinsa ne don ya isa zuwa ga Allah (SWT) ta nagartacciyar akidar da ya isa zuwa gare ta a iyaka iliminsa. Kar a bambanta a kan haka tsakanin ’yan Shi’a da wasunsu. Sabanin fahimta a addinin mu kuwa karbabbe ne. Ba kungiyar dake da hakkin killace hakkin sabani ga kanta da haramta wannan hakki sauran kungiyoyi.  Allah Ya ba mu ikon fahimtar gaskiya da haduwa a kanta.

Last modified on

25 comments

Leave a comment

Make sure you enter the (*) required information where indicated.Basic HTML code is allowed.

Visit the new site http://lbetting.co.uk/ for a ladbrokes review.

Copyright © Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Kano - Nigeria 2006. All rights Reserved

Login or Register

LOG IN

Register

User Registration
or Cancel